KASANCEWA
Ina son kasancewa a tare da ke na tsawan rayuwata fiye da yadda matafiyi ke buƙatar ruwa a tsakiyar sahara, fiye da yadda gangar jiki mai numfashi ke buƙatar iska, fiye da yadda tsirrai ke buƙatar hasken rana. Ina son ki tun daga babin farko na labarin rayuwata har zuwa ƙarshe. Na yi kewar rashin kasancewar ki a kusa da ni. Ki Huta Lafiya.
Marubuci: Abba Muhammad Dan Hausa
TASIRI
Duk da muna nesa da juna ina iya fahimtar yanayin da kike ciki na farin-ciki ko damuwa, ina iya jiyo bugun numfashinki a cikin zuciyata, ina iya jiyo sautin murmushinki a cikin kunnuwana. Hakan na nuna ƙarfin tasirin sonki ne a cikin jikina. Ke ce mahaɗin rayuwata. Ina Son Ki.
RAYUWA
Fatana a ce nan da watarana mu kasance tare a sabuwar rayuwa a matsayin mata da miji, har ya kasance mun mallaki 'ya'ya da zamu rayu tare da su cikin farin-ciki. Burina ki kasance a tare da ni har ƙarshen rayuwa domin samun tarin kulawar da na tanadar miki a gidan aurena. Ina Son Ki.
BURI
Burina a ko da yaushe na kasance a kusa da ke, idanuwana su zamo a cikin naki, na kasance cikin fara'a domin ki, ko da tafiya nake ya kasance kina kusa da ni, ko da magana zan yi ya kasance ke ce mai amsa tambayoyina. Ina son ki so mara iyaka da lokacin ƙarewa. Ki Huta Lafiya.
DARE
Ganin ki a cikin baccina na ɗaukaka dukkan daren da na yi mafarkinki a cikinsa fiye da sauran dararen da babu ke a cikinsu. Tinaninki ya na sanya ni murmushi. Kasancewa a tare da ke shi ne mafarkin da nake fatan ya tabbata a zahiri, son ki shi ne aikin da zuciyata za ta kasance cikin yi a tsawon rayuwata. Ina Son Ki. Ki Kwana Lafiya Cikin Mafarki Mai Daɗi.
SAKO MAI MUHIMMANCI
Kana da damar tura wa abokiyar tsinkar furenka, amma ba a amince wani ya yi amfani da shi da niyyar yaudarar wata ruhi ba. Akwai mai ganin Ka/Ki a ko'ina wato Allah. A kiyaye haƙƙin mallaka, a guje wa satar fasaha.