BUGUN ZUCIYA
Tamkar yadda duk taurari su zamo 'yan rakiyar zahra, to haka duk matan duniya su kasance 'yan rakiya a gare ki. A wannan ranar farin ciki, zan so a ce farin cikin ki ya zarce na kowa, tamkar yadda kwalliyar ki ta fi ta kowa, haka ma nake son murmushin ki ya zarce na kowa. Fatima ba zan iya cewa ga irin kyawun da za ki yi ba a yau, amma tabbas zan iya cewa, babu wani ido wanda zai kalle ki sau ɗaya, bai ji yana son sake kallon ki a karo na biyu ba, domin kwalliyar ki ta fi a bar ki ki yi tafiya a kan ƙasa Fatima. Ina yi miki Barka Da Sallah Fatima Mami bugun zuciyata, kuma farin cikina, daga naki Real Ababiyo. Ni Real Ababiyo nake cewa da ke, na gode tare da Barka Da Sallah!
MURMUSHI
Ki kan saka ni murmushi, koda kuwa a sanadin ki ne nake fushi, kin san dalili? Ba zan iya kallon kyakkyawar fuskar ki a lokacin da na shiga damuwa ba, face sai wannan damuwar ta wanke daga zuciyata. Ubangiji bai saukar da cuta ba, sai da ya saukar da maganin ta. Don haka, har kullum ina farin ciki da cewa, na same ki a matsayin maganin cututtukana. Dukkan wata cuta da ke damuna, ke ce maganin ta, ba lallai ki sani ba, amma ni dai na sani ke ce maganina. Barka Da Sallah. Ina son ki, ina ƙaunar ki. Ina Son Ki!
KWALLIYA
Idan zan bai wa kowacce mace maki da na gani bisa kwalliyar ta, to kuwa bisa adalci, ban ga wacce ta kai na ba ta ɗaya bisa ɗarin maki ba, amma duk da cewa ban ga taki kwalliyar ba, ina mai sanar da ke a matsayin wacce ta lashe gasar kwalliyar wannan ranar, kin ci ɗari bisa ɗarin maki. Ina son ki!
TSORO
Masoyiyata kin san ne mene ne? Sabo da kallon ki da na yi, duk wacce na gani a taron idin nan, sai na riƙa ji tamkar turo ta aka yi ta ba ni tsoro, ban ƙara gasgata kyawun da kike da shi ba, har sai da na tsinci kaina a tsakiyar waɗanda ba sa da kyan. Da fatan kin yi sallah lafiya?
KISHIYA
Tamkar yadda jan fure ba zai yi wuyar gane wa a cikin koren ciyayi ba, to haka ma ko a cikin mata miliyan kika kasance, ba za ki yi wuyar ganewa ga wanda ya kalla ba. A gurin kyawu kam, ban taɓa ganin kishiyar ki ba. Fatana dai kin yi sallah lafiya?
MATSALA
Na tafiyar da kowacce daƙika ta daren jiya cikin tunanin ki, ban iya yin tunanin komai ba, har gari ya waye, bayan na tafi sallar idin, na yi mamaki, ganin cewa duk macen da na kalla, fuskar ki nake gani a cikin ta ta, hakan kaɗai ya sa na gane cewa, idan ban gan ki a yau ba, to akwai matsala. Barka Da Sallah.
MUTUWA
Farin cikin ki ne, farin cikina. A kodayaushe ina son kasancewa a gefen ki, ina son zama kusa da ke, ba na son na yi nesa da ke idan ba dole ba. A gaskiya ina son ki. Ke ce rayuwata dukkan ta, abokiyar zuciyata, ina matuƙar son ki, ke komai ce a gare ni, ba zan rabu da ke ba, idan ba mutuwa ba ce ta ɗauki raina ba. Ina son ki 'yammata. Barka Da Sallah. Ina son ki!
KEWA
Wannan saƙona ne na Barka Da Sallah zuwa gare ki Maryam Malesh. Yau rana ce ta farin ciki, amma lokaci mafi farin ciki a gare ni, shi ne lokacin da na samu kaina a gaban ki, anan ne zan ba wa idanuwana abin da su daɗe su na son gani. Zan ba wa kunnuwana sautin da su daɗe su na son ji, sannan zuciyata za ta samu farin cikin da ta daɗe ba ta samu kamar sa ba, a duk lokacin da na tsaya a gaban ki, zan so ki dubi cikin idanuwana, za ki ga yadda su yi kewar ki, sannan za ki ji yadda zuciyata take buga wa a domin ki, Maryam Malesh ba ni da irin ki a raina, ba ki da tamka a raina, haka kuma ba ni da kamar ki. Ni nake yi wa Maryam Malesh Barka Da Sallah, fatan kin yi sallah lafiya? Daga naki Real Ababiyo, na gode da saurarena.
Ba zan iya tuna halin da na kasance ba kafin haɗuwar mu, amma tabbas zan iya faɗar halin da zan iya tsintar kaina a ciki, idan har nan gaba rabuwa ta shiga tsakanin mu, ba lallai ba ne ki fahimci damuwata ko abin da nake nufi ba, amma dai ina gujewa kaina rasa ki, rasa ki a gare ni babbar jarabawa ce, wacce ba lallai ba ne na iya cinye ta ba, ba na fatan Allah ya jarabce ni ta hanyar raba ni da ke ba. Ina son ki, ina burin kasancewa tare da ke, har iya ƙarshen rayuwata, ba na son na yi nesa da ke idan ba dole ba. Barka da sallah. Ina son ki.
MURNAR SALLAH
Aminci a gare ki Hafsat, na turo miki wannan saƙon ne domin taya ki murnar wannan rana wato sallah. A wannan rana na san farin cikin kowa, wunin ne, yayin da ni kuma farin cikina ke ce ba wunin ba, domin na san duk tsayin wunin ba zai wuce sa'o'i goma sha biyu ba, ya wuce, yayin da ke kuma za ki kasance a cikin zuciyata na tsawon lokacin da zan kasance a raye. Kwanaki ɗari uku da sittin na shafe ina jiran zuwan wannan ranar da zan ce miki Barka Da Sallah. Ina yi miki fatan kin yi sallah lafiya? Malama Hafsat.
RAYE
Ina son ki ne domin ban san wata macen da ta kai ki ba. Ina son ki ne domin ban taɓa ganin wata macen da ta kai ki ba. Ina son ki ne domin na gamsar da ke cewa, ke ba kamar sauran mata kike ba, kafin na haɗu da ke ban san dalilin zamo wa ta a raye cikin wannan duniyar ba, amma kuma bayan haɗuwa ta da ke, na gane cewa soyayyar ki ce dalilin da ya sa nake rayuwa a wannan duniya. Ke rayuwata ce, ke masoyiyata ce, ke komai ce a gare ni. Ina son ki, sama da yadda zan iya faɗa miki, ke ce rayuwata, sannan ina yi miki Barka Da Sallah. Ina fatan Allah ya maimaita mana bai-ɗaya. Ina son ki!
DUHU
Da so samu ne, a ce na zamo mutum na farko da ya fara ganin ki a wannan safiya, duk da cewa ko wanka ba ki yi ba a yanzu, amma na tabbata komai kankantar hasken alfijir ya isa ya kore tarin duhun dare. Da fatan kin tashi lafiya, kuma kin wayi garin wannan rana mai albarka ta sallah. Ina son ki!
Yayinda kowa ke ɗokin shan ruwa da cin abinci, ni kuma zuciyata ta kasa yin ko ɗaya, domin a ganina ko duka ruwan duniya zan shanye ba za su iya gusar min da ƙishirwar da zuciyata take ji a sanadin soyayyar ki ba, har sai idan na gan ki ne zan iya ci ko na sha. Ina yi miki barka da safiyar sallah.
SAFIYA
Da yawa sun sa ran za su wayi garin wannan safiya, amma Ubangiji bai ba su damar hakan ba, mu da Allah ya albarkaci rayuwarmu da ganin wannan rana, mu gode masa tare da addu'ar shaida wasu ranakun sallar anan gaba. Ina yi miki barka da safiyar sallah.
AGOGO
A yau farin cikina ba ranar ba ne, face wacce nake sa ran gani a ranar, farin cikina ba na waɗanda za su kawo mana ziyara ba ne, face wacce zan kai wa ziyara da kaina. Da kowacce bugawar agogo nake ƙara ƙaguwar son ganin ki, kin tashi lafiya? Barka da wannan safiya ta sallah.
MUSAMMAN
A wannan rana ta musamman, nake miƙo gaisuwa ta musamman, ga wacce ta kasance ta musamman, a jerin mutane na musamman a rayuwata. Barka da safiyar wannan rana mai albarka. Ina son ki.
JIRA
Na tsani jira a rayuwata, amma idan ke ce wacce zan jiran, to kuwa zan iya jira na tsawon rayuwata, ba tare da gajiyawa ba, kowacce daƙika da na shafe ina jiran ki, daɗa farin ciki zai a zuciyata, hakan na nufin adadin zaman jiran ki da na yi, adadin farin cikin da zan riƙa samu a zuciyata. Jiran ki abin so ne a gare ni, ba na taɓa gajiyawa da shi, kowacce daƙika na ɓata a tare da ke, abar farin ciki ce a gare ni. Ina son ki 'Yammata. Barka da sallah, ina son ki.
MATATA
Da tafiyar kowacce daƙika ta rayuwata nake ƙara nisa a tafiyar soyayyata da ke, a yanzu Hafsat na yi nisan da wani kira ba zai taɓa sa wa na juyo ba, duk da cewa waiwaye adon tafiya ne, amma tabbas na yi imani ba zai taɓa zamo wa ado a tafiyar soyayyata da ke ba. Ina son ki Hafsat, ina matuƙar ƙaunar ki a raina, soyayyar da nake yi miki a raina Hafsat ta sanya na daina ganin mata a matsayin mata, face dai maza 'yan uwana, a cikin dukkan mata, ke kaɗai ce idona yake gani a matsayin mace. Ina son ki Hafsat, kuma ina mai tabbatar wa da duniya irin ƙaunar da nake yi miki, idan har na same ki Hafsat, zan yi farin ciki, irin farin cikin da ake cewa daɗi kashe ni. Idan na samu Hafsat a matsayin matata, to kuwa farin cikin da zan yi, har yanzu babu tunanin sa a raina. Hafsat ina gani idan na same ki, to na kammala abin da ya kawo ni duniya. A duniya dai kam, na gama dacewa, sai dai na yi kokari lahirata ta yi kyau, da auren ki zan samu rabin addinina, yayin da zan ƙara cike addinin ta hanyar kyautata miki. Ina son ki Hafsat Amira, ina ƙaunar ki Amira. Wannan saƙon daga tumaturin ki ne Hamza. Fatana dai kyakkyawata, ta yi sallah lafiya? Ina son ki, na gode da saurarena da kika yi.
FARIN WATA
Ke kalli sararin sama, ko za ki iya faɗa min dalilin da ya sa farin wata bai fito ba a yau? To, ni na san dalili, kunyar haɗa ido yake yi da ke, ban san mai yasa ba amma na tabbata idan ya fito a yau, hasken ki ba zai bari nasa ya haska ba, kin fa yi kyau 'yammata, kyau sosai fa nake nufi. Ina son ki, kin ji.
ZOLAYA
Da farko, da na ga wannan kwalliyar taki, bakina kasa rufewa ya yi, wallahi ban san me zan ce ba. Idan na ce kin yi kyau, na rage miki matsayi, kada ki ji kamar zolayar ki nake yi, wallahi har a raina nake faɗa miki hakan, kin yi min kyau sosai 'Yammata, ji nake tamkar na sace ki na tafi da ke, ba wannan ba ma, wai Don Allah mintina nawa ya ɗauke ki kina tsara wannan kwalliyar? Hmm 'Yammata, ko ma mintina nawa ne ƙanwata, wannan kwalliyar ba ta da tsara, na rantse.
TANTAMA
Da akwai jimloli guda uku, da ba na faɗa wa kowa su bayan ke, kuma a duk sanda na faɗa miki su, ba na nufin wasa, har a raina da gaske nake. Idan kika ji na ce ina son ki, to wallahi har a raina da gaske nake. Idan kuma ki ji na ce kin yi kyau, to har a raina hakan nake nufi, da kuma duk sanda ki ji na ce ba zan iya rayuwa ba tare da ke ba, to kar ki yi tantamar hakan, kin fa yi kyau fa? Hmm ina mai miki Barka Da Sallah.
ƘANWATA
Kin san mene ne? Sai yanzu idanuwana su samu damar karya nasu azumin, wai ta ya zan iya daina kallon ki ma? Da wannan kwalliyar dai babu wanda zai kalle ki bai ji yana son sake kallon ki ba, wallahi ƙanwata kin haɗu, haɗuwa sosai fa, Allah dai ya tsare min ke, kar wani ya ƙwace ki daga hannuna, ke wallahi kin yi kyau sosai!
TSAWON RAYUWATA
Ana cewa, idan kana son mutum da gaske, koda za a samu dalilai dubu, da ya kamata a ce ka rabu da shi, domin su, har kullum za a samu cewa, ka nemo dalillai dubu da za a samu cewa ka ci gaba da zama da shi, na iya tsawon rayuwarka. A gurina, ban taɓa samun dalilin rabuwa da ke ba, amma a kullum sai kin ba ni wani dalilin ci gaba da son ki na iya tsawon rayuwata. Ina fatan na samu tsawon rai ne, domin na yi soyayya da ke. Ina matuƙar son ki, barka da sallah. Ina son na rayu da ke, na ci gaba da rayuwa da ke, na iya tsawon rayuwata. Ina son ki!
HUBBI
Aminci a gare ki, Habiba Hubby, da fatan wannan saƙon nawa ya same ki cikin daddaɗan yanayin da za ki iya fahimtar siyaƙin sa. Na turo miki wannan ne domin na taya ki murnar wannan rana mai albarka wato sallah. A wannan rana na san farin cikin kowa, wunin ne, yayin da ni kuma farin cikina saɓanin yadda suke tunani ne, ke ce farin cikina, ba wunin ba, domin na san duk tsayin wunin ba zai wuce sa'o'i goma sha biyu ya wuce. Yayin da ke kuma za ki ci gaba da kasancewa a cikin zuciyata na tsawon lokacin da zan kasance a raye. Habiba Hubby, na tsawon waɗannan kwanaki talatin da mu shafe muna azumi, babu abin da zuciyata ta kasance tana yi face tunanin ki, babu abin da idanuwana su kasance su na son gani face fuskar ki, haka ma babu sautin da kunnuwana su daɗe su na mararin ji sama da sautin muryar ki. Ina so a yau, na yi tozali da kyakkyawar halittar da Allah bai taɓa nuna min kalar ta ba. Ina so a yau na ga kyakkyawar sarauniyar da ko a jaridu labarin kyakkyawar da ta kai ta, bai taɓa zuwa ba, ina so a yau na samu kaina a gaban kyakkyawar hubbina, ina so na samu kaina a gaban ki, ina mai furta miki ina son ki, ina mai furta miki irin yadda na yi kewar ki a raina, wallahi Hubbi, na yi kewar ki.
A lokacin da na fara ganin ki, babu abin da na fara tsoro sama da na faɗa miki cewa ina son ki, amma daga lokacin da na sanar da ke cewa ina son ki, babu abin da ya fi ba ni tsoro sama da rasa ki. Hubby, idan na rasa ki, na rasa rayuwata, ba zan iya rayuwa ba tare da ke ba. Hubby ki fahimci irin yadda nake son ki, wallahi idan na rasa ki, zan rasa raina. Idan na rasa ki Hubby, a ina zan iya samun wacce ta kai ki? Don haka, rasa ki na nufin rasa komai a rayuwata. Idan na rasa ki, ba abin da zan tsaya tsinta a wannan duniya, dole na yi bankwana da ita, kar Allah ya nuna min wannan rana, da zan cewa duniya sai watarana.
Hubbina kin ba ni soyayyar ki, a lokacin da ya kasance cewa ba ni na fi kowa ba, sai dai don ya kasance cewa ni kika zaɓa.
Hubbina, kin bar kowa, kin riƙe wanda ba kowa ba. Yayin da kika mai da wanda ba kowa ba, ya zama kowa a gare ki. Idan har zan iya manta wannan halarcin naki a gare ni, to kuwa har abada ba zan iya yafe wa kaina ba. Habibah zan kula da soyayyar ki, sama da yadda zan iya kula da rayuwata, haka kuma zan riƙe amanar ki, tamkar dai yadda ki riƙe tawa, ba sunana Shafi'u ba, idan har na iya bari zuciyar ki ta san wani abu koma-bayan farin ciki. Na gode da saurarena.
SAURARE
Za ki ji cewa kamar na fiye faɗa miki kalmar Ina Son Ki, ba wai ina yin hakan ba ne don sabo da na yi da furta hakan a gare ki, ina faɗa miki Ina Son Ki ne domin daɗa tunatar da ke cewa, ke ce rayuwata, matuƙar dai kika bar ni, to ni ma zan iya barin duniyar, kada ki ƙosa ko ki gajiya da saurarena yayin da nake faɗa miki cewa "Ina Son Ki". Domin ina son ki ɗin, amma ki tuna ban da kowa bayan ke, ke kaɗai nake so. Kuma ke kaɗai nake burin kasancewa tare da ke, har ƙarshen rayuwata. Ina son ki da dukkan zuciyata.
Sanusi Kabir ne ya gabatar da su, wakilin mu ya fitar da su a rubuce, ga dukkan wanda yake son ya saurare su a ainihin yadda suke, zai iya sauke Audio ɗin ta hanyar latsa nan.