Karatun Alkur'ani ibada ce mai girma wacce ake samun lada mai tarin yawa tare da samun Aljanna, wanda da yawan mutane a yanzu sun shagala ga barin haka, akan sami wanda idan ba a cikin sallah ba ya kan shafe watanni bai ɗauki Qur'ani ya karanta ba, wanda hakan ba ƙaramar tawaya da asara ba ce.
Marubuci:- Imam Aliyu Indabawa
Alkur'ani rahama ne, ceto ne, kuma alkhairi ne ga mai karanta shi. Lokacin da Allah ke ambatar siffofin salihan bayinsa 'yan aljannah sai ya fara da makaranta Alkur'ani kamar faɗinsa cewa"
إن الذين يتلون كتاب الله وأقاموا الصلاة وأنفقوا مما رزقناهم سرا وعلانية يرجون تجارة لن تبور
"Waɗanda suke karatun Alkur'ani suke sallah a kan lokaci suke kuma ciyarwa a ɓoye da a bayyane suna ƙaunar kasuwanci mara yankewa".
Wasu daga malaman tafsiri suka ce kasuwanci mara ƙarewa da aka ambata shi ne rahama da lada.
An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar Allah ya ƙara musu yarda, Annabi (S.A.W) ya ce " Babu hassada sai a cikin abu biyu, mutumin da Allah ya ba shi Alkur'ani ya ke karanta shi dare da rana, da wanda Allah ya ba shi dukiya ya ke ciyarwa dare da rana".
لا حسد إلا في اثنتين رجل آتاه الله القرآن، فهو يقوم به آناء الليل وآناء النهار، ورجل آتاه الله مالا، فهو ينفقه آناء الليل وآناء النهار
Daga faloli da darajojin karanta Alkur'ani:
1. Samun ɗaukaka a wajen Ubangiji duba da hadisin da Manzo (S.A.W) ke cewa " Allah yana da waɗanda ke matuƙar ƙauna a cikin mutane, aka tambaya su waye ya rasulallah? Ya ce su ne makaranta Alkur'ani.". Ibn Maja ya rawaito shi, Albani ya inganta shi.
قال رسول الله صلى الله عليه وسلم
إن لله أهلين من الناس قالوا: يا رسول الله ، من هم ؟ قال: هم أهل القرآن ، أهل الله وخاصته.
رواه ابن ماجة وصححه الألباني
Manzon Allah ya ce " Mafificin cikinku shi ne wanda ya karanci Alkur'ani ya ke karantar da shi.
خيركم من تعلم القرآن وعلمه
2. Samun lada mai yawa tare da kyakkyawa ababen ninkawa.
Kamar hadisin da Muslim ya fitar da shi cewa Manzon Allah (S.A.W) Ya ce " Shin ɗayanku ba zai yi sammako zuwa masallaci ya fahimci ayoyin Alkur'ani guda biyu ko ya karanta su ya fi masa da a ba shi Taguwa guda biyu ba, aya guda uku ta fi Taguwa guda uku, aya guda huɗu ta fi Taguwa guda huɗu.
أفلا يغدو أحدكم إلى المسجد فيعلم أو يقرأ آيتين من كتاب الله خير له من ناقتين وثلاث خير له من ثلاث وأربع خير له من أربع ومن أعدادهن من الإبل
Manzo ya ce " Wanda duk ya karanta aya ɗari a wani dare ba za'a rubuta shi cikin gafalallu ba, ko za'a rubuta shi cikin masu ibada".
ومن قرأ في ليلة مائة آية لم يكتب من الغافلين أو كتب من القانتين
3. Samun ɗaukaka a duniya.
Kamar hadisin da ke cewa" Allah na ɗaukaka wasu mutane da Alkur'ani ya kuma ajiye wasu".
إن الله يرفع بهذا الكتاب أقواما ويضع به آخرين
4. Samun daraja maɗaukakiya a Aljannah.
Hadisi ya bayyana cewa" Ranar alƙiyama za a ce da ma'abocin Alkur'ani karanta ka yi sama, rera kamar yadda kake rerawa a duniya, mazauninka zai tiƙe a ayar da ka tsaya." .
يقال لصاحب القرآن: اقرأ وارتقِ ورتل كما كنت ترتل في الدنيا، فإن منزلتك عند آخر آية تقرؤها
5. Samun ceto gobe kiyama.
Manzo (S.A.W) Ya ce "Ku karanta Alkur'ani don zai zo muku mai ceto gobe ƙiyama"
6. Saukar nutsuwa.
Hadisi daga Abu-huraira: Babu mutanen da za su taru suna karanta Alkur'ani sai nutsuwa ta sauka a gare su.
وما اجتمع قوم في بيت من بيوت الله يتلون كتاب الله تعالى، ويتدارسونه بينهم، إلا نزلت عليهم السكينة، وغشيتهم الرحمة، وحفتهم الملائكة، وذكرهم الله فيمن عنده
7. Ninkuwar lada.
Annabi (S.A.W) Ya ce "Wanda ya karanta harafi guda daga Alkur'ani yana da lada, kowanne lada akwai ninkinsa goma.".
قال: من قرأ حرفا من كتاب الله فله حسنة، والحسنة بعشر أمثالها
8. Darajar kasancewa tare da Annabawa da manzanni.
Hadisi daga Nana Aisha (R.A), Manzo (S.A.W) Ya ce" Mahiru da Alkur'ani yana tare da Annabawa da manzanni, wanda ke karanta Alkur'ani yana sassarƙewa don wahala yana da lada biyu.".
الماهر بالقرآن مع السفرة الكرام البررة والذي يقرأ القرآن ويتتعتع فيه وهو عليه شاق فله أجران
Ma'anar Mahiru shi ne wanda ke karanta Alkur'ani ya ke kiyayewa da shi ya ke kuma aiki da shi.
Allah ya tabbatar da mu tare da Alkur'ani ya sa ya kasance ceto a garemu gobe ƙiyama Amin.