WAYE YAFI WANI TAFKA SHIRME DA RASHIN KAN GADO...
2. BASAKKWACE: Wanda yake yiwa shuka ban ruwa a dai-dai lokacin da ake sharara ruwan sama.
3. ƊAN FULANI: Da ya fesa turare a jikinsa a dai-dai lokacin ɗaukar hoto da niyyar wai idan an wanko hoton zaiji ƙamshin turaren.
4. ƊAN KADUNA: Da ya sanya radiyo a firinji domin ya saurari cool music.
5. ƊAN KEBBI: Wanda yaci abinci a hotal ya wanke kwano.
6. BABARBARE: Wanda ya tsugunna ya gaida sarkin garinsu lokacin da ya ganshi a TV a gurin wani taro.
7. ƊAN BAUCHI: Wanda yasa aka yi masa polish a takalmi saboda zaiyi hoton passport.
8. BAKATSTSINE: Wanda yana tafiya yayi tuntuɓe da wani abu a duhu saiya ɗauka ya shinshina a hancinsa yaji ashe kashi ne sai yace "ALHAMDULILLAH!" da ban taka ba.
9. DAN GASHUA: Wanda yaje banki da sifana zai buɗe account.
10. BAZAMFARE: Wanda yayiwa ATM CARD ɗinsa lamineshin saboda gudun kada ya karye ko kuma ya koɗe.
LURA: Ba muyi wannan abun domin cin fuska ga wata ƙabila ko yanki ba, mun yi ne kawai domin a yi nishaɗi.
A ra'ayin Ka ko kuma a ra'ayin Ki waye yafi wani shirme a cikin su? Aika mana da ra'ayin Ka/Ki a adireshin e-mail ɗin mu a muryarhausa24@gmail.com
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.
Tushe/Asali: www.muryarhausa24.com.ng