Tsakanin So Da Soyayya
In har aka sami ƙauna a ɓangare guda, wato shi kaɗai yake son ta, ita kuwa ko mai sunansa ba ta buƙatar gani, a nan ba a cewa suna soyayya, komai bala'in ƙaunar da yake mata, haka in an juya lamarin ma ba ta sake zane ba, idan aka sami ƙauna mai ƙarfi ko da a tsakanin jinsi guda ne, ana iya ce mata soyayya, matuƙar suna ƙaunar juna, kenan lokacin da muka ce "Wane yana son wance" sam ba ma nufin ita ma tana maido masa da irin wannan ƙaunar, wata ƙila zuciyarta tana wurinsa ko wurin wani, in kuwa muka ce "Yana soyayya da wance" To duk suna ƙaunar junansu.
Saɓanin {bege}, shi kam wata kalma ce da take nuni da samuwar ƙauna mai tasiri a zuciyar masoyi yayin da ya yi nesa da masoyinsa kuma yana da buƙatarsa a dai-dai wannan lokacin, a duk lokacin da ka ji an ce "Wane yana begen wance" to ƙaunarta ce ta taso masa alhali ba su kusa, ko ma Allah ya yi mata rasuwa, shi ya sa ake cewa " Allah ya kyauta ranar bege" shi bege ba dole ne sai mutum ya yi furuci ba, ana iya ganewa ma ta yadda yake gudanar da lamuransa, da kuma 'yan canje-canjen da aka fahimta a rayuwarsa.
Da yake {so} ko {ƙauna} su ne jigon batun da muke so mu tattauna a kai, to zai fi fa'ida mu fayyace su, wannan kalma ta {so} muna ƙoƙarin keɓance ta ne a tsakanin namiji da mace, waɗanda suke fatar su hayayyafa su yaɗu ta wurin wata gamayya, to sai dai kalmar a Hausa ba ta da faɗi kamar Turanci, wato { Love}, a Turance {Love} ana nufin { so, soyayya ne da kuma saduwa}, a Hausa kuwa hatta tsakanin so da soyayya mun bambanta.
A ƙarshe dai za mu buƙaci rayuwar Annabi (S.A.W) ta zama mana madubi, yadda za mu ga tsabar soyayyar da ba mu taɓa ganinta ko jin ta ba a rayuwarmu ta duniya, soyayya tana ɗaya daga cikin manya-manyan abubuwan da Annabi (S.A.W) ya koyar, kuma tana ɗaya daga cikin abubuwan da Allah (S.W.T) ya tanadar wa lada sama da sauran ibadu gaba ɗaya.
MAKALOLI MASU ALAKA:
Tun da kuwa soyayya ta sami irin wannan matsayi, ka tabbata dole a kewaye ta da wasu dokoki da sharuɗɗa, domin kuwa sheɗanun aljannu da na mutane ba za su bar ta kamar yadda Allah (SWT) ya yi ta ba, ba kuma za su bari a aiwatar da ita kamar yadda Annabi (SAW) ya yi kuma ya koyar ba.
Zamu Ci gaba Insha Allah.
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.
Tushe/Asali: www.muryarhausa24.com.ng