Wani bidiyon wata basiniya 'yar ƙasar China ya karaɗe shafukan sada zumunta, wanda bidiyon yake nuni da yadda wasu 'yan ƙasar China suke hawa kan tsohuwar waƙar Hausa ta mawaƙi Abubakar Sani, anyi wa waƙar taken "ZAKKA".
Duba da yanayin yadda dukkanin su, suka hau kan waƙar ya ɗauki hankulan al'ummar Hausawa, tamkar dama sune ainihin waɗanda suka fara hawa kan waƙar ZAKKA.
Sai dai dukkannin su, sun koyi yaren Hausa ne, a ɗaya daga cikin jami'o'in ƙasar Nijeriya, inda ake yiwa macen laƙabi da KANDE yayin da ake yiwa namijin laƙabi da MURTALA.
Wasu ɗalibai ne, waɗanda suke yin karatu a ƙasar Sin, suka buƙaci su taya su ɗebe kewa da waƙar Zakka.
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin