Sace Zuciya
1. TSARI: Duk wata ‘ya mace tana son ta ga namiji mai tsari, ba wai tsari irin na magana ba, abin da nake nufi da haka shi ne, namiji ya kasance yana da tsarin rayuwa mai kyau, ba mutum ya zama shashasha maras kan gado ba.
2. KYAU DA KWALLIYA: Wasu matan suna son mutum mai kyau da kwalliya ba irin su wancan nanka ba, sau da yawa za ka ga mata suna soyayya da saurayi saboda tsabar kyau da Allah ya ba shi, da kuma iya kwalliya kamar ɗawisu.
3. KALAMAI: Yana da kyau Namiji ya zama ya iya kalaman da za su janyo hankalin duk wata ‘ya mace, rashin iya kalami kan janyo rashin masoyi, maimakon haka sai ka zama tamkar ɗan bora a soyayya, dole ne ka kasance ka iya kalaman da zaka birge budurwa.
4. KIRKI DA KULAWA: Namiji yakan tafiyar da zuciyar 'ya mace dalilin kasancewa mai kulawa da kirki, Misali; duk bayan wani lokaci ko sa’ar da ba ta fi rana ɗaya ba ko kwana biyu a ce kana zuwa ganin ta ko kuma kana kiran ta, idan ya yi yawa ne a ce kun haɗu sau uku, musamman ma a irin wanan lokacin da wayar hannu ta zama ruwan dare.
Wani lokacin idan haɗuwa ta yi ƙaranci sai ka kirata a waya amma fa ka sani yawan zuwa gun mace ko masoyiyarka ce wani zubin nasa gundura, ma’ana za ta ji duk ta gaji da ganin ka, musamman idan ya zama soyayyar taku ba ta yi ƙarfi ba.
5. KAR KA RIƘA YAWAN YI MATA MAGANA A GABAN ƘAWAYE: Ka guji yawan kula yarinya cikin sahun
ƙawayenta ko kuma cikin jama’a, hakan zai ƙarama kima, sannan da nesanta kanka ga barin wulaƙanci.
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.
Tushe/Asali: www.muryarhausa24.com.ng