Duk wani manomi ba sai an gaya masa abin da ya kamata ba wajan kula da gonar sa. Ya san lokacin da gonar keda buƙatar ruwa, taki, ko feshin kwari. Duk Yana hakane don a samu yabanya mai kyau domin ya girbi alkhairin abin da ya shuka ba tare da hasara ko ɓacin rai ba.
Marubuci: Nura Nakowa
Ita zuciya tana buƙatar kulawa. Kamar su ɗaya da shuka dole sai da banruwa.
Saboda haka so gona ce sai ana kewayawa domin sanin halin da take ciki domin abin da rai ke so bibiyarsa yake yi domin sanin ingancin sa.
Rashin sanin hali ko yanayin da masoyi ke ciki tamkar rashin damuwa da shi ne. Ya zama tamkar tuwo ne babu miya, domin ɗaya ya damu da soyayyar amma kuma ɗayan bai damu ba. Shi yasa a soyayya ake son kulawa akai-akai domin jaddada ƙaunarka ga wanda kake so.
Zuwa gurin masoyi da kyakkyawar manufa domin a zanta yana ƙarawa masoyi martaba a zuciyar wanda yake so. Idan ba ka je ba da akwai wasu hanyoyi dayawa waɗanda za su maye gurbin rashin zuwanka wanda kuma suna daga cikin abin da muke magana akai cewa 'So Gona Ce Sai Da Gewaya'. Daga ciki da akwai yin aike ko tura saƙo, ko kuma idan ka samu ka zo ka yi bayani ko ka aikata abin da zai burge masoyin ka wanda zai sa ya manta da kewar ka da yayi na wasu lokutan. Yin hakan zai sa ka ci ribar soyayyar ka.
Da akwai abubuwa masu yawan gaske waɗanda su suke sawa so yayi ƙarko.
Kamar:-
- Bada lokaci da kulawa.
- Ihisani ko alkhairi.
- Kawar da zargi da ƙorafi.
- Rusunawa da rarrashi.
- Soyayya ba ta son gaggawa.
- Sai da lallaɓawa ake satar zuciya.
Akwai sirrika da yawa a cikin soyayya, kuma wanda ya san sirrin so shi yake ƙirga riba.
Wai shin, mene ne sirrin so kuma ya ake ƙirga ribar so..?
Mu hadu a rubuta na gaba.
Rubutu na zai dinga zuwa muku a tsakanin ranakun litinin, laraba da juma'a.
Muna maraba da saƙonnin ku dakuma tayamu sanar da wasu labarin wannan shafin.