Da farko dai ina son ki san cewa ke ce wani abu na farko a rayuwata. Ke ce wacce ki ke sa ka ni farin ciki a lokacin da na ke cikin damuwa. Ke ce tudun dafawata a lokacin da na ke neman tudun dafawa. Ke ce wacce ki ke jagoranta ta zuwa kyakkyawar madakata. Ba ni da wata damuwa a tare da ke. Ke ce ta farko da na yarda da ke a rayuwata fiye da komai. Ban san ya aka yi na samu nasarar samunki a rayuwa ta ba, sai dai a koda yaushe ina godiya ga Allah da ya haɗa ni da ke.
Marubuci: Bashir Abdullahi El-bash
Ke ce abubuwa da dama a gare ni. Ke ce ki ke samar min da ƙamshi a lokacin da na shaƙi wari. Ke ce tauraruwata da ke haskakawa. Ke ce babbar abokiyata. Ke ce ta kusa da ni a lokacin kuka. Ke ce abokiyar wasa na. Hakazalika, ke ce ki ke zuwa min a farko a kowane lokaci. Ke na ke tunawa a duk lokacin da wani tunani ya mamaye ni. Ki na kulawa da ni matuƙa, ba ni da kalmomin da zan gode miki.
Na sani cewa dangantar soyayya ba abu ne mai sauƙi ba, hakazalika, na sani cewa ba shakka aure shi ma ba abu ne mai sauƙi ba. Sai dai duk da haka na sani cewa da yardar Allah wata rana zan aure ki. Ba shakka idan mu na tare da juna za mu aiwatar da komai. Za mu warware dukkan wata matsala ta kuɗin biki. Za mu cim ma burinmu na samun wurin zama da kula da iyalanmu cikin aminci da shawo kan matsalolin aiki. Ba shakka idan mu na tare da juna za mu iya komai tare. Ina godiya a gare ki.
Na gode da soyayyarki gare ni a yanzu, tun kafin na aure ki da zaman jiran wata rana da zan zama mijin ki. Na san kin ga abubuwa da dama a gare ni amma har yau ba ki ƙi ni ba, ki na ci-gaba da nuna soyayya a gare ni. Kin gan ni ina rera waƙar da na ke sha'awa a mota tamkar wani wawa, kin gan ni a lokacin da na ke kuka tamkar wanda ya rasa komai, kin gan ni a lokacin da na ke dariya tamkar wanda ya zare, kin ga ni a cikin kyakkyawar shiga, kin gan ni a cikin ado na ƙasaita tamkar sabon zuwa duniya.
Kin gan ni a cikin rauni amma duk da haka ki na sona, kin gan ni a cikin matsananciyar damuwa amma duk da haka ki kan zauna kusa da ni ki gwada rarrashi na. Kin ga idanuwana na zubar da hawaye ki na share mun. Duk wannan tabbaci ne na irin soyayyar da ki ke mun. Kin gan ni a lokacin da na ke cikin rashin tsaro ina jin tamkar ba ni da komai, duniya ta tsane ni, duk da haka ki na tare da ni ki na rarrashi na ki na faɗa min kalaman soyayyarki gare ni.
Murmushinki ya kan faranta min rai. Ina son ki har yanzu. Ina son ki a lokacin damuwa da baƙin ciki. Zan ci-gaba da son ki a duk halin da ki ke ciki. Ƴan mata da dama su kan kawo farmakin neman su yi wuff da ni, sai dai sun kasa samun shawo kaina saboda tsantsar soyayyar da na ke yi miki. Ba na jin cewa zan iya maye wurinki da wata a cikin zuciya ta, ba na tsammanin cewa akwai wata ƴa mace da za ta ba ni kulawar da ki ke ba ni, ba na jin cewa akwai wacce za ta so ni kamar yadda ki ke sona. Abu ne wanda ke kaɗai za ki iya saboda ke ɗin ta musamman ce. Saboda haka babu wata gasa, ba yanzu ba, ba a miliyoyin lokuta masu zuwa ba, ke ce ɗaya tilo da ta san ni da, kuma ke ce ɗaya tilo da za ta ci gaba da sona.
Ina kallon gaba inda za mu aiwatar da komai tare. Ina kallon gaba a lokacin da zan sa ki cikin farin ciki na mu'amalance ki yadda ya kamata. Ina kallon lokacin da zai zo wanda zan sumbace ki a daddaɗan yanayi cikin sirri. Ina kallon lokaci na gaba wanda zan karantar da ke daɗaɗan littattafai, na kunna miki fina-finai masu ƙayatarwa. Da lokaci na gaba wanda zai mu je mu ci abinci a gidan abinci na alfarma.
Saboda haka, ya ke matata wacce zan aura, ina tabbatar miki za ki samu dukkan wata kulawa da gata daga gare ni, zan kasance tare da ke a halin ƙuruciya da halin tsufa, zan zauna tare da ke da ƴaƴan da za mu haifa cikin aminci. Za mu zauna tare har abada, babu wani abu da zai sa ni farin ciki duk duniya sama da ke.
Na sa ni cewa babu wani yanayi da zai zo na guje ki. A koda yaushe ina son ki, ko da a halin baƙin ciki da damuwa ne. Ina yi miki wannan alƙawari saboda kin cancanta da shi.