Thursday, 14 November 2019

ALLAHU AKBAR: TA YI NASIHA MAI RATSA ZUCIYAR DUK WANI MAI IMANI JIM KADAN TA RASU

Tura Wannan Zuwa Ga
Nasiha daga wata wadda Allah ya karɓi rayuwarta mutuniyar (kuwait) mai suna (Nadia Aljarullahi) Allah yayi mata rahama Amin.

ALLAHU AKBAR


Ta rubuta nasihar kafin mutuwar ta da ƴan makwanni.

Tana faɗin:

Yaƴin da na mutu bana cikin damuwa,

Ba na ta jikina wanda ya riga ya gama aiki.

Musulmai su ne zasu aikata mini komai game da shirya gawata zuwa makwanci.

1- zasu cire tufafin da ke jikina.

2- su wanke ni tas.

3- su sanya ni cikin likkafani.

4- su fiddoni daga cikin ɗakina.

5- domin tafiya da ni sabon masaukina wato (ƙabari).

6- Mutane da yawa zasu taru domin rakani makwanci na.

Kai zaka samu mafi yawa ma ayyukan su suka ajiye domin halarta sakani makwanci na.

Tare da hakan zaka samu mafi yawa daga jama'ar ba za suyi tunani akan nasiha ta ko da rana ɗaya ce a cikin rana ku.

7- Dukkan abubuwan da na mallaka a ranar zan rabu da su.

Kamar su:

1. Makullan dukiya ta
2. jikkunan da na mallaka
3. Takalman dana mallaka
4. Suturar dana mallaka.

Idan Allah yasa na dace da iyalai masu nagarta su yi sadaka da su domin amfanata a lahira.

Ku sani fa cewa Duniya babu wani baƙin cikin rabuwa dani da zatayi.

Haka kuma harkar da ake gudanarwa a cikin duniya zai ci gaba da gudana.

Aiki na kuma wani yazo ya ci gaba da yin sa a madadina.

Dukiya ta kuma ta zama halas ga magada.

Tare da cewa ni za'ayi ma hisabi akan tara ta da na yi.

Kaɗan ce ko mai yawa ce.

Kwatankwacin farar fatan dake kan kwallon dabino ce ko zaren dake tsakiyar kwallon dabino ce sai dai an yi mini hisabi akan ta.

Farkon abunda zai ɓace ma mutane nawa shi ne suna na.

Saboda haka zaka ji mutane na faɗi ina gawar mai mutuwar?

Ba zasu taɓa kiran suna na ba.

Yayin da zasu yi mini sallah, zaka ji sun ce a matso da gawar.

Ba zasu kira suna na ba.

Yayin da za'a sani kabari sai ka ji an ce a matso da gawa.

Saboda haka yasa kasantuwata 'yar wani mai matsayi ko kuma 'yar wata babbar ƙabila, ko kuma mai matsayi babba baya taɓa ruɗata.

Me ƴa kai duniya wulakan ta!!!

Babu abunda ya kai girman rayuwar da zamu iske a lahira.

Yayin da Za'a Binne Mamaci


Ya kai wanda kake raye a yanzu ka sani zaka gamu da bakin cikin guda uku:

1- Mutanan da suka sanka sama sama zasu riƙa faɗar Allah sarki bawan Allah ya rasu.

2- Abokan ka zasu yi bakin ciki na ƴan awowi ko kuma kwanaki daga baya su ci gaba da harkokin su har suna dariya.

3- An daɗe ana bakin ciki a cikin gidan ku ƴa kai mako ɗaya ko biyu ko kuma wata ko wata biyu ko shekara.

Bayan nan sai su ajiƴe ka a cikin littafi na tarihi.

Rayuwar ka ta karya ta kare, ta gidan duniya.

Ka fara rayuwa ta gaskiya ita ce ta gidan lahira.

Ka rabu da:

1- Kyawon dake gare ka

2-Dukiyar da ka mallaka

3- Lafiyar dake ggare ka

4- 'Ya'yan da ka haifa

5- Ka rabu da benayen da ka mallaka

6- Matar ka

Babu abunda yayi maka saura sai aikin da ka aikata.

Daga nan zaka fara rayuwa ta gaskiya kuma marar iyaka.

Tambaya a nan:

Me ka tanadar ma rayuwarka ta ƙabari da kuma ta Lahira ??

Ka sani wannan al'amari ne dake bukatar tunani mai zurfi.

Saboda haka kayi ƙoƙarin kiyaye waɗannan abubuwan kamar haka:

1- Aikata farillai

2-Aikata nafilfili ko nafiloli

3- Yin sadaƙa a boye

4- Ayyuka masu kyau

5- Sallahr dare

Ko ka samu rabauta lahira.

Idan Allah ya datar da kai kana daga cikin masu taimakon mutane ta hanyar tunatar dasu wannan zantukan masu muhimmanci?

To ka sani zaka samu ladar ka a cikin littafin ka na kyawawan ayyuka.

وذكر فان الذكري تنفع المؤمنين

Saboda mamaci ya kan zaɓi yayi sadaka idan Allah ya ara masa damar komawa duniya.

Allah na faɗin

رب لولا اخرتني إلى   أ جل قريب فاصدق

A yayin da bawa ƴa zo mutuwa ya kan faɗi cewa ya Ubangiji da zaa jinkirta mini ya zuwa wani lokaci da na yi sadaƙa

Bai ce da yayi

1- Hajji ba ko Umra

2- Ko sallah
3- Ko azumi

Malamai suka ce mamaci bai ambaci yayi sadaka ba sai don ganin girman ladar sadaƙa da ya gani a yayin da ya mutu.

MAKALOLI MASU ALAKA:

DAN ALLAH KUBANI MINTI BIYU KU KARANTA WANNAN NASIHA

HANKALI NA YANA TASHI IDAN NA TUNA DA WANNAN

ME KUKA SANI GAME DA LITTAFIN KU AL-QUR'ANI MAI GIRMA?

Don haka ku yawaita sadaƙa, ku sani mumini ƴana cikin inuwar sadakar sa a ranar ƙiyama.

Daure kayi sadakada  (Ka turawa 'Yan Uwa da Abokanan Arziki) sakan 10 a cikin lokacin ka domin mika wannan saƙo da niyyar yin nasiha.

Ka sani kalma mai daɗi sadaka ce.

Allah yasa Mu dace Duniya da Lahira Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user