Sunday, 28 April 2024

Karanta Kalaman Soyayya Masu Daɗin Gaske Mara Misaltuwa Tare Da Ratsa Sassan Jiki

Tura Wannan Zuwa Ga

MUTU


Da na mutu, gwanda na rayu, sai dai da na rayu babu ke. To gwara na mutun, wataƙila mutuwar ta zamo hutu a gare ni, idan na dace, da a ce na rayu, ni kaɗai a cikin duniya, ba tare da ke ba, to gara a ce na rayu ne a matsayin bishiya, domin ko ba komai, masoya za su zauna a ƙarƙashin inuwata su more soyayyar su. Zama a wannan duniya ba tare da ke ba, tamkar zama ne a cikin wuta da rigar fetur. Ina son ki, sai anjima.


Zafafan Kalaman Soyayya
Hoto: Lawn Starter


ALFAHARI


Ba komai ba ne ya sa ba na son na mutu ba, face sai dai na san idan na mutu, ba zan sake ganin ki ba. Yayin da ni kuma zuciyata, ba za ta iya jure kewar ki a halin mutuwa ko rayuwa ba, idan har mutuwa ta yi gaggawar ɗauka ta, kafin na cike alƙawarin soyayyata a gare ki, to kuwa zan bar wasiyyar rubuta sunan ki akan kabarina, domin hakan ne kawai zai sa na yi alfaharin zamo wa masoyi na gaskiya a gare ki. Ina son ki, ina ƙaunar ki.


ADO


Da Ɗawisu zai ga irin kyawun halittar da Allah ya yi miki, da kuwa dole ya tsige gashin kansa da kansa, kuma har abada ba zai so ya sake haɗa ido da ke ba. Duk wanda bai taɓa faɗa miki, ke kyakkyawa ba ce, to kuwa kishi yake yi da kyawun da Allah ya ba ki. A duk lokacin da na gan ki, kin yi ado, ina rasa kayan adon ne suka yi miki kyau ko kuwa ke ce kika yi wa kayan adon kyau, amma a ƙarshe na kan tuna cewa inda babu kyau, kayan ado yake yin tasiri.


HASKE


Garin ya yi haske, amma bai kai hasken fuskar ki ba, zuwa anjima kuma, garin zai yi duhu, sai dai na san, ba zai taɓa yin duhun rashin ganin ki ba a gare ni. Barka da safiya! Ina son ki!


ZUCIYA


Duk bugun da zuciyata ta yi, soyayyar ki ce take ƙaruwa a cikin ta, tamkar yadda kifi ya zamo abokin ruwa, haka soyayyar ki ta zamo abokiyar zuciyata. Da zuciyata nake auna nisan tazarar da ke tsakanina da ke, da iya yanayin inda kika yi nisa da ni da iya yadda ƙararrawar da ke alamtar min da kusancin ki a gare ni za ta ƙara sauti. Daga zuciyata, zan iya gane kina raye ko kuma ba kya raye, soyayyata a gare ki kenan wacce ba ta da sirki. Ina son ki. 


FARIN CIKI


Idan har ya kasance farin ciki ɗaya nake da shi, to kuwa wannan farin cikin ke ce wadda zan bai wa shi, na gwammaci na shafe tsawon rayuwata babu ɗigon da ya shafi zuciyata, ba zan damu da sa kaina a farin ciki ba. Idan har ke kin yi farin cikin. To, kuwa shikenan burina ya cika, iya abin da nake so ki fahimta a yanzu shi ne idan har na ɓata miki, ki yi haƙuri. Ina ba ki haƙuri 


LISSAFI


Idan za a iya sauya soyayyar da nake miki zuwa abinda ido ke iya gani. To, kuwa na tabbata wani ido ba zai iya hango ƙarshen ta ba, ita tamkar ruwan sama ce wacce komai lissafin mai lissafi ba zai iya ƙididdige adadin su ba. A kalamai kam ban san iya adadin kalma nawa ne za su wadaci na bayyanar da soyayyar ki ba, sai dai zan iya taƙaice komai a kalmomi uku rak wato Ina Son Ki!


SO


Idan kika so ni, kowa ma ya ƙi ni. Idan kika kula ni, kowa ma ya bar ni. Idan kika ja ni kowa ma ya sake ni. Idan kika aure ni kuma. To, kowa ma ya tsane ni. Ni soyayyar ki kaɗai ta ishe ni. Ni ke ce komai a gare ni, koda babu kowa a tare da ni, idan ga ki, to kuwa zan yi walwala, amma idan ga kowa a tare da ni, amma babu ke to kuwa har abada walwala ta yi bankwana da zuciyata. Ina son ki.


ƘARSHE


Idan kina tafiya, zan riƙa take miki baya. Idan kina magana zan yi ta sauraren ki. Idan kika yi shiru, zan yi ta yaban ki. Idan kina barci, zan riƙa tsaron ki. Idan kina aiki, zan riƙa taya ki. Idan kika kira ni zan kasance a gaban ki. Idan kuma kika ba ni dama, zan yi ta cewa Ina Son Ki. Ina ƙaunar ki, ina burin kasancewa tare da ke har ƙarshen rayuwata. Ina son ki.


MAMAKI


A rana ɗaya na gan ki, a ranar na kamu da ƙaunar ki, na yawaita tunanin ki, tun kafin na san sunan ki, na riƙa mafarkin ki, wai gani ga ki, na tsaya a gaban ki, ina furta miki kalmomin ina Son Ki, amma bisa mamaki sai ki, sai kika ja tsaki tare da tofar da yawu a gefen ki, kika ɗan ƙara gyara muryar ki, kika kafe ni da idanuwan ki. Sannan cikin wata murya taki kika ce ba na son na rasa ka.


DAMUWA


Idan na rasa ki a rayuwa, ba zan taɓa yin kuka ba, domin kuwa shi kuka ana yin shi ne ga abin da ake tunanin za a iya mantawa zuwa gaba, hawaye ba sa taɓa wanke damuwar da zuciyata za ta shiga, a sanadin rasa ki. Hawaye sun yi ƙanƙanta matuƙa su hana rayuwata barin gangar jikina. Soyayya a gare ki a yadda take za ki fahimce ta, sannan ki gane ban taɓa son ki ƙasa da yadda zan iya rayuwa ba tare da ke ba. Ina son ki.


MAGANA


Wanda bai san ki ba, ya faɗo. Wanda bai taɓa ganin ki ba, yana ruwa. Wanda bai taɓa magana da ke ba, ya samu matsala. Wanda bai taɓa jin sautin muryar ki ba, ya shiga uku. Wanda labarin ki bai taɓa riskar shi ba, ya shiga tara. Wanda ya taɓa ganin ki, ya zo daidai gurin. Wanda ya taɓa magana da ke kuma ya wuce gurin. To, wanda ya gan ki ya kushe ki, babu kalmar bayyanar da haukar sa.  Ina son ki.


RUHI


Tamkar yadda ba za a taɓa wayar gari tafin hannu ya kare hasken rana ba. To, haka ma har abada ba za a taɓa wayar gari a samu cewa na daina son ki ba. Tamkar yadda idan ruwan zafi ya gauraya da na sanyi, ba za a taɓa ware su ba. To, haka ma soyayyar ki ta kasance da ruhin jikina, wacce aka ce matuƙar za a ware su, sai dai a raba ruhin da gangar jikina. A soyayyar ki kam sai dai abin da ya ci-gaba amma babu ranar dakatawa, ina son ki. Nagode.


MATSALATA


Murmushi, sunansa murmushi a fuskar kowa, sai dai murmushi a fuskar ki ya zarce murmushi a fuskar kowa. Ke ba kamar kowacce mace ba ce, domin kuwa Zahra ma tauraruwa ce, amma kuma ai ba ta yi kama da sauran taurari ba. Ranki ya daɗe, abin da yake damuna ba zai wuce soyayya ba, abin da kuma zai iya magance min matsalata ba zai wuce ke ba, ki ba ni dama na furta miki koda kalmomi uku waɗanda su ƙunshi Ina Son Ki. 


RUBUCE 


Idan har idanuwana za su iya kallon wata 'ya mace da sunan soyayya. To kuwa makanta ce ta fi cancanta ta zamo hukunci a gare ni. Babu wani sashi na jikina da zai yi wani abu ga wata macen da ba ke ba, kuma ya ce zai ci gaba da kasancewa a tare da ni. Ke dole rayuwata ce, wacce ko da so ko babu son raina, sai na kasance tare da ita. A cikin zuciyata kike a rubuce, kuma har abada ba za ki goge ba. Ina son ki, ina ƙaunar ki.


ƘUNCI


Ba na son ki, sai don na aure ki. Ba na natsuwa sai don na saurare ki. Ba na tafiya sai don na zo gidan ku. Ba na farin ciki sai idan na gan ki. Ba na ƙunci sai idan an taɓa min ke. Ba na walwala sai idan an yabe ki. Ba na kuka sai idan an kushe ki. Ba na magana sai idan zan yabe ki. Ba na karatu sai idan na ga saƙon ki. Ba na rubutu har sai idan ke zan rubutowa kalmar Ina Son Ki. 


TSORO


Sunana masoyin ki. Muradina auren ki, burina soyayyar ki, addu'ata amincewar ki. Farin cikina ganin ki. Walwalata murmushin ki. Abin nemana farin cikin ki. Abin da na fi ƙi damuwar ki. Tunanina, hidimta miki. Tsorona rasa ki. Furucin bakina kuma Ina Son Ki.


ƘAWAYE


A gaban ki zan ce da ke "I love you". A bayan ki kuma "I miss to you.". A gaban ƙawayen ki kuma "My only one.". A  gaban abokaina kuma "The mother of my children.". A gaban ahalin ki, zan ce da ke "My wife.". A gaban ahalina kuma zan ce "The one I can't live without you". A gaban dukkan matan duniya kuma zan ce da ke "My soulmate". Ina son ki. Na gode.


DAƊI


Ina so na kyautata miki ta hanyar abin da hannuwan za su iya ɗauka su ba ki. Da a ce ina da wadata zan iya yi miki alkawarin maida ke sarauniya, sai dai a yanzu da iya wadatar kalamai nake da shi, to kuwa zan yi miki alkawarin yin amfani da iya kalaman da Allah ya wadata ni da su, zan sa ki ji kanki tamkar sarauniya. Ina jin daɗin yadda ki fahimci cewa ita kyautatawa ba da iya kuɗaɗe ake yin ta ba, face da dukkan abinda Allah ya wadata ka da shi. Ina son ki.


LANTARKI


Misalin yadda nake ganin sauran mata a sa'in da na ƙare kalle ki, shi ne misalin wanda ya sha zuma kafin ɗanɗanon ta ya bar bakinsa sai aka ba shi maɗaci ko kuma wanda a cikin duhu ya ƙurawa ƙwan wutar lantarki ido sai farat ɗaya aka janye hasken. Kyawun da kike da shi na tabbata ko kyau idan ya gan ki sai ya tabbata ke kyakkyawa ce. Da wannan kyawu naki na san duk wacce ta gan ki sai ta raina kanta. Ina son ki.


MASOYIYA


Gadara, gadara ta ɗaya ce shi ne tana so na. Ni ma ina son ta, kuma a iya sanina ba a iya raba zuciya da abin da take so. Masoyiyata, ina son ki. 


ƘOƘARI


A ganina Shah Jahan bai yi wani ƙoƙari ba don ya gina Taj Mahal wa matarsa Mumtaz Mahal ba. Da ni ne shi da nake son tabbatarwa da duniya irin soyayyar da nake yi ma matata har a bayan ranta. To kuwa ba a iya gina Taj Mahal zan tsaya ba, bayan kasancewa ta cikakken mai hidimta miki anan duniya, idan kuma lokacin ki ya yi, to kuwa zan bi ki mu tafi tare, koda kuwa lokacin mutuwata bai yi ba. Son da nake yi miki ba zai ba ni damar ci-gaba da zama anan duniya ba, ballantana har ta kai ga  na gina wani abu domin tunawa da ke.  Ina son ki.


KALMOMI


Ina son ki!! Ko sau dubu zan furta miki waɗannan kalmomin a ƙarshe sai na ji ina son sake furta miki su sau adadin yadda na faɗe su a baya. Idan na kalle ki ƙara son ki nake. Idan na ji sautin muryar ki ƙara son ki nake. Ganin wanda ya taɓa ganin ki ma, ƙara sani cikin shauƙin son ki yake, shi yasa a duk lokacin da na ɗaga hannuna sama godewa Allah nake bisa ba ni ke da ya yi, ba tare da ko-sisina ba. Allah na gode ma ina son ki. 


TAUSAYI 

 

Barkanki na zo ne na yi miki wani laifi a yanzu. Eh laifi mana, tunda na zo ne na ce miki ina son ki, kuma ba zan ɗaga daga nan ba, sai na ji hukuncin da ki yanke a kaina, sai dai ina yi wa kaina fatan ba kai wa Gidan Yari ba ne hukuncin da na aikata a yanzu . Eh Gidan Yari mana, domin idan ki ce ba kya so na tamkar kin sani Gidan Kaso ne. Da mai tausayi kika yi min kama, don haka zan sake maimaita laifina, Ina Son Ki. 


HANYA


Malama Salamu Alaiki, ki yi haƙuri na ɗan dakatar da ke a kan hanya ko? A wallahi dole ce ta sa kasancewar idan na bari ki tafi a yanzu, ban san kuma ranar da zan sake ganin ki ba, amma ina mai ba ki haƙuri kasancewar ba kowacce mace ba ce take son a dakatar da ita a hanya ba. Daga ta can na hango ki, shi ne na ji zubi da tsarin rayuwar ki sun burge ni, da ma na gan ki cikin wannan shigar ta kamala ji na yi kamar ba za ki saurare ni ba, har ga Allah Wallahi ni dai kin burge ni. Ina son ki, da ma abin da na zo faɗa kenan.


FARKO 


Ba ke ce mutum ta farko da ta yi min alkhairi ba amma a yau kin zamo mace ta farko da alkhairin ta a gare ni ya kasa fita cikin raina. Komai ƙanƙantar alkhairi idan ki yi min, to a zuciyata a babba yake zamtowa. Tun daga kan saƙonnin soyayya, kyaututtukan da kike yi min, kulawar da kike ba ni, da koma menene jin sa nake tamkar kin ba ni duniya da abin da yake cikin ta. Ba ni da wadatattun kalmomi, illa na ce na gode. Ina son ki.


ALƘAWARI


Kin ce na ba ki so, na ba ki ƙauna. Kin ce na yi miki alƙawari, na ba ki kalmata. Kin ce na ba ki kulawa na ba ki dukkan lokacina. Kin ce na zamo naki, na ba ki zuciyata. Kin ce kar mu rabu, na ba ki amanata. Kin ce na raɗa miki suna, na ba ki ƙanwata. Kin ce na yi miki kyauta, na ba ki zobena. Kin ce na saka ki nishadi, na ba ki kalamaina. Kin ce na faɗa miki kalmomi uku masu daɗi na ce Ina Son Ki. 


BATURE


Ado ba ya ƙarawa kyau ƙawa, kamar yadda sukari ba zai iya ƙarawa zuma zaƙi ba, a karon farko da na gan ki na gane cewa Baturen da ya yi kayan kwalliya ba don irin ku ya yi su ba. Daga kanki na fahimci cewa ita zinariya sai dai a yi ado da ita amma ba a taɓa yi mata ado, kalmar kyau kuwa idan ba a kanki aka laƙaba ta ba. To kuwa an yi aiki da ita a gurin da ba ta dace ba. Ina son ki.


HAWAYE


Duk yadda na kai ga ɓata miki rai ba zan bari hawayen ki ya kai ga zuba ƙasa ba. Da hawayen ki ɗaya ya ɗiga a ƙasa, to gwara a ce tun farko ban san ki ba, ballantana har ta kai ga na zamo silar zubar su daga idanuwan ki. 


RAƊAƊI


A duk lokacin da ki ɓata min rai na yi fushi, ke ma sai na ga kin yi fushin, wanda hakan yake nuna min zuciyar ki, ba za ta iya barin tawa kaɗai a cikin ƙunci ba. Za ta taya ta jin raɗaɗin tare, haka abin yake idan na kasance a cikin farin ciki, ke ma sai na ga zuciyar ki na taya tawa farin ciki. Ina son ki.


SAƘO


A duk sanda na turo miki saƙo na kan yi wata addu'a wato Allah ya sa idan kika karanta saƙon nawa ya saka ki murmushi. Ya kore damuwar da ke cikin zuciyar ki. Ya kuma sa ki fahimci cewa sai idan kin yi farin ciki ne kaɗai zuciya ke iya samun natsuwa. Idan akwai halittar da Ubangiji ya halitta domin ta saka wata halittar farin ciki a duniya. To ni kuwa Ubangiji ya halicce ni ne kaɗai domin na saka ki farin ciki. Burina a kodayaushe bai taɓa wuce ɗaurawa fuskar ki murmushi ba. Ina son ki.


SAUTI


A tarayyata da ke ban taɓa sanin wani abu da ba sunansa farin ciki ba. A zamana da ke kaf ban taɓa jin wani sauti da ba farin ciki yake amsawa ba. A tsawon lokacin da muka shafe a tare kuma idanuwana ba su taɓa karanta wata kalma da ba ma'anar ta farin ciki ba. Kin gina zuciyata da tubalin farin ciki ta yadda har abada sai dai na ji an faɗi kalmar damuwa ba dai na san ma'anar ta ba. Ina son ki. 


UKU


Da akwai abubuwa uku, da na na gajiyawa da su, kuma duk a kanki ne abar so na. Na ɗaya ba na taɓa gajiyawa da kallon ki a yayinda kike a gabana ko hoton ki a yayin da ba ki a kusa da ni. Na biyu, ba na taɓa gajiyawa da sauraren muryar ki yayin da kike magana da ni ko kike magana da wanina. Na uku, ba na taɓa gajiyawa da furta kalmomin yabo a gare ki, a gaban ki ko a bayan idon ki, ba abin da zuciyata ta sani face tunanin ki. Babu abin da bakina ya sani face furta kalmomin yabo a gare ki. Ina son ki.


Sanusi Kabir ne ya gabatar da su, wakilin mu ya fitar da su a rubuce, ga dukkan wanda yake son ya saurare su a ainihin yadda suke, zai iya sauke Audio ɗin ta hanyar latsa nan.


Ku ci gaba da kasancewa tare da mu a kodayaushe, don ci gaba da samun zafafan saƙonnin soyayya na saurare da na karantawa.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user