A taƙaice, akwai alamomi guda uku da suka yi fice wajen nuna mutane masu matuƙar basira.
Marubuci: Bello Galadanchi
Ga su kamar haka;
1. RASHIN TSORO DA FARGABA WAJEN BAYYANA ABIN DA BA SU SANI BA
Mutane da dama na jefa kawunansu a cikin tarko, na nuna cewa sun san abin da ba su sani ba. Wani lokaci har girgiza kai suke yi suna amsawa, wai sun fahimci abin da aka faɗa. Bil adama yana yin haka ne don yana jin kunyar cewa bai san wani abu ba.
Mutane masu basira ba su da kwana-kwana. Tashin farko za su ce maka “Ban fahimta ba. Ko za ka yi min bayani dalla-dalla kamar shekaruna biyar?”
Irin waɗannan mutane ba su damu da ra’ayoyin sauran jama’a ba, game da iliminsu ko basirarsu. Abin da yafi ɗaukar musu hankali shi ne suna begen fahimtar duk wani abu da ya shige musu duhu. Sun san cewa idan suka fahimci tushen abu, to za su iya fahimtar abin da ya fi wannan wahala.
Ƙwaƙwalwar bil adama na ƙara tsufa, abubuwa suna ƙara yi mata wahalar ganewa. Saboda haka mutane masu basira sun fahimci wannan lamari, shi yasa ba su da wasa da lokacin su. Duk lokacin da suka samu damar koyon wani sabon abu, sai su fitar da kunya da fargaba, su zama ɗalibai.
2. SUN IYA BAYYANA AIKINSU CIKIN SAUƘI
Musamman mutanen da suka ƙware a aikinsu, sun laƙanci hikimar yi wa jama’a ƙarin haske dangane da aikinsu dalla-dalla. Ko me yasa? Saboda sun share shekaru wajen binciken wannan ilimi lungu da saƙo.
Waɗannan mutane sun fahimci yadda bare ke fuskantar wannan aiki na su a karo na farko, kuma sun san ɓangare-ɓangare daban-daban na wannan ilimi, yadda za su iya yi wa mai sauraro bayani a tsanake domin fahimta cikin sauƙi.
Shahararren masanin kimiyya da fasaha Albert Einstein ya ce “Idan ba za ka iya yi wa jama’a bayanin abu ba a sawwaƙe, to ba ka laƙance shi ba”.
3. BA SU MAGANA DOMIN SAURARON MURYARSU, AMMA SABODA ZAƘULO ILIMI DA KARAWA JAMA’A HASKE ZA SU IYA.
Mutane masu basira ba su da lokacin yin ƙananan maganganu ko hirar wasu jama’a.
Wannan ɓata lokaci ne a wajen su.
Sun laƙanci sauraron duk wani mai magana da su, domin fahimtar abin da ake gaya musu, kafin su bayyana nasu ra’ayin.
Suna sha’awar tattauna sababbin hanyoyin warware matsalolin rayuwa, ko kuma neman arziki a maimakon hirar banza da gulman wofi.
A taƙaice, mutane masu basira ba su da kunya wajen mayar da hankulansu akan abubuwan da suka fi muhimmanci.