Allah da ya halicci Ɗan Adam ya kuma saukar da shi a doron ƙasa, sai ya kimsa masa sha’awar samun canje-canje na yanayi da guri da hali. Yayin da ya daɗe a cikin wani yanayi ko guri ɗaya, duk yakan ji ya gundure shi, ya gaji da shi, komai daɗinsa, yana son ya ga wani canji.
Ɗan Aljannah Ba Ya Bukatar Wani Canji
Hoto: Just Dawah
Marubuci: Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo
Wannan yanayin halitta da Allah ya yi wa Ɗan Adam, ita ce take taimakon shi wajen kawo ci-gaba a rayuwa ta duniya, da raya ƙasa, da haɓaka ta, kamar yadda Allah ya nema daga wajensa.
Amma a Aljanna sai Allah ya cire masa wannan sha’awar, ya sanya masa tsananin ƙauna da sha’awar zama guri guda, ba tare da ya ƙosa ba, ko ya riƙa tunanin canji daga yanayin da yake ciki na ni’ima zuwa wani yanayi daban.
Wannan kuma shi ne ya fi dacewa da rayuwar Ɗan Aljanna wanda Allah ya masa tanadin duk wata buƙatarsa, ya samar masa duk wani abu na jin daɗi da morewa a cikin gidan Aljannah.
Da a ce, za a bar shi da waccar sha’awa ta shi, kamar yadda take a duniya, to da ya nemi Allah ya canza masa wata aljannar ba wadda yake ciki ba, domin ya gaji da ita.
Shi ya sa Allah ya ce mana, “Lallai waɗanda suka yi imani kuma suka yi aiki na ƙwarai, ajannatan Firdausi sun tabbata masauki gare su. Suna masu dawwama a cikinsu, ba su buƙatar wani canji game da su”. [Al-Kahfi, 107-108].