1- Rana: Da ma'anar ɗaya daga cikin halittun Allah (S.W.T) da ke sararin samaniya, dunƙulalliya ce ta fi sauran halittun girma da haske da kuma zafi. Tana ɓullowa ta gabas ta faɗi a yamma.
Ma'anar Kalmar Rana
Hoto: Freepik
Marubuci: Halifa Abdulyassar
2- Rana: Da ma'anar ɗaya daga cikin ranakun mako. misali: Ranar juma'a, asabar, ranar sallah da sauransu.
3- Rana: Da ma'anar aikata aikin alkhairi misali : Haihuwa mai rana ( Bahaushe kenan lokacin da ya tuna wani alheri, ko abin kirki da ɗansa ya yi masa ko ya yi ga waninsa.)
4- Rana: Da ma'anar nuna bajinta misali :
a - Na ga ranar darasin Mal. Bin Ɗalladi mai littattafai a jarabawata ta ƙa'idojin rubutu.
b - Na ga ranar darasin Mal. Muhammad Ath-thaaniy Yunusa Al- kanawiy a jarrabawar al'ummar Hausawa da al'adunsu.