Tuesday, 13 September 2022

Karanta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (46) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa Ga

BURINA NA ZAMA MAI SUKUNI


Burinka kenan? To ya kamata ka sa idon lura sosai ka gane: Idan kana aikin gwamnati ne wanda ta hanyarsa ce kake samun kuɗi masu ɗimbin yawa, kamar dai ɗan siyasan da aka buɗa masa ya sami wani babban matsayi, kuɗi na zuwa masa ta ko'ina, wannan ba a la'akari da shi a matsayin mai tabbataccen kuɗi, matsayinsa daidai da wanda mahaifinsa ya rasu ne ya bar shi da tarin dukiya mai ɗumbin yawa, kuɗin na zube kuma ana ganin cewa nasa ne, a zahiri ba haka abin yake ba.


Jin Daɗi
Hoto: BM MAGAZINE UK


MarubuciBaban Manar Alkasim


Akwai wata 'yar gada a tsakiya, tabbas sun rabu da mahallinsu na asali zuwa wurinsa, shi kuma dole ya yi aiki don samar musu da mahalli a wurinsa, ba shi ya sha wahalar tara su ba, don haka kashe su ta kowace hanya abu ne mai sauƙi a wurinsa, idan muka lura da kyau wasu kansilolin da shugabannin ƙananan hukumomi gami da kantomomi na madafan iko iri daban-daban da zarar sun rabu da mahallan aikinsu sai ka nemi kuɗin ka rasa, kwashe su aka yi ko bayar da su suka yi kyauta oho. Haka waɗanda suka gaji maƙudan kuɗaɗe daga mahaifansu idan ba dace aka yi ba bayan wasu 'yan shekaru sai ka nemi waɗannan kuɗaɗen ka rasa, babban dalili kuwa shi ne ba a yi wa kuɗaɗen mahalli mai kyau da za a ajiye su ba.


Kuɗi duk yadda suka kai da yawa idan ɗibar su ake yi ba ƙarowa ba, tabbas raguwa za su yi ta yi har a neme su a rasa, wanda ya gaji dukiya mai bala'in yawa a lokaci guda, ko kuɗin siyasa suka riƙa shigo masa ta ko'ina akwai buƙatar ya yi tsari na yadda za su ci gaba da ƙaruwa sosai. Wannan tsarin wani abu ne mai matuƙar wahala ga wanda ba ya sana'a ko ba Ɗan kasuwa ba, domin a wannan lokacin yana da buƙatar sanin makama, idan ba haka ba waɗanda ke zagaye da shi za su iya wawurewa ba tare da ya sani ba, tsoron faruwar hakan sai ya bar kuɗinsa a banki yana figa kaɗan-kaɗan, an kama hanyar cinye abin da aka taskace kenan.


Kwanakin baya aka ba mu labarin wani ma'aikacin siyasa da ya sami maƙudan kuɗi da ake lissafa su da miliyoyi, ya sayi gidaje da manyan benaye na shaguna, gami da filaye a wurare daban-daban, yana da tsabar sulalla a banki, idan ka lissafa abin da zai riƙa samu na hayar gidajennan da shaguna kuɗaɗe ne masu yawa, za su ishe shi ya gine filayen da ke ƙasa ya zuba 'yan haya, amma sai ya haɗe wasu gidajen  ya samar da irin tabkeken gidannan da shi kaɗai yake ciki sai matan shaƙatawa da ke masa ɗawafi a kowani lokaci, motar da yake hawa ta miliyoyi ce, a zagaye da shi ga 'yan ku-ci ku-ba munan a duk inda ka duba, lokacin da aikinsa ya ƙare sai rayuwar ta canja, ya riƙa sayar da kadarorinsa ɗaya bayan ɗaya, har dai ya dawo ƙaramin gidan da yake ciki, shi ma ya sayar da rabi.


Kai da jin wannan ka san ba a yi wa dukiyar tsarin da ya dace ba, abin da yake faruwa kenan da masu gadon dukiya su ma, iya tsare dukiyan ba tare da sanin makama ba, abu ne mai matuƙar wahala, shi kuma sanin makamannan karatu ne, koda kuwa mutum ba zai shiga aji ba, bari na ba ka misali, wani shugaban 'yan kasuwa ne da ake yabonsa da riƙon amana da adalci, aka ba shi shawarar shiga siyasa, abokan sana'arsa suka mara masa don a ƙarshe alfanun da zai samu zai dawo musu ne, wato dai nasu ya samu, abin da ba su sani ba shi ne kowane gida da tsarinsa da kuma irin mutanen dake cikinsa, gwaninsu na ɗarewa karaga ya canja abokan tafiya, sai suka fara ganin kamar ya baɗa musu toka a fuska, suka fita harkarsa.


Ya sami kuɗi tabbas, kuma dama shi ma Ɗan kasuwa ne, ko na ce sarkin kasuwan ma, amma da ya sami kudi irin waɗanda ba su yake kamawa ba a baya, sai bai yi tsarin sanin makaman riƙe su ba, ƙarshe da ya sauka ba a jima ba ya dawo cikin jama'arsa, su kuwa suka yi ta ajiye masa maganganu, ba abin da yake iya cewa, bisa waɗannan dalilai ya zama dole mu dubi masu kama kuɗaɗe da yawa a wata dama da suka samu na ɗan ƙaramin lokaci, shin za mu iya la'akari da su a matsayin waɗanda suka ci nasara a rayuwa? Amsar dai ita ce "A'a!" To idan sun ajiye waɗannan maƙudan kuɗaɗen a banki me zai sa ba za mu yi la'akari da su a matsayin masu cin nasarar ba? Amsar dai ita ce sai sun mayar da kuɗin ya zama rainonsu tukun.


Wato su juya kuɗaɗen ta wata hanya yadda za su dawo da riba, ko kuma su nunku a sanadiyyar ribar da aka samu, ya zama an yi musu wani tsari mai ƙarfi wanda za su riƙa ƙaruwa ba ƙarewa ba. A wannan matsayi ko mutum ya rabu da aikinsa ba za a iya ganin wani canji mai girma ba, kuɗin sun zauna kenan, in ma gado ya yi, ya sami nasarar juya kuɗin gwargwadon sanin makaman da ya yi, sai dai a ga kuɗaɗen na ƙaruwa ba wai ƙarewa ba, idan muka lura da duk bayanan sama, za mu gane cewa rashin tabbataccen tsari na ƙaruwar kuɗi shi ne yake sa shi ya ƙare.


DUBA NA GABAKaranta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (47) Cikin Sauki


Na sami labarin wani kansila da ya yi ta yi wa wani babban mutum alkhairi kan sharaɗin idan ya sauka zai samar masa aiki, na ce ya san abin da yake yi, wani kuwa ya faɗaɗa sana'ar gidansu ne, ya yi ofis wanda zai riƙa zama idan ya sauka ya ci gaba da sa ido, shi ma ya yi ƙoƙari gaskiya. Wani da ya yi gadon maƙudan kuɗi bai canja komai na rayuwarsa ba, sai ya koyo sana'ar mahaifin ya ci gaba da ita, yanzu haka ana ganin kamar ya fi shi kuɗi, na ce da a ce ya sayi ƙaton gida, ya canja mota da abokai, ya auro irin jajayen matannan, da wani Turancin ake yi ba wannan ba.


Za mu ci-gaba Insha Allah.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user