Yin kabbarori Sunnah ne mai ƙarfi a sallar Idi ƙarama(Idul fitr). saboda fadin Allah:
"وَلِتُكْمِلُوا الْعِدَّةَ وَلِتُكَبِّرُوا اللَّهَ عَلَىٰ مَا هَدَاكُمْ وَلَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ".
"...kuma dõmin ku cika adadin, kuma dõmin ku girmama Allah a kan Yã shiryar da ku, kuma tsammãninku, zã ku gõde".
Lokacin farawa daga ganin watan Shawwal, ma'ana daga faɗuwan ranan ƙarshe na watan Ramadhan.
Ibnu Abbas ya ce: "Haƙƙi ne a kan dukkan musulmi idan sun ga watan Shawwal su yi Kabbara". Lokacin yana ƙarewa ne daga fitowan liman zuwa gabatar da sallah".
Sigan Kabbarorin:
ALLAH AKBAR ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLALLAH, ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD.
Tushe/Asali: Zauran Daliban Ilimi