4. Soyayya ta ƙuruciya ta bambanta da sauran da aka ambata a baya in ba ta farko ba, soyayya ce da galibi ba ta da dalili sama da burgewa, 'yammata sun san abubuwan da suke burge samari da su na kwalliya da ado, don haka a shirye suke su yi wa saurayin da suke ƙauna duk abin da yake buƙata, ko wanda suka tabbatar zai ja hankalinsa, galibin abin da ake musayarsa a tsakaninsu yana da alaƙa ne ta kai tsaye da zuciya zalla, don haka dole sha'awar saduwa ta zama ita ce ƙoli-ƙoli da komai.
Marubuci: Baban Manar Alkasim
Soyayyar ƙuriciya ta fi tsanani ne wurin:-
i. Son ganin juna da ƙaunar zama da juna, a dai sami wani dalili na mannuwa da juna, ko jin sassanyar murya, da musayar murmushi da dariya cikin zazzaƙar murya mai motsa sha'awar juna, kwalliya da nau'o'in ado da turare abubuwa ne da ake amfani da su don burge juna, in budurwa za ta zauna da saurayi ko a ɗakin mamanta ne sai ta ƙure adaka, mai yuwa ma ta sanya takalma masu tsada, don dai ta tabbatar da ta burge shi, a zatonta in zai ƙaunace ta sosai ta wannan hanyar, akwai yuwuwar samun dauwamammiyar soyayyar.
Shi kuwa namiji ba shakka yaƙi yake yi na a mutu ko a yi rai, galibin samari, masamman a matattarar da ake samun kuɗi a hannun samari, ba abin da suka fahimci soyayya kamar juya wannan kuɗin wajen mallakar zuciyar mace, ƙoƙarin saurayi kawai budurwar ta fahimci cewa zai iya gamsar da ita komai, masamman abubuwan da suka shafi rayuwa, shi ya sa ko bashin kuɗi zai yi don ya ba ta, ko ya ma ta wani abu na burgewa abu ne mai matuƙar sauƙi, ko da kuwa ba ta nema ba, har aron kaya ko mota don zuwa zance abu ne mai matuƙar sauƙi, na zauna a wata matattara wace sai budurwa ta ga irin ginin gidan saurayin kafin ta yarda a fara soyayyar.
ii. Rashin binciken yuwuwar rayuwa cikin fahimtar juna, da wahala saurayi ya tsaya duba yuwuwar cikakkiyar musayar motsin rai da mace kafin ya fara nemanta, wasu za ka taras karatu ya haɗa su, sai sun gama shaƙuwa da juna kafin a fara zancen zuwa gidajen juna, sau da yawa shawara kan rabuwa ko wani bincike yakan zama sharhin bayan labarai ne kawai, amma bai da wani tasiri ko kaɗan, duk wani hange da iyaye suke yi bai da wani amfani don ba sa ɗaukar duk wata shawara da ta saba wa mannuwarsu da juna, koda mummunan halin masoyi ya bayyana sukan raya cewa za su iya canja shi a lokacin da suka zauna da juna, ba tare da nazarin cewa wata ɗabi'ar ba ta sauyuwa cikin sauƙi ba.
ii. Yadda za ka tabbatar da cewa soyayyar ana yin ta ne kawai ido rufe ba tare da lissafi ba, da zarar masoyi ya sami tasgaro sai ka ga ya ruguje gaba ɗaya, yana iya gaya maka kai tsaye cewa ya yi asarar da ba zai iya maido da ita ba, duk da cewa babu wata hidima ta jiki da aka yi cikin sakewa da natsuwa a tsakanin juna, ba saduwa ta auratayya a tsakaninsu ta ina soyayya ta kammala bare mutum ya san ya yi asarar rabin jikinsa? Soyayya ta gaskiya ba ta hana tunani da sanya komai a mahallinsa, ita jagoranci ma take yi don kai masoyi zuwa ga biyan buƙatarsa amma ta hanyar da ta dace.
iv. Soyayyar ƙuruciya gaba ɗayanta saƙe-saƙen zuciya ne ba tare da tabbatarwa ta hanyar da ta dace ba, wasu abubuwan zai yi wahala matattara su karɓa to bare kuma addini, Annabi (S.A.W) ya nusar kan haka don a sami wani shinge a tsakanin waɗannan masoyan don tsoron aukawa kwazazzabon da-na-sani, iyaye kuma a yau suna taimakawa sosai wajen ba wa 'ya'yansu damar su kutsa cikin tekun sha'awar juna kafin saƙuwar soyayya ta gaskiya.
v. Ginuwar makwancin soyayya a zuciya kaɗai ba tare da tanadin ƙwaƙwalwa da sauran sassan jiki ba abu ne sananne a soyayyar ƙuruciya, in da za ka tsare saurayi ko budurwa ka yi wa ɗayansu tambayar ƙwaƙwaf kan cewa: Don me kake son ɗan uwanka? Bai iya cewa ga dalili sama da buƙatarsa ta kansa shi kaɗai, da wahala ya yi tunanin alaƙar matar da iyayensa, ko 'ya'yansa bare kuma 'yan uwansa, wani abu ya gani a jikinta ya burge shi, ko ita ta gani a tare da shi ya ba ta sha'awa, amma tana da damar tambayar kanta: "Shin wanga ya dace ya zamto uban yarana?"
MAKALOLI MASU ALAKA:
Bambanci Tsakanin Sha'awa Da Soyayya (1)
Bambanci Tsakanin Sha'awa Da Soyayya (2)
vi. Kasancewar soyayyar ƙuruciyya a zuciya kaɗai take, juyawarta abu ce mai matuƙar sauƙi, don ita kanta zuciyar ba ta da gaɓa guda, a don haka ko magana ce aka ce ta zuci ce ba a ɗaukar ta da wani mahimmanci, don an san yadda take, duk yadda soyayyar ƙuruciya ta kai da haɓaka, in dai ba a gina ta a turba ƙaƙƙarfa ba to ka san cewa shekaru na ƙaruwa ne ƙarfinta yana raguwa, don ƙyalkyalin abin da ya sa aka gina ta shi kansa ya fara dushewa.
Zamu Ci gaba Insha Allah.
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin