Matasa da dama na samun kawunansu cikin zullumi wajen zaɓen neman aikin yi, ko kuma kama sana'a. Wanne ne ya fi? Idan kana ɗaya daga cikin waɗannan mutane, to bari mu warware maka bakin zaren.
Marubuci: Bello Galadanchi
Za mu kwatanta samun aiki a kamfani ko masana'anta da fara naka sana'ar akan ɓangarori kamar haka:
1. LOKACIN AIKI: Idan kai ma'aikaci ne, to za ka shafe tsawon sa'o'i arba'in zuwa hamsin a ofis ko masana'anta tare da abokan aiki. Kullum, da ka gama aikin sa'o'i takwas zuwa goma, sai ka tafi gida wajen iyalanka.
Amma idan ka fara sana'a taka ta kanka, to fa wani lokacin babu dare babu rana. Ko yaushe a cikin aiki kake. Sannan kuma ba ka da shugaba balle ka yi gardama da shi.
2. RAYUWAR GIDA DA NA AIKI: Shi ma'aikaci, da ya gama aikinsa na wannan rana, sai ya tafi wajen iyalansa ya manta da batun aiki. A ɗaya ɓangaren, idan ka ce za ka kama sana'a, to akwai lokuta da dama da za ka samu kanka a cikin zulumi wajen daidaita rayuwar gida da na aiki.
3. RASHIN TABBAS: Idan aiki ne da kai, ba ka da damuwa sosai, saboda abunda kawai kake da buƙatar yi shi ne kaje wajen aikinka, ka yi abunda aka saka ka. Da lokacin gama aiki yayi, ka tattara naka ka tafi gida. Idan wata ya zo ƙarshe, kana zaune za ka ji "alert".
Amma in ka ce sana'a za ka yi, to ba ka da tabbacin daga inda albashinka zai fito, saboda haka kullum kana cikin tunanin hanyoyin samun kuɗaɗen shiga. Cikin dare ɗaya komai zai iya watsewa.
Na kashe muku gwiwa ko? Amma karku damu. Yanzu bari mu yi tsokaci akan muhimmancin fara sana'arka da kanka.
1. BABU MAIMAITA ABU ƊAYA KULLUM: Kowace rana ta na da irin nata ƙalubale. Aikin yau daban, na gobe daban. Babu ruwanka da maimaita abu ɗaya kullum-kullum.
2. ALFAHARIN ZAMA MAI SANA'A: Za ka yi matuƙar alfaharin gaya wa jama’a cewa wannan kamfaninka ne, ko waɗancan kayan a kamfaninka ake ƙera su.
3. ARZIKI: Wannan yana da muhimmanci. Idan a masana'anta kake ko gwamnati kake wa aiki, to albashinka a lissafe yake. Ka san ko nawa za'a biya ka a ƙarshen wata.
Amma idan sana'arka ka fara, to kuɗi kuwa sai abunda Allah ya yi. Adadin arzikin da za ka samu ya danganta da ire-iren shawarwarin da kake yanke wa.
Saboda haka sai kayi nazari ka zaɓi wanda yafi dacewa da kai. Idan shawara ta kake so, to gaskiya ka fara sana'ar ka daga tushe. Babu shakka akwai matuƙar ƙalubale a farko, amma idan har ka jajirce, ka fahimci sana'ar yadda ya kamata, to za ka samu nasara da ikon Allah.