Saturday, 29 June 2019

Kalli Hotunan Wacce tafi kowa Kyau a Nigeria (Sarauniyar Kyau ta Nigeria)

Tura Wannan Zuwa Ga
Kamar yadda shafin MuryarHausa24.com.ng ya shahara wajen kawo muku sababbin hotuna masu inganci waɗanda suka fi ɗaukar hankulan shafukan sada zumunta.


Aisha Ahmad


Waɗannan wasu  ne daga cikin zafafan hotunan wacce tafi kowa kyau  a Nijeriya.


Aisha Ahmad

Kyakkyawar budurwar Aisha Ahmad ta lashe wannan gasa ne bisa la'akari da yadda ta tsallake mata kimanin sama da guda hamsin da suka shiga cikin gasar kyau a Nigeria.


Jerin 'yam matan da suka shiga gasar Kyau a Nigeria


A halin yanzu Aisha Ahmad ita ce take riƙe da kambun kyawawan Jihar Kano (Miss Kano) Wadda tafi kowa kyau a jihar Kano.


Sai da aka tantance ta kafin takai wannan matsayi na sarauniyar kyawawa a arewacin Nijeriya cikin jihar Kano.


Sharhi




Aisha Ahmad ta wakilcin milliyoyin kyawawan jihar kano inda ta ciri tuta a matsayin wacce tafi kowa kyau a jihar Kano.


Sai dai wasu daga cikin al'ummar Jihar Kano dama duniya baki daya sunce sam-sam wannan abin akwai son Zuciya  ta ya ya za'ace itace tafi kowa Kyau akaf faɗin jihar Kano? Wannna zance ne kawai.


Sharhi


Sai dai wasu sun ce ba abin mamaki bane don tafi kowa kyau kasancewar Kanawa basa bin tsarin Yahudu da Nasara, kuma suna Allah wadai da shigar wannan baiwar Allah cikin wannna gasar.


Sharhi


Yayin da wasu suka ce "Idan har wannan tafi kowa Kyau a jihar Kano , tofa Kanawa baku da kyau gwara mu tsaya a jihar Borno mu auri 'ya'yan mu".


Sharhi



Wani mazaunin jihar Kano Yace "Gaskiya Mu Kanawa an raina mu, wannan ai sai dai ace tafi kowa muni amma badai kyau ba".


Sharhi



Bayan biyo ƙorafe-ƙorafe da mutane suke yi a ciki da wajen ƙasar nan, sai aka samu wani yana Cewa "Gaskiya ne wannan duk wacce take da ja  to hassada ce".




Sharhi



Wani ya baiwa kowa dariya sosai a lokacin da yace "Wallahi Koshi da yake Namiji yafi ta Kyau".


Sharhi


Wasu dai sun nuna rashin jin daɗin su ƙarara akan zaɓen Aisha Ahmad  a matsayin Sarauniyar Kyawawan Jihar Kano "Wannan sai dai taci gasar munana zata iya ci amma kyawawa karta kawo kanta wajen su, masu zaɓen jakai ne indai ita suka ɗauko a matsayin kyakkyawa".


Sharhi


A karshe sunyi fatan Allah yasa abin ya tsaya iyakar nan.

Sharhi





Kalli Hotunan Wacce tafi kowa Kyau a Duniya (Sarauniyar Kyau)




Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user