Monday, 14 November 2022

Hanyoyi 15 Don Tantance Ilimi Mara Amfani

Tura Wannan Zuwa Ga

Malamai waɗanda suka yi rubuce-rubuce akan kimiyya da fasahar koyo da koyarwa, wato ladabai da dabarun ɗalibta da ɗalibai da na malunta da malamai, tun daga irin su Imam Khatibul Bagdadi, da Ibn Abdul Barr, da Alƙali Iyad, da Imam Annawawi, da Imam  Algazzali, da Imam Azzurnuji, da Ibn Jama'a, da Imam Shaukani, da kuma kusan dukkan waɗanda suka rubuta littatafan  Mustalahul hadis,  har zuwa kan Malaman wannan zamani irin su Bakr bin Abdullahi  Abu  Zaid da Sheikh Bin Baz, da Sheikh Usaimin, Allah ya yi rahama a gare su gaba ɗaya da sauran su, dukkannin waɗannan Malamai  sun ja kunnen ɗalibai da malamai akan illoli da cututtuka da matsalolin da ilimi mara amfani yake haifar  wa al'umma. 


MANYAN ILLOLIN ILIMI MARA AMAFANI
Hoto: Brookings


Marubuci: Shehu Mansur Dala


Duk mutumin da ya dirarwa karatu ba tare da ya karanta a ƙalla littafi ɗaya daga cikin waɗannan littafai na kimiyya da fasahar koyo da  koyarwa ba,  (ءاداب طلب العلم/ءاداب العالم والمتعلم) haƙiƙa karatun sa zai kamu da wasu muggan ƙwayoyin cuta masu mutuƙar haɗari waɗanda za su iya rusa al'umma gaba ɗaya, su raba su da imanin su da komai nasu mai kyau da amfani. 


Kuma duk karatun da aka samu  ta wannan hanyar, komai yawansa zai kasance ilimi ne mara  amfani, wanda mai shi babu abin da zai sa a gaba sai rusawa maimakon ginawa, da wargaza kan al'umma maimakaon  haɗa kawunan su, da jefa su cikin ruɗani da shakku da tashin hankali,  maimakon shiriyar da su, da kwantar musu da hankali. A ƙarshe  ya halaka, kuma ya halakar da mutane. Allah ya kiyaye.


Allah ya sakawa Malaman mu da alkhairi, sun kula sosai da tarbiyyar mu da koya mana kimiyya da fasahar koyo da koyarwa,  ta yadda ba sa barin ɗalibi ya yi nisa a karatu sai ya karanta littafin Ta'alimi (تعليم المتعلم طريق التعلم) daga farko har ƙarshe, wani ma sai an sa shi ya maimaita  shi har sau uku, kuma da ma a kullum sai an samu a ƙalla ɗalibai biyu suna karanta shi kowa yana dubawa. Ta haka aka samu ilimi mai amfani wanda yake cike da ladabi da tarbiyya da nutsuwa da amfanar da al'umma. Alhamdulillah. 


Tun daga lokacin neman ilimi alamun waɗannan cututtuka suke fara bayyana ga wasu ɗaliban, waɗannan littafan su ne suke ƙunshe da magani da ma rigakafin su.


Amma fa idan aka sake har suka girma ba a yi maganin su ba, to fa wannan ɗalibi idan ya zama malami kowa sai ya shiga cikin damuwa saboda illar da karatun sa zai haifar ga kowa. 


Waɗannan illoli da cututtuka suna da yawa, kaɗan daga cikin su su ne:


1. Neman ilimi ba don Allah ba, sai don neman girma da abin duniya da alfahari ga mutane. 


2. Ƙin yin aiki da ilimi. Amfanin ilimi aiki da shi, ya kamata duk abin da ka koya ka yi ƙoƙarin yin aiki da shi. 


3. Dogaro da littafai ba tare da tuntuɓar Malamai ba. Wato mutum ya zama Malam-littafi. Ba shi da malami sai littafi kawai ko na'ura mai ƙwaƙwalwa (Computer) ko a shafin matambayi ba ya ɓata (Google). 


A haka za ka ga wanda ko Arba'una hadis bai karanta ba, amma ya tsinto lambobin hadisai daga Sahihul Bukhari yana ƙaryata hadisan da masu sharhin sa, da dukkannin Malamai na da da na yanzu!!! 


3. Neman ilimi a wajen guntaye. Wato waɗanda ba malamai managarta ba, ba malamai masu ingantacciyar aƙida da nutsuwa da ladabi na ilimi ba. 


4. Neman ilimi daga sama. Sai ka ga ɗalibi ya kinkimo Mukhtasar ko Alfiyya ta ɗan Maliku, ko Alfiyyatul hadis, ko Sahihul Bukhari, alhali ko Akhdari da Ajurumiyya da Baiƙuniyya da Arba'una hadis bai yi ba. !!!!!! Ka ga kuwa ai akwai matsala tun da dai ba a fara yin gini daga sama. 


5. Tafasa tun ba a ƙone ba. Sai ka ga da zarar ɗalibi ya fara sanin fassarar kalmomi sai ya yi tsalle ya  haye kujerar malunta, ya jibga kaya a jikin sa ya naɗa rawani, shike nan ya zama malami. Har ma rubutu za ka ga yana yi, wai shi ma ya zama mawallafi. 


A haka kuma zai rinƙa keta alfarmar Malamai na gaske musamman  idan   yana zaton sun saɓawa wata gurguwar fahimtar sa. Wannan cuta ita ake kira Atta'alum (التعالم). A kan ta ne Assheikh Bakr bin Abdullahi Abu Zaid ya rubuta littafinsa mai suna (التعالم واثره على الفكر والكتاب)


6. Girman kai, da alfahari da cika baki, da kuri, da jiji da kai da ƙi-faɗi


7. Yawan musu da gardama da jayayya da tsokane-tsokane da jan magana. 


8. Kasala da nauyin jiki da jan ƙafa wajen neman ilimi da  yawan nazari da halartar wuraren ilimi. 


9. Raina mutane musamman malamai da ɗalibai. 


10. Ƙarancin ibada, musamman  sallolin farilla a cikin jam'i,  da sallolin nafila, da ƙiyamullaili, da azumin nafila, da yawaita zikiri, da rashin tsayayyen  wuridin karatun Alƙir'ani. Wannaan babbar tawaya ce ga ɗalibi da malami wacce take fitar da shi daga sawun malam na ƙwarai (العلماء الربانيون) ta jefa shi cikin miyagun malamai (علماء السوء)


10. Hassada ga ɗalibai da malamai, ga  waɗanda Allah ya yi wa wata baiwa ta musamman. 


11. Gaba da nuna ƙiyayya da jin haushin ɗalibai da malamai da mawadata da masu mulki da ƴan uwa. Musamman  waɗanda Allah ya yi wa wata baiwa ta musamman


12. Ɓata lokaci akan wasanni da hirarraki da latse-latsen waya marasa amfani


13. Saɓawa Allah da aikata manyan zunubai kamar zina, luwaɗi, shaye-shaye, ƙarya, saɓawa iyaye da sauran su. Allah ya kiyaye mu. 


14. Munanan halaye waɗanda za su sa a ƙyamaci mutum a kasa raɓar sa ballantana a amfana da karatun sa. Kamar girman kai, hassada, kushe mutane, cin mutuncin su, zalunci da sauran su. 


15. Dakatar da yin nazari da sayen littattafai da zuwa makaranta da tattaunawa ta ilimi  da malamai da ɗalibai, saboda jin cewa wai shi yanzu ya zama malami. Wannan babbar matsala ce, kuma yaudarar kai ne. 


Waɗannan su ne muhimman illolin da ilimi mara amfani yake haifarwa ga mai shi da kuma gaba ɗayan al'umma. 


Tabbas waɗannan  matsaloli su ne suke wahalar da ƴan kazallaha masu da 'awar  su da malaminsu sun fi kowa ilimi. 


Ya Allah ka tsare mu daga ɓata da ɓatar wa, ka ba mu ilimi mai amfani, ka tsare mu daga ilimi mara amafani Amin.


Daga ƙarshe ga waɗansu littattafai masu amfani ga ƴan uwa na ɗalibai domin magani da rigakafin waɗannan cututtuka, a yi ƙoƙari a neme su koda a yanar gizo-gizo ne a karanta, a kuma nemi ƙarin bayani daga malamai


1.التعالم واثره على الفكر والكتاب/ الشيخ بكر بن عبد الله ابو زيد.

٢.عواءق الطلب/الشيخ عبد السلام بن برجس ال عبد الكريم

٣.التحذير الواصب من اتخاذ العلم سبيلا للدنيا والمناصب./الشيخ معاذ بن احمدبن فؤاد الزعيم

٤.هذا العلم فاين العمل ؟/الشيخ احمد رشدي

٥.طلاب عمل لا طلاب علم/الشيخ محمد الخيمي.

٦.سباءك الذهب في كشف ءافات الطلب /الشيخ احمد بن ابراهيم بن ابي العينين.


Na bar ku lafiya

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user