Me kike tunani ga wanda ake ƙoƙarin raba shi da abin da yake ƙauna fiye da komai? Dole zai zautu kuma zai ɗimauce, shin ko menene na ce a cikin irin wannan yanayin sai ki ji haushina ko ki ga laifina? Kamata ya yi ki ji tausayina a daidai lokacin da ake ƙoƙarin raba ni da wadda zuciyata ke ƙaunar ta rayu tare da ita a matsayin uwar 'ya'yana fiye da kowace mace a faɗin duniya.
Marubuci: Abba Muhammad Dan Hausa
Ina son ki, na san wannan ba sabuwar kalma ba ce da na fara furta wa a gare ki, ya kamata ki fahimce ni. Na san na yi laifi a bisa furucina, ki yi haƙuri don Allah.
Sadaukarwa ga ɗaliban/masoyan da makararren masoyi (Latecomer) yake yunƙurin raba wa da abar ƙaunarsu.
Sannan kuma, ya na da kyau mu yi haƙuri a duk lokacin da muka rasa wani abu da muke so, cikin fatan samun wanda ya fi shi a nan gaba a rayuwarmu.