Yau Lahadi, 10 ga watan May, 2020 matata wacce zan aura ta dawo min da amsar wasiƙar da na aika mata.
Marubuci: Bashir Abdullahi El-bash
Ga abin da ta ce:
"Ranka ya daɗe mijina wanda zan Aura,
Ina Son Ka,
Tsawon shekaru na roƙi Allah ya turo min miji nagari mai tsoronsa. Ban taɓa fahimtar amfanin addu'ata ba sai anan kusa-kusa da na gane muhimmancin samun mijin da na ke fata. Ina tunanin an halicce ka ne kawai domin ni, ka na tafiya a wani wuri a cikin wannan duniya. Ina cike da fatan ka ci-gaba da bin tafarkin Ubangiji wanda zai jagorance ka ka dawo gare ni.
An halicci mace daga haƙarƙarin namiji ba daga ƙafar da ya ke takawa ba, ba kuma daga kansa ba, sai daga ɓangaren da za ta kasance tare da shi ƙarƙashin kulawa da soyayya. Ba zan taɓa tsammanin ka kasance ma'asumi komai naka ya zama ɗari bisa ɗari ba, domin Allah ya sani ni ma ba haka na ke ba.
Za ka iya yin kuskure. Saboda haka, na sani, za mu ɗauki darasi daga kuskuren da ya gabata domin mu kasance tsintsiya maɗaurinmu ɗaya tsawon shekarun da za mu rayu. Ina cike da fatan zan so na kasance da iyawarka da kuma rauninka.
Na yi alƙawarin zan kasance tare da kai a kowane lokaci komai wuya komai rintsi, a mummunar rana da halin tsanani da ka iya tunkarar rayuwarmu.
Na yi alƙawarin faranta maka a kowane lokaci, zan tunatar da kai matsayinka ko da za ka iya mantawa. Na yi alƙwarin zan so ka har abada ba tare da cin amana ba. Na yi alƙawarin zan yi mana addu'a a kullum mu da ƴaƴanmu. Na yi alƙawari a kowane lokaci zan kiyaye da duk abin da ka nuna buƙatarka akai sannan kuma zan maida hankali akan duk abin da ka ce.
Ba zan taɓa zama ma'asumiya komai nawa ya zama ɗari bisa ɗari a ce babu kuskure ba. Zan iya ɓata maka a wasu lokutan na kuma faranta maka a wasu lokutan. Ina fata daidai ɗina zai shafe kurakuraina a wurinka.
Zan yi ƙoƙari kullum na shirya maka kayan karin kumullo da abincin rana da na dare. Zan tsaftace gidanmu na adana maka jakar sanya kuɗinka ta aljihu da makullanka da kayan amfaninka na yau da kullum ka same su cikin aminci a duk lokacin da ka ke buƙatarsu. Zan saurare ka na kuma amsa kiranka zuwa duk ɗakin da ka buƙa ce ni a cikin gidanka mu shaƙata cikin soyayya da jin daɗi.
Zan yi amfani da wannan dama na ƙara gode maka. Na gode maka da ka gabatar da soyayya ta gaskiya a gare ni. Na gode maka da ba ka taɓa sanya wata mummunar rana ta zamto damuwa ga zuciyata ba. Na gode maka kan yadda ka ke sanya ni na ke kasancewa cikin farin ciki a kowane lokaci fiye da jiya. Na gode da kyakkyawar fahimta, da tausayi da nagartacciyar zuciya. Na gode da kallona da ka yi a yadda na ke. Na gode da ka so ni ta duk sashena kyawu da munina.
DUBA WANNAN: Zazzafar Wasikar Soyayya Zuwa Ga Masoyiya
Fatana akanmu soyayyarmu ta kasance har abada cikin farin ciki da rungumar juna, jikokinmu su kasance da mu cikin jin daɗi da nishaɗi. Tare da haka ina fatan mu ci-gaba da sanya Allah farko. Ina son ka, zan ci-gaba da ƙaunarka har abada.
Daga mai biyayya a gare ka, matarka wacce za ka aura". Insha Allah!