Tuesday, 6 December 2022

Zazzafar Wasikar Soyayya Zuwa Ga Masoyiya

Tura Wannan Zuwa Ga

Wata ƙila za ki karanta wannan wasiƙa kafin ki haɗu da ni, ko bayan kin haɗu da ni, Saboda haka ina buƙatar ki san wasu 'yan abubuwa.


Wasikar Masoyiya
Hoto: Getty Images


MarubuciBashir Abdullahi El-bash


Yau Talata, 5 ga watan May, 2020. Na rubuto miki wannan wasiƙa ne a yau saboda ba zan iya daina tunaninki ba, sannan kuma ba zan iya dakatar da kaina daga tunanin yadda farin cikinmu zai kasance ba. Ina fatan za ki ɗauki wannan wasiƙa a matsayin alƙawarin da na yi mi ki; zan yi iya ƙoƙarina wajen ganin na kasance miji a gare ki.


Har ya zuwa yau ban gama sanin dukkan wasu wahalhalun rayuwa da ka iya shiga harkokin rayuwata ba, sai dai ina da cikakkiyar ƙwarewar soyayya kan sanin abin da na ke so da yadda hoton rayuwata zai kasance tare da wacce na ke son mu kasance a tare; (ke kenan).


Waɗanda suke kewaye da ni su na ci-gaba da kasancewa hanyar samun ilimina da kuma muradina kan yadda na ke buƙatar soyayyata ta kasance. Saboda haka, yau anan, zan gwada yin iya bakin ƙoƙarina na yi waɗannan abubuwa:


Na yi alƙawarin zan yi iya ƙoƙarina na ga na sanya ki cikin shauƙi da farin ciki a kullum. Dan haka zan ba ki mamaki matuƙa. Murmushinki kwanciyar ruhina ne. Saboda haka, kawai ki misaltawa zuciyarki irin ƙoƙarin da zan yi wajen kasancewa hanyar samun farin cikin ki.


Na yi alƙawari, a kowanne lokaci zan kalle ki cikin martabawa kamar yadda na yi tun a farkon lokacin da na ji ina son ki.


Na yi alƙawari zan yi ƙoƙarin sanya haske a idanuwanki, zan kalla na ga ko ki na cikin mamaki na ƙarfafa miki gwiwa, ko a lokacin da ki ke kan koyon sumbata ta.


Na yi alƙawari zan riƙe hannunki a lokacin da mu ka kai shekaru 100 kamar yadda na riƙe hannunki a karon farko. Ba zan taɓa barin zumuɗin soyayyarmu ya faɗi ya mutu ba, zan ba ki mamaki.


Na yi alƙawari zan bar ki ki yi tunanin inda za mu je daga baya. Na yi alƙawari zan yi bakin ƙoƙarina a kullum domin nuna ƙaunata a kan ki. Zan kular miki da kaina zan samar miki da sabon shauƙin so da sabon darasi da kuma sabuwar sha'awa domin mu kasance cikin jin daɗi da nishaɗi.


Na yi alƙawari zan samar da sabon labarin da za mu ba wa juna, ina fatan ya kasance mafi kyau da ki ka taɓa samu idan ki ka shiga. Soyayyarmu za ta ci-gaba da girma tsawon shekaru.


Ina fatan na ƙalubalance ki ki ƙalubalanci kan ki kan abin da ya fi; zan maida tunaninki ya zama na daban. Ko da ƙarfina zai ƙare wajen kare naki, zan yi iya bakin ƙoƙarina wajen ganin damuwa ba ta mamaye zuciyarki ba har abada.


Koda a cikin baƙin ciki da duhu, na yi alƙawarin nuna mika bambancin inuwar duhu da kuma taimaka miki shiga cikin hanyoyin haske waɗanda su ke nan a kowane lokaci da zarar an neme su. Bayan su gabaɗaya, a kowane lokaci akwai mummuna sannan mafi muni, da kuma kyakkyawa sannan mafi kyau komai ya na da alaƙa.


Na yi alƙawarin zan sumbace ki a duk tsawon rayuwata tare da ke, tare da shauƙi zan ɗora laɓɓana akan laɓɓanki. Idan mu ka sumbaci juna ina son lokaci ya tafi a hankali domin jin daɗinmu ni da ke.


Na yi alƙawari zan yi wasa kamar yadda ki ke so.


Na yi alƙawari zan yi iya bakin ƙoƙarina wajen kasancewa mai jan hankalinki, sannan kuma zan yi iya bakin ƙoƙarina na kasance mai lafiya domin kare kanmu da ƴaƴanmu da jikokinmu. Wani zai samu damar koyar da su dambe, zan koya miki yaƙi, ina buƙatar ki koyi yadda za ki yi yaƙi da yadda za ki kare kan ki, ka da ki yi amfani da horon da ki ka samu wajen yaƙa ta.


Na yi alƙawari zan taimaka miki ki kasance cikin ƙoshin lafiya a hankalinki da gangar jikin ki, zan yi muku girki zan kuma yi muku tsafta. Ki tsammaci kyakkyawan haɗin karin kumullo, ba tare da bayyana sirrinmu ga kowa ba.


Na yi alƙawarin zama madubin dubawa ga ƴaƴanmu. Ina buƙatar ke da su ku kalle ni a matsayin hanyar ƙarfafar gwiwarku. Ina da burin ɗora su akan kyakkyawar turɓar da mahaifina ya ɗora ni.


Na yi alƙawari zan yi iya ƙoƙarina na so ahalinki kamar yadda ki ke son su. Na yi alƙawarin zan saurare ki a duk lokacin da ki ke buƙatar hakan domin sanar da ni wani abu kan wani abu ko ba ni shawara.


Zan saurare ki musamman ma idan ya kasance ba ki bayyana tunaninki ga wani ba, da kuma abin da ki ke son sanar da ni ko da a lokacin da ba za ki iya magana ba ne. Na yi alƙawari a koda yaushe zan saurare ki.


A lokacin rayuwarmu a tare, na yi alƙawarin tabbatar da cewa ki ji a ranki cewa ke ce cibiyar gida, na sani za ki kasance kuma a kowane lokaci zan riƙa bayyana miki yabona saboda hakan. Kasancewar mutum magidanci ba komai ba ne idan babu mace.


Na yi alƙawari ba zan yi jinkiri wajen ba ku duk wata kariya ba. Na yi alƙawari zan yi komai da zan iya akan ku ba tare da tauye muku dama da ƴancinku ba a zahiri da tunani da kuma hankali ba. 


DUBA WANNAN: Kyakkyawar Wasikar Budurwa Zuwa Ga Saurayi


Na yi alƙawarin samar da al'adar iyali da kuma tabbatar da cewa damarki ta rayuwa ta kasance har abada ta hayar ƴaƴanmu. Na yi alƙawarin ba ki duk wata cikakkiyar kulawa da ƙauna daidai iyawata a kowane lokaci. Insha Allahu.


Daga naki Bashir Abdullahi El-bash, mijinki wanda za ki aura Insha Allahu.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user