Monday, 28 September 2020

Tsakanin So Da Soyayya (03)

Tura Wannan Zuwa Ga
In dai ya kasance soyayya mutun guda ba ya iya yin ta sai tare da wanda yake maido masa da irin abin da shi yake nuna masa, to ya zama dole a wannan matsayin mutum ya zaɓi wanda zai yi musayarta, duk wani ma'abocin soyayya ko mai yin magana a kanta, in har ya fara za ka ji yana ambaton soyayya ta gaskiya, kuma yana neman a riƙa maido masa da ita.

TSAKANIN SO DA SOYAYYA

MarubuciBaban Manar Alkasim

In kuwa haka ne, mai yin ta ya zama dole tun farko ya gina ta a kan ginshiƙi mai ƙarfi, wato: Tsoron Allah, gaskiya, ikhilasi da kuma amana, ba tare da kallon wata maslaha ta duniya ko kwaɗayin wani abuba, da haka har ya zamanto farin cikin masoyi shi ne himmarsa ko da kuwa nasa ran zai ɓaci, kau da baƙin cikin masoyi shi ya sa a gaba, ba tare da ya kalli abin da zai samu bayan haka ba.

In har wannan zai samu tabbas masoyi zai kai matsayin maigadi ne na rayuwar masoyinsa, ta wajen kare addininsa, jininsa, mutuncinsa da kuma dukiyarsa, bai damu ya rasa wani abu nasa ba sabo da Allah, matuƙar nasa masoyin zai tsira.

Kenan ba ƙaramin abu ba ne, indai masoya za su iya musayar irin wannan a tsakaninsu tabbas za su sami matsayin da ba kowa ne yake iya samun kamarsa ba a wurin Allah, don haka ne ma a cikin wani hadisi na Qudusiy wanda Muslim ya rawaito Allah (SWT) yake cewa:-

إن الله يقول يوم القيامة: أين المتحابون بجلالي؟ اليوم أظلهم في ظلي يوم لا ظل إلا ظلي.

Ina masu ƙaunar junansu sabo da ɗaukakaTa? Yau zan inuwanta su a cikin inuwaTa, ranar da babu wata inuwa sai Tawa. Muslim

Shin irin wannan so da ƙaunar juna zai iya yuwuwa mu kwatanta su a tsakanin jinsuna mabambanta wato mace da namiji ko ba zai yuwuba sai dole a jinsi ɗaya, wato mace da mace, ko namiji da namiji? Ba shakka wannan zai iya zama wani batu wanda za a ɗauki dogon lokaci ana ɗauki ba daɗi, a ƙarshe da wahala a sami matsaya guda.

To sai dai a lokacin da namiji yake ƙoƙarin neman abokiyar rayuwarsa me ya gani tare da ita har ya ji yana sha'awar ta zama mai ɗakinsa? Daga nan muke fara sakin layi ko mu yi gini a kan ginshiƙi na ƙwarai da tubali mai ƙarfi, an ce ba a auren dole, sai an sami fahimtar juna tsakanin ma'auratan guda biyu, wannan kam ba wanda zai yi musun halascin hakan, sai dai tambayar wace iriyar fahimta ake buƙata?

Nan ma gardama tana iya turnuƙewa, mu marubuta muna da irin harshemmu da muke magana da shi, malaman addini suna da nasu, matasa kuma da irin tasu fahimtar, sai dai a ƙarshe duk muna ganin cewa ribar za ta koma wa ma'auratan ne.

Tambayoyin farko: Shin ka binciki halinta na saurin fushi, rashin yafiya da ba da uziri, ƙarya, munafurci da hassada, haƙuri, juriya da yafiya, ƙarancin surutu, ko ɗabi'u irin: Girmama iyaye, amana, kamun kai da tarbiyya ta ƙwarai gami da son addini, ko kuwa adonta ne da iya wanka suka janyo hankalinka ko ma wataƙila jar fata ka gani har ka ga ba za ka iya rabuwa da ita ba? Wannan amsar dai kamar tana da sauƙi amma tabbas in aka saka ta a jarabawa masu faɗi suna da dama.

Dalili kuwa an ce soyayyar Allah da Annabi ake yi amma kullum sai yaudarar juna da saɓon Allah, ƙarya, tayar da sha'awar juna, kusantar zina, da ƙoƙarin isa zuwa ga biya wa juna buƙata duk da sunan soyayya, wai kuma tsaftatacciyar kamar yadda muke alamtawa.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Abin takaici hatta iyaye suna ba da babbar gudummuwa wajen barin ɗiyarsu ta zauna da wani ƙato, su biyu, a nesa da gida, cikin duhun dare! Duk dai a hanyarsu ta fahimtar juna kafin aure, ko kuma samar da tsaftatacciyar soyayya.

Iyaka kenan? Da saura, mu tara gaba.

Zamu Ci gaba Insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user