Sallar Juma'a Ga Matafiyi ko Matafiya
Hoto: English Alarabiya
Marubuci: Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo
2. Idan matafiyi yana son haɗa sallar azahar da la'asar a ranar juma'a, to yana iya bin sallar juma'a da niyyar azahar, sannan sai ya haɗa ta da sallar la'asar, domin shi a wurinsa ya yi sallar azahar ce ba juma'a ba. Wasu daga cikin malamai sun hana sallatar juma'a da niyyar azahar, amma babu wata ƙwaƙƙwarar hujja a kan haka, domin saɓanin niyya tsakanin liman da mamu ba ya tasiri wajen hana bin sallar junansu, bisa zancen malamai mafi rinjaye.
3. Matafiyi zai iya limancin juma'a ga mazauna gari bisa zance mafi inganci. Domin kasancewar juma'a ba ta wajaba a kansa ba ba ya nufin rashin ingancin juma'arsa idan ya sallace ta, duk kuwa wanda sallarsa ta inganta to limancinsa ya inganta.
4. Ya tabbata cewa Sayyidina Mu'awiya (RA) ya yi tafiya zuwa wani gari da ake kira An-Nukhaila, kuma ya yi wa mutanen garin sallar juma'a. [Duba Ibn Abi Shaiba#5501]. Hakanan shi ma Sarki Umar Ɗan Abdul-Aziz ya je wani gari da ake kira As-Suwaida'u, tafiyar kwana biyu daga Madina, kuma ya ja su sallar juma'a duk kuwa da yana matafiyi. [Dubi Ibn Abi Shaiba#5500].