Na samu tambayoyi da dama musamman daga matasa, akan dalilan da suka sa nake iya yin abubuwa da yawa a lokaci ɗaya, kuma su ma ta yaya za su koya sannan su aiwatar. Tsakani da Allah wannan ba abu ne mai wahala ba. Ni ma akwai lokacin da babu abin da nake ƙauna kamar cin abinci, sannan na kwanta na yi bacci. Kowace rana sai dai na ce “zan yi wannan, zan yi wancan”, ko “ina so na cimma wannan, ina so na yi nasara a wancan”. To amma abin da na lura da shi shi ne, wannan matsala ta kasala ta addabi matasan mu na Hausawa sosai, kuma ba laifin su ba ne. Idan kana fama da wannan cuta, to yau za ka samu maganin da zai warkar da kai. Maganin da na sha kenan, kuma kai ma zai yi maka aiki.
Marubuci: Bello Galadanchi
A farkon farawa, akwai matuƙar muhimmancin tantancewa idan matsalar ka kasala ce, ko kuma abubuwa ne suka yi maka yawa.
Idan kullum kana da abubuwan yi da yawa, amma ba ka iya kammala su, to akwai yiwuwar cewa ka gagara horas da kanka ne. Maganin anan shi ne ka kawar da duk wani abu da ke ɗauke maka hankali daga gefe, kamar amfani da waya, ko karance-karance marasa amfani, ko hira da sauransu. Kana buƙatar samun hanyoyin ƙarfafawa kanka gwiwa da kanka.
Idan kuma kana da abubuwan yi masu yawa, kuma babu abin da yake ɗauke maka hankali, amma kuma ba ka iya kammalawa, to kar ka yi tunanin cewa kasala ne. A’a. Buri ne ya yi maka yawa, saboda haka dolen dole ka zaɓi ayyukan da suka fi muhimmanci, ka mayar da hankali a kan su.
Idan ba ka da abin yi kwata-kwata, kullum sai bacci da hira, sai yawo a unguwa da ƙwallon kafa, hira da danne-dannen waya, to matsalarka a nan ita ce rashin ƙarfin gwiwa. Hakan zai iya samo asali daga yanayin rayuwarka, ko matsalar takaici, ko kuma irin mutanen da kake mu'amala da su. Akwai jama’a masu ɗimbin yawa dake cikin wannan rukuni.
Babu shakka, ƙalubalantar kasalar ka na da nasaba ne da rukunin da ka faɗa.
Ga hanyoyin da za ka iya amfani da su wajen warware wannan matsala;
1. KA KOYI BAI WA AIKINKA DARAJA: Wani abin mamaki shi ne mutane da yawa sun tsani aiki ko sana’arsu. Sana’arka na iya zama masoyiyarka kuma abin ƙayatarwa. Fahimtar darajar sana’ar da kake yi abu ne da sai ka koya, kuma yana ɗaukar lokaci da maimaitawa kafin ka ƙware. Idan kana ƙaunar aikinka, to za ka zama mai ƙwazo akai, kuma hakan zai kai ka ga cimma burinka na rayuwa. Sau nawa muka ji labarin mutanen da suka fara da talla, amma suka zama masu arziki? Sahad Stores a Kano misali ne. Ku tambayi labarin Ladan Wapa ko Ɗahiru Mangal a Katsina.
Idan abokan aikinka sun ƙware wajen ƙorafi da kuka dangane da yadda suka tsani sana’ar da suke yi, to ka ƙaurace musu. Duk farin cikin ka, mutane masu yawan ƙorafi za su shafa maka cutarsu, domin kai ma ka zama kamar su.
2. KA ƘALUBALANCI ƊABI’UNKA: Idan ɗabi’arka a farkon kowace rana ita ce buɗe Facebook, ko kuma kunna kiɗa, ko kuma kallon T.V, to ka zama mai sauya ɗabi’a a kowace rana. Wani lokacin, ka cire facebook daga kan wayarka, ko kuma ka cire T.V ɗin daga inda yake, ka kulle shi a ɗaki. Darasin anan shi ne, duk lokacin da ka ƙalubalanci ɗabi’un da kake yi kullum, to dole ka ƙirƙiro wasu sababbin ɗabi’u.
Kai kuma idan ka tashi, sai ka yi wani abu wanda zai kasance gudummuwa domin kaika ga nasara a rayuwarka.
3. KA KAFA SABON TSARI: Wato balaguron daina kasala tafiya ce ta maza. Kowa da ka gani a zuciyar shi yana cewa “gobe in sha Allahu, zan tabbatar na kammala wancan abu”. Matsalar anan ita ce da goben ya zo, to zuciyar ka tana nan a mace kamar jiya. Saboda haka hanya mafi amfani wajen ƙalubalantar wannan matsala ita ce ka rubuta abin da za ka yi kullum da safe bayan ka tashi daga bacci. Ba sai ka rubuta manya-manyan abubuwa ba. ‘Yan ƙanana waɗanda za ka iya gamawa a rana su za ka rubuta. Duk wanda ka gama, sai ka saka biro ka soke shi. Jama’a, kasala ɗabi’a ce, kuma ƙirƙirar sabuwar ɗabi’a ita ce hanyar yin ƙafar ungulu da tsohowar ɗabi’a.
4. KA JAJIRCE KUMA KA AUNA CI-GABAN DA KAKE SAMU: Idan har abubuwa suka fara gyaruwa, to kar ka sassauta, kuma kar ka gaji. Wato kasala kamar shaiɗan ne. Kullum neman mafaka take yi a ɓangarorin da kake da akasi. Dole sai ka yaƙi zuciyarka da nufin hana kanka komawa gidan jiya. Babu shakka wani lokacin za ka koma gidan jiya, anan ne za ka jajirce domin komawa filin yaƙi da ci-gaba da yunƙurin samun nasara. Ka tuna cewa kasala ba hali ba ne, ɗabi’a ce.
Bayan ‘yan watanni, ka auna irin ci gaban da ka samu, sannan ka yi tunani ka gani ko kwalliya ta biya kuɗin sabulu. Idan har ka yi farin ciki da halin da ka samu kanka a ciki, to ina mai tabbatar maka cewa ka ci kasala da yaƙi, kuma rayuwarka ta canza kenan har abada. Allah Ya ɗaukaka mana kasar mu ta gado Amin.