Friday, 23 July 2021

Karanta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (36) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa Ga

IN KA CIZA KA HURA


Duk wani mai biɗar nasara a rayuwarsa ya san sai ya dage, amma wace iriyar dagewa? Hausawa kan faɗi "Rai dangin goro, ban iska yake so" ba yadda mutun zai ce kullum aiki ba hutu, ka je wurin aikinka amma ka sami lokacin da za ka ɗan huta da iyali, gobe sai ka ji daɗin fitowa da ƙarfi, idan kai ɗan kasuwa ne ka ga kiristoci ba sa fitowa sana'a ranar lahadi saboda addininsu, in ka fito sai ka fi samun ciniki don shagunansu a kukkulle, ƙila ma su kansu in suna buƙatar wasu abubuwan su zo wurinka su saya.


Rai Dangin Goro

MarubuciBaban Manar Alkasim


Nemi wata rana ka fito aiki amma ka tashi da wuri, saboda ka koma wurin iyali, kodai ku yi wasa a gida ko ku je ziyara wasu wuraren, za ka ɗan huta kuma yaranka za su gan ka, ko ba komai ranar za a sauya baki ta wurin cin wani abincin, bare kuma za ka rage mata yawan bari-bari da ƙiriniyar yara, ko dai su zo wurinka su yi wasa, ko in ƙananan su natsu, ƙila ma ka sayo musu wasu ƙananan abubuwa da suke buƙata, duk dai a dalilin kasancewarka a gida, ba yadda za ka haɗa farin cikin mace a lokacin da maigidanta yakenan da lokacin da bayanan.


Na ɗan fita wasu matattarar sai na ga wasu in suka so shan iska sukan ɗauki matansu ne su bar ƙasar da su, su je Dubai ko Saudia da sauran wurare, na ce masu kudi ne, wasu kuma sukan ɗibi iyalin ne su je bakin kogi suna kallon ruwa suna shan shayi, na san wannan ma ba za mu iya ba, wasu sukan ɗebi iyalin ne su shiga kasuwa a sayi abinda rai ke so, shi ma yana da alaƙa da wadata, talaka ba zai iya ba, wasu sukan kwashi matansu ne da yara su leƙa gidanjen shan iska, shi ma ɗin addini da ala'ada ba zai ɗaga mana ƙafa ba, hatta fita unguwa da iyali gaskiya ba kowa zai iya ba, ƙila sai dai zama da iyalin a yi wasa da dariya, wannan kam sai dai mutum ya ƙi yi.


In ya zauna a cikinsu ana ɗan wasa da dariya koda sau ɗaya kawai a mako abin zai yi kyau, yaranka za su sami cikakkiyar sakewa da tambayarka abin da suke so, ko su kawo maka kukan abinda yake damunsu, ko ka faranta musu rai kamar dai yadda suke buƙata, kai ma ka sami natsuwa ga lada tsagwagwa daga mahalicci, in ba ka yi hakan ba to zai kasance jikinka na son hutu, dole ya buƙaci waɗanda za su riƙa ɗebe maka kewa koda ba iyalin naka ba, haka su ma iyalin in ta ƙure musu su buƙaci wanda zai ɗebe musu kewa koda ba kai ɗin ba, ka ga ɗaukar mataki tun wuri ya zama dole kenan.


Kwanaki aka kawo hirar wata matar talaka, malama ce a makarantun boko, ta ga ƙoƙarin yaron ajinta kullum sai baya-baya yake yi, a ƙarshe ta daure ta sami mahaifiyarsa da take kawo shi kullum ta gaya mata abinda yake faruwa, sai uwar ta ce "Wallahi ko ni in zan gaya miki irin zaman ƙuncin da muke yi za ki san muna cikin damuwa, ba ma yaron ba" malamar ta so ji ko za ta iya taimakawa da shawarwari yadda dai za a ƙwato jin daɗin rayuwar a dawo da shi, ta ce "To! Allah masani, amma ga ku ɓulɓul, fesfes, kullum a manyan motoci cikin fara'a da walwala anya akwai damuwa anan?"


Matar ta ce "Wallahi in da ina tare da maigidana a gidan haya, kullum sai ya fita mu samu abinda za mu ci ya fi min wannan bala'in da muke ciki, mace da mijinta sai kwana biyu ko uku za ta ganshi, in ya zo da ayyuka sai ta haɗa wata biyu ba ta gan shi ba, to in za ta ci abinci mai kyau bayan ta ƙoshi mai kike tsammani?" Malama ta ɗan ba da shawarwari matar ta tabbatar mata da cewa wallahi za ta kashe auren kuma ba ta ma damu ko wa za ta aura ba matuƙar yana gida tana ganinsa a gabansu yana sauke haƙƙinsa na aure.


Koke-koken mata game da rashin zaman maza a gida ya yi yawa, ya kamata mazan su fara duba lamarin, mun samu wace uwayenta suka yi ta ba ta haƙuri har dai a ƙarshe ta gudu gidan 'yan uwanta, bai iya sauke haƙƙinsa, ta yi, ta yi ya nemi magani ya ce shi ya riga ya girma bai buƙatar komai, ta nemi ya sawwaƙe mata shi kuma ya ce yana ƙaunarta ba zai iya ba, wata shekaranta takwas ta fita, ita ma duk dai matsala guda ce, maigidan bai da lokacin kula da iyalinsa, bai iya yin komai in ya dawo, wata 'ya'yanta takwas tana haƙuri kuma ba ta nuna damuwa, amma yanzu kafofin sadarwa na zamani sun fito ta gano akwai abinda take rasawa, a ƙarshe ta fita.


DUBA WANNANKaranta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (37) Cikin Sauki


Akwai wace mako ɗaya tal aka yi ta ƙara gaba, wata bazawara har an sa rana ta tsare angon ta yi masa tambayoyi game da mazantakarsa, ƙarshe auren da ba a yi ba kenan, don ya fito ƙarara ya nuna mata cewa zai iya yi mata komai na rayuwa in ba haƙƙoƙinta na shinfiɗa ba, ta ce abinda ya raba ta da tsohon mijinta kenan, shi ma an fasa, don samun nasara a gidajen aurenmu ya zama dole mu kula da iyalanmu kamar yadda muke kula da ayyukammu da sana'o'immu.


Zamu Ci gaba Insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin

aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user