Wednesday, 10 August 2022

Bambanci Tsakanin Tunanin Mai Kudi Da Na Mai Arziki

Tura Wannan Zuwa Ga

1. MAI KUƊI NA RAYUWA NE A CIKIN WADATA  – MAI ARZIKI KUWA BA SHI DA MATSALA WAJEN TAFIYAR DA RAYUWA A TAKURE


Tunanin Mai Kuɗi shi ne zama cikin wadata ne gimshiƙin farin ciki, shi kuwa Mai Arziki ya fahimci cewa saka kansa a cikin takura na buɗe idanunsa da ba shi hikimomin warware matsalolin da za su ba shi damar ƙirƙirar hanyoyi masu ɗorewa na samun kuɗaɗe. Babu shakka fara sana’a jefa kaine a cikin takura da kasada, amma kuma sai da kasada ake buɗe ƙofofin alherin da ragowar jama’a suke tsoro da fargaba. Ka rungumi zama cikin takura. Akwai ƙalubale, amma farashin da za ka biya kenan domin cimma burinka na rayuwa.


Abin da ya bambanta tsakanin Mai Kuɗi da Mai Arziki
Hoto: Istockphoto


MarubuciBello Galadanchi


Ka yi watsi da zama cikin wadata, sannan ka nazarci ire-iren damammakin da kake da su. Yin aiki a ƙarƙashi wani zai iya ba ka wadata, amma idan kana so ka yi arziki, to dole sai ka shiga takura. Za ka iya faɗuwa, kuma wannan abu ne da zai ƙara maka hikima da hangen nesa. Idan ba ka faɗi ba, to ba ka aiki tuƙuru


2. MAI KUƊI NA RAYUWA NE FIYE DA HALIN DA YA KE DA SHI – MAI ARZIKI KUWA A SAUƘAƘE YA KE RAYUWA


Zai yi wahala ka ga mai arziki yana tuƙa motar miliyoyin naira irin wadda babu kamar ta a garin baki ɗaya, ko ya zauna a katafaren gidan da duk garin babu irin shi. Masu arziki ba sa sayen kadarorin da darajarsu ke faɗuwa, sun fi mayar da hankali wajen mallakar kadarorin da darajarsu ke ƙaruwa. Mafi yawancin masu arziki suna amfani da motoci ne waɗanda ba su da tsada sosai, kuma sukan daɗe ba su canza ba. Ka tuna cewa idan kana samun naira miliyan goma a shekara, sannan kana kashe naira miliyan goma a kowace shekara, to ba ka da ko sisi. Babu abun sha’awa da mutuntawa kamar mutumin da ke rayuwa dai-dai ƙarfin da Allah ya ba shi. 


3. YUNƘURIN MAI KUƊI SHI NE YA SAMU ƘARIN MATSAYI A WAJEN AIKI – MAI ARZIKI KUWA SHI NE YA MALLAKI WAJEN AIKIN


Mafi yawancin masu kuɗi suna aiki a ƙarƙashin wani ne. Suna da aikin yi, amma mafi yawancin masu arziki kuwa sun mallaki sana’o’in kansu ne. Masu Arziki sun fahimci cewa suna buƙatar mutane su yi aiki a ƙarƙashin su domin dukiyar su ta ƙaru. Masu arzikin duniya na mayar da hankali ne wajen ƙulla dangantaka, ragowar jama’a kuwa albashi suke nema.


4. MAI KUƊI ABOKIN KOWA NE – MAI ARZIKI KUWA SAI YA ZAƁA


Masu arziki sun fahimci cewa idan suka zagaye kansu da matanen da suka yi nasara a rayuwa, to su ma za su yi nasara. Idan kuwa ka zagaye kanka da mutanen da zuciyar su ta mutu, to babu shakka za su kashe maka zuciya. Arzikinka kusan ɗaya ya ke da na abokan ka guda uku, saboda haka idan kana so ya ƙaru, to ka fara mu'amala da mutanen da suka fi ka hali. Muhimmin abu shi ne ka fahimci yadda mutane masu nasara suke tunani. Idan kana so ka yi arziki, to ka fara tunani kamar mutane masu arziki. Ka tabbatar kana share lokaci mai yawa tare da mutanen da suka fi ka nasara a rayuwa.


5. MAI KUƊI NEMAN KUƊI YAKE – MAI ARZIKI KUWA NEMAN ILIMI YAKE


Babu wuya Mai Kuɗi ya canza aiki ko sana’a idan har ya ga inda zai samu ƙarin kuɗi. Mai Arziki ya fahimci cewa nufin aiki tuƙuru ba don neman kuɗi ba ne kawai, musamman a lokacin da yake da ƙuruciya. Wannan lokacin na neman ilimi ne da halaye, da hikimomin da za su kaisu ga samun kuɗi. Mai Arziki zai iya kama aiki a matsayin akawun shago domin fahimtar yadda duniyar saye da sayarwa take, ko kuma aiki a banki domin laƙantar tsarin kuɗi da amfani da shi. Idan har kana so ka yi arziki, to ka dinga neman aiki saboda neman ilimi da hikimomin da za su sa ka yi arziki. Albashi ba zai sa ka yi arziki ba. Idan kana da ƙuruciya, to ka yi ayyuka domin neman ilimi, ba don neman kuɗi ba.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user