Bayani Akan Layya
Marubuciya: Faridah Bintu Salis
LAYYA: ita ce dabbar da ake yankewa domin neman yardar ALLAH daga cikin nau'o'in Tumaki da Awaki da Shanu da Raƙuma waɗanda suka cika shekarun yin layya, kuma sun kuɓuta daga kowane aibi.
An sharɗanta yanke dabbar layya a ranar goma ga watan Zu-lhijjah da yini biyu masu bi mashi, bayan dawowa daga sallar idi, bayan kuma Liman ya yanke. [Fawakihud-dawaniy 1/440].
Sheikh Abubakar Jabir Al-Jaza'iriy ya faɗa acikin littafinsa mai suna [Minhajul Muslim] Yace: LAYYA wata dabba ce wadda ake yankewa ranar idi domin neman yardar ALLAH, ana yin ta ne don raya sunnar Annabi Ibrahim (A.S) domin ALLAH yayi wahayi zuwa gare shi da ya yanke ɗanshi Isma'eel (A.S), sannan kuma ya fanshe shi da Rago, ya yanke shi a madadinsa.
Kamar Yadda yazo acikin Alƙur'ani ALLAH (S.W.T) Yace:
ﻭَﻓَﺪَﻳْﻨَﺎﻩُ ﺑِﺬِﺑْﺢٍ ﻋَﻈِﻴﻢٍ
Ma'ana: "Kuma mun fanshe shi da abun yanka Maigirma." [Suratul Saffat aya ta 107].
Kuma an tambayi Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) akace masa: Mene ne matsayin wannan LAYYA??? Sai yace: Sunnar Babanku ce Ibrahim (A.S). [Minhajul Muslim].
LAYYA sunnah ce ta Manzon ALLAH ( ﷺ) kuma ya kwaɗaitar da yinta ga Al'ummarsa kuma ya tsoratar ga barin yinta ga wanda ya samu iko da dama.
Manzon ALLAH (ﷺ ) Yace: “Wanda yake da wadata, kuma bai yi Layya ba, to kada ya kusanci (Filin Sallar) Idin Mu.” [Sahihul Jamii 6490].
Wasu daga cikin maganganun Magabata dangane da LAYYA:
Layya sunnah ce ba wajibi bace. [Bn baaz da Bn uthaimeen].
Layya ta halatta mutum da iyalansa da duk wanda yasa (musulmi) a cikin layyar tare dashi [Bn uthaimeen Rahimahullah].
Iyalai guda layya guda ta wadatar dasu, koda mutum yana da 'ya'ya masu aiki kuma suna da aure ana basu albashi, da sharaɗin cewa abincinsu da abin shansu gudane; ma'ana wajen dahuwar abincin guda ɗaya ne, amma idan kowanne daga cikinsu yana da wajen dahuwarsa daban to layyarsa ta saɓa da layyar sauran. [Bn uthaimeen ].
Wanda zai yanka layyar shine Wanda yake ɗauke da nauyin gidan; Uba ko Miji ko Babban Ɗa ko Babban Yaya. [Bn uthaimeen Rahimahullah].
Mace layya bata lizimceta ba, tana shigane cikin ta namiji, Uba ko Miji ko Ɗa ko Ɗan Uwa, amma da zatayi nufin zatayi layya tana da damar yin haka, sai ta hanu daga cire gashinta da farcenta kamar namiji. [Bn uthaimeen Rahimahullah].
Ya halatta ga macce tayi layya [Bn uthaimeen Rahimahullah].
Yin layya ga mamaci tana da hali guda uku, ga maganar Bn uthaimeen:
HALI NA FARKO: Mamacin da yayi wasiya cewa amai layya to sai amai a zartar da wasiyarsa.
HALI NA BIYU: Rayayye yayi wa kansa layya sai yayi niyar shigar da mamacin aciki tare dashi wannan ya halatta.
HALI NA UKU: Mutum yayi Wa mamaci layya sai dai abinda yafi kar ayi saboda Manzon ALLAH baffansa ya mutu matar sama ta mutu amma baiyi musu layya ba.
Mutum yasamu yaci bashi dan yayi layya matuƙar yana saran samun ikon biyan bashin. [Bn baaz da Bn uthaimeen].
Bayani Akan Layya
Abunda yafi kada mutum yayi layya da Rago sama da ɗaya. [Bn uthaimeen Rahimahullah].
Mai aikin hajji baya layya sai dai zai iya barma iyalansa kuɗi don su sayi abin layya su yanka wa Kansu shi kuma yayanka hadaya a Makkah bazaiyi layya ba. [Bn uthaimeen Rahimahullah].
Ya halatta ga mai aikin hajjin da yayi nufin layya ya yankata a Makkah. [Bn baaz Rahimahullah].
Ba'a layya sai da dabbobin ni'ima raƙumi, shanuwa da tumakai, dole dabbar layya takai shekarun da aka iyakance ashari'a:
1. Raƙumi biyar
2. Shanuwa biyu
3. Tunkiya wata shida
4. Akuya shekara ɗaya
lokacin da shari'a ta iyakance ayi yanka shine bayan sallar idi har zuwa kiran sallar magrib akwana na uku ga sallah " [Bn uthaimeen].
Layya ba tayi har sai in dabbar ta kuɓuta daga aibi. [Bn uthaimeen Rahimahullah].
Wannan a taƙaice kenan daga maganganun da suka keɓanci Layya.
Manzon ALLAH (ﷺ ) Yace: “Lallai ALLAH Ya hukunta kyautatawa akan komai, idan zaku yi kisa ku kyautata kisarku, idan zaku yi Yanka Ku kyautata abun yankawarku, kuma ɗayanku ya wasa wuƙarsa ya hutar da abun yankawarsa.” [Muslim].
Addu'ar da ake yi idan za'a Yanka dabba:
ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻣﻨﻚ ﻭﻟﻚ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺗﻘﺒﻞ ﻣﻨﻲ
"BISMILLAHI WALLAHU AKBAR, ALLAHUMMA MINKA WA LAKA, ALLAHUMMA TAQABBAL MINNI".
Ma'ana: “Da sunan ALLAH, kuma ALLAH ne Mafi Girma, Ya ALLAH (wannan Dabba) daga gareka take kuma mallakar kace, Ya ALLAH ka karɓa daga gare ni.” [Muslim 3/1557, Baihaqiy 9/287].
ALLAH Ya bamu iko da dama Ya kuma amsa mana dukkan Ibadun mu Amin.
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.
Tushe/Asali: www.muryarhausa24.com.ng