Haƙiƙa, li’itikafi yana da sharuɗɗan inganci guda bakwai:
1. Musulunci: Li’itikafi ba ya inganta ga kafiri.
2. Balaga: Ba ya inganta ga yaron da bai balaga ba, ko mahaukaci.
3. Tsarki: Ba ya inganta ga mai janaba ko haila ko nifasi.
4. Masallaci: Li’itikafi ba ya inganta a cikin gida ko ɗaki ko Masallacin da ba a sallar jam’i a cikinsa.
5. Azumi: Li’itikafi ba ya inganta ba tare da Azumi ba.
6. Barin runguma ko sunbatar mace da daddare ko da rana.
وَلاَ تُبَاشِرُوهُنَّ وَأَنْتُمْ عَاكِفُونَ فِي الْمَسَاجِدِ. (سورة البقرة: آية 178)
Allah (S.W.T) ya ce: “Kar ku rungume su (mata), lokacin da kuke li’itikafi a cikin Masallaci.” (Suratul Bakara: aya ta 178).
7. Neman iznin miji: Li’itikafin mace ba ya inganta idan mijinta bai yi mata izini ba.