Aboki
Hikimomin Yau Da Kullum
Hoto: 2018 Flora expo
Marubuci: Anas Darazo
Faɗa
Idan ka tabbatar da abin da kake aikatawa ko kake faɗa mai kyau ne, yana da kyau ka zama mai ɗabi'ar ko in kula ga abinda mutane za su faɗa kan abun. Duk tsiyar su kada ka ɗaga kafa.
Mu'amala
Ka kula da irin mu'amalar da kake da mutane, ka zama mai gaskiya kada ka kuskura mutane su ɗauke ka maƙaryaci. Ka ga idan ka duba kasuwanci ko sana'a ko aure da sauran harkoki masu muhimmanci mutane sun fi son su yi da wanda suka yarda da shi ne. Idan kana da burin ɗaya cikin waɗannan abubuwa lalle ne ka gujewa ƙarya, ka zama mai gaskiya ka tabbatar ka samu yardar mutane.
Magana
Baƙar magana ba tada 'expire date' mutane sukan daɗe suna kallon ta a goshin wanda ya faɗa musu. Ka guji faɗawa mutane baƙar magana.
Lokaci
Ya kai Matashi ka ɓata lokaci tare da Dattijai, duk lokacin da ka samu dama ta kasancewa tare da wani mai yawan shekaru wanda kuma ya taɓuka abun arziki cikin shekarun nasa, kada ka yi wasa da damar, idan ka zauna da shi za ka koyi abubuwa da yawa musamman idan kana masa tambaya.