Idan aka kwance mota baki ɗayanta, aka raba komai na jikinta, sannan aka zuba maka komai nata a gareji ɗaya, shin kana gani za ka iya haɗa ta? Idan aka ba ka takardun da aka yi amfani da su wajen ƙera ta fa?
Marubuci: Bello Galadanchi
To a jami’a ne ake koyar da duk waɗannan dabarun, saboda kowane aji zai mayar da hankali ne wajen tabbatarwa ka laƙanci wani ɓangare na karatun da kake yi. Idan karatun haɗa mota kake yi, to za ka samu malamai daban-daban waɗanda suka ƙware a sassa daban-daban na mota.
Bayan ka kammala ɗaukar waɗannan ajujuwa, to za ka iya haɗa mota. A taƙaice, jami’a ce za ta ba ka makaman da za ka yi amfani da su wajen laƙantar abin da kake so ka yi a rayuwarka.
Ilimi makami ne, kuma duniyar nan filin daga ne. Akwai makamai iri biyu, kuma ana so ka zaɓi ɗaya. Na farko shi ne sanda, na biyu kuma ƙaton bindiga ne mai ɗaukar harsashi ɗari biyu da hamsin a lokaci ɗaya. Wanne za ka zaɓa?
Bugu da ƙari, idan har kana so ka yi sana’a, to akwai matuƙar muhimmanci ka je jami’a domin nazartar wannan sana’a, idan kuwa ba haka ba, waɗanda suka yi wannan karatu za su mallaki manyan makamai a filin daga, kai kuma a ƙyale ka da sanda.
Na tabbata wasu daga cikinku za su lissafo sunayen mutanen da suka yi nasara ba tare da karatu a jami’a ba. Wani hanzari ba gudu ba, mafi yawancin waɗannan mutane sun daina karatu ne, saboda sun laƙanci wani ilimi da ya ba su tagomashi har sana’ar su ta samu babban ci-gaba a ɗan ƙaramin lokaci. Amma daga baya, dolen dole suka koyi ragowar darrusan da ba su kammala a jami’a ba ta wasu hanyoyi na daban.
Idan kai ba Bill Gates ba ne, ko Mark Zuckerberg, to kar ka yaudari kanka. Ka nemi ilimi yanzu-yanzun nan.
Shawara ta ita ce ka yi ƙoƙarin gina sana’arka a dai-dai lokacin da kake karatun jami’a, kuma kar ka daina karatu sai idan har ka cimma babbar nasara a dare ɗaya.
Wani abin dariya shi ne a lokacin da muke da ƙuruciya, gani muke kamar mun san komai. Yarinta ce kawai. Da ka cika shekaru 30, za ka fahimci cewa ashe babu abin da ka sani.
Karatun jami’a ba ɓata lokaci ba ne, saboda zai koya maka dabarun zaman rayuwa a cikin ɗan ƙaramin lokaci, a maimakon ɓata lokaci mai tsawo kana tafka kuskure da da-na-sani kafin ka laƙanci sana’a.
Idan karatun ya gundure ka, to ka samu wani abu daga gefe kana yi. Malamanka za su ba ka shawarwari kyauta. Idan ka girma ka zama mutum, to fa sai ka biya kuɗi sannan za’a ba ka shawara.
Ka zama mai sauƙin kai, ka nemi ilimi, kuma ka yi amfani da makaman da jami’a za ta ba ka.
A rayuwar nan, akwai hanya mai sauƙi, kuma akwai mai wahala. Shawara ta rage ga mai shiga rijiya.
A ƙarshe kuma idan har sana’ar taka ta samu matsala, to takardar digiri ɗinka za ta zama madafa har sai ka samu ka farfaɗo. Ba lallai ba ne ta sama maka aiki, amma masu azancin magana suka ce “Da babu, gwamma ba daɗi”.