KIN ZARCE SAURAN MATA
Ina neman wata kalma wadda babu wanda ya santa. Ina neman wata kalma da zan furta miki cewa.....ke ta daban ce, ke kyakkyawa ce, kin zarce sauran mata. Zuciya ta da taki ba za su taɓa rabuwa ba har abada. Ina son ki.
Marubuci: Abba Muhammad Dan Hausa
SINADARIN RAYUWA TA
SO shi ne abun da ya dunƙule zuciyoyinmu waje guda har muka tsinci kanmu a cikin soyayya, ina fatan ba za ki bari wani ɗan ƙaramin abu ya zo ya raba tsakaninmu ba? Ina son ki. Ke tamkar gishiri ce a cikin rayuwa ta, idan na rasa ki zan yi rayuwa ne da babu armashi a cikinta. Ki Huta Lafiya.
ZAN SO KI JI
Da akwai wasu tarin tsintsaye da suke wuni suna tattauna batutuwa a kan irin matsayin da na baki a cikin zuciya ta. Zan so ki ji irin abun da suke cewa, domin kuwa a lokacin ne za ki tabbatar da irin son da nake yi miki. Ina Son Ki!
KE CE MURMUSHI NA
Da akwai miliyoyin furanni a cikin lambun masoya a wannan duniya. Da a ce zan tsunko kowanne fure na baki shi a hannunki, hakan bai isa ya bayyanar da adadin yadda nake son ki ba. Ke ce murmushi na, kuma ke ce farin ciki na. Ina Son Ki!
SON KI NA MOTSAWA A ZUCIYA TA
Da akwai wasu lokuta da nake zubar da hawaye saboda ke, na san za ki ce saboda me? Da akwai wani lokaci da yake zuwa na ji tamkar na yi fikafikai na tashi sama... Kin kuwa san duk saboda mene ne? Saboda motsawar sonki a cikin zuciya ta da tsintar kaina a cikin matsanancin shauƙi a dukkan lokacin da na ji muryarki ko na tina da ke.....Ina fatan za ki amince mu rayu a tare har abada. Ina Son Ki!
HMM!! KI YARDA DA NI
A dukkan lokacin da dare ya yi, ki ɗaga kanki sama ki kalli sararin samaniya, za ki ga wani tauraro yana saukowa izuwa gare ki, karda ki yi mamakin me ya sa haka ya faru? Ki yarda da ni, hakan zai iya faruwa a zahiri domin kuwa ni ma na yi hakan har ta kai ga na same ki. Hmm! Ki Huta Lafiya.
INA SON KASANCEWA A TARE DA KE HAR ABADA
A lokacin da na samu soyayyarki sai na ji tamkar ni ne na fi kowa sa'a a duniya. A dukkan sanda na rintse idanuwa na sai na hango ni tare da ke muna tafiya a bisa gajimare. Idan na kwanta bacci sai na yi mafarkin mun zama mata da miji. Ina sonki, tare da son kasancewa a tare da ke har abada. Ki Huta Lafiya.
A CIKIN IDANUWANKI AKWAI WANI SIRRI
Sama cike take da taurari masu hasken da ke haske duniya a cikin kowanne dare. Amma haske mafi haskaka fuska da yaye duhun zuciya, na gan shi ne a cikin idanuwanki. Ki Kula Min Da Kanki. Ina Son ki.
HARSHEN ZUCIYAR KI
Furanni na furta kalmomin yabo a kanki a dukkan lokacin da na shiga lambu mai ɗauke da ƙorama gami da korayen ciyayi da bishiyu masu ɗauke da tsintsaye. Sukan rera baitukan yabo a gare ki, cikin harshen da zuciya ce kawai ke iya fahimtarsa. Ina Son Ki.
BA ZAN IYA RAYUWA IDAN BA TARE DA KE BA
A mafarki da kuma a cikin soyayya babu abun da ba zai iya faruwa ba. Ina son Ki sosai hakan ya sa nake ji tamkar ba zan iya rayuwa idan ba tare da ke ba. Ba na fatan rasa ki a rayuwa ta, domin kuwa a dukkan lokacin da na rasa Ki, na tabbatar da rayuwa ta za ta shiga garari. Ina Son Ki kuma ba zan taɓa canjawa a kan hakan ba.
INA SON KA MASOYI NA!
Tsuntsaye na buƙatar fukafukai domin tashi, kifi na buƙatar ruwa domin ya yi rayuwa, ni kuma ina buƙatarka domin na yi rayuwar farin ciki. Ina son ka masoyi na!
MU KASANCE A TARE
Ina son jinka a kusa da ni, ta yadda numfashi na da naka zasu gauraya, ta yadda zan ke juyo sautin bugun zuciyoyinmu na fita a tare. Mu kasance a tare har abada. Ina Son Ka!
INA FATAN MAFARKI NA YA ZAMA GASKIYA
A kullum na kwanta bacci, na kan yi mafarkin ka zama uban 'ya'ya na, ni kuma na zama mata a gare ka. Sai dai na san iya mafarki ba zai wadatar da ni ba a bisa kulawar da nake tinanin samu daga wajenka. A saboda haka nake fatan mafarki na ya zama gaskiya watarana. Ina Son Ka!
MASOYI NA
Ina Son Ka, zan kuma ci-gaba da sonka tun daga futowar rana har izuwa faɗuwarta a cikin kowace rana har abada. Ka Huta Lafiya.
KA ZAMA RUHI NA
Ina fatan ka fahimci manufa ta? ina fatan ka gane nufi na a kanka? Zan rayu ne cikin sonka har zuwa ranar ƙarshe, saboda kai ba saurayi ne kawai a waje na ba, ka zama ruhi na, sonka na yawo ne a cikin jinin da ke gudana a jiki na. Ina Son Ka!
INA SON KI!
Ba zan iya musalta adadin yadda sonki yake lunkuwa a zuciya ta ba a cikin kowace rana. Ina son ki matata. Babu wani abinci da yake yi min daɗi a baki na matuƙar ba ke kika girka shi ba. Ina nan tafe izuwa gare ki da shirin zuwa cin abincinki mai daɗi. Ki kula min da kanki.
ZUCIYA TA NA CIKE DA KEWARKI MATA TA
Mata ta uwar 'ya'ya na. Na kan yi kewarki sosai a dukkan lokacin da na duba gefe na ban gan ki ba. kamar kullum, yanzu haka ina zaune cikin tinaninki. Zuciya ta na cike da kewarki, zan samu sassauci ne kawai idan na ji ki a kusa da ni. Ki kula min da kanki har zuwa lokacin da zan dawo kulawarki ta dawo hannu na. Ina Son Ki.
BA NI DA KAMAR KI
Na futo wajen aiki hakan na nufin mun yi nesa da juna. Amma ina son, ki san da cewa, a duk inda nake, a duk inda na shiga, ba zan rabu da tinaninki a matsayinki na mata ta da nake matuƙar so da ƙauna ba. Ina nan tafe a hanya zuwa gare ki. Ki kasance mai tina cewa, ba ni da kamar ki. Ina Son Ki.
INA ALFAHARI DA SAMUNKA
Hasken idaniya ta, annurin rai na. Miji na, uban 'ya'ya na. Tabbas samun miji irinka shi ne abun da mata da yawa suke fata. Na same ka hakan ya sanya nake jin tamkar na fi kowace mace sa'a a duniya. Ina fatan dawowarka gida lafiya, miji na abun alfahari na.
KAI NE NAKE GANI NA JI SANYI A ZUCIYA TA MIJI NA
Ina fatan kana nan lafiya miji na? Ina nan zaune cikin gida amma zuciya ta tana tare da kai. Kai ne kawai nake gani na ji sanyi a cikinta. Ina nan ina jiran dawowarka gida lafiya. Ina son ka. Ka kula min da kanka.
SAKO MAI MUHIMMANCI
Kana da damar tura wa abokiyar tsinkar furenka, amma ba a amince wani ya yi amfani da shi da niyyar yaudarar wata ruhi ba. Akwai mai ganin Ka/Ki a ko'ina wato Allah. A kiyaye haƙƙin mallaka, a guje wa satar fasaha.