Wednesday, 15 May 2024

Alfarmar Mahaifiya A Rayuwa

Tura Wannan Zuwa Ga

Ita ce ta fara nuna maka soyayya, tun kafin kasan menene so, tun kafin ka haɗu da 'yammatan da kake ƙaryar za ka iya rasa wani ɓangare na farin ciki idan ba ka same su ba.


Alfarmar Mahaifiya A Rayuwa
Hoto: Livehindustan


MarubuciYahaya S. Kaya


Ta sadaukar da abubuwa da yawa a kanka, babban abun da ta sadaukar shi ne rayuwarta, domin kulawa da kai tun daga ƙuruciya, har zuwa lokacin da ka mallaki hankalin kanka.


Zuwanka cikin duniyarta, ya sa ta daina tattalin tata duniyar ta koma tattalin taka duniyar.


Idan da ace ta mallaki Rai ɗari, babu shakka za ta sadaukar da dukansu domin ba ka kariya.


Saboda kai, za ta iya jure duk wata wahala da ƙuncin rayuwa na gidan miji, domin ta tsaya ta yi gadinka, don tana tsoron kada ta gusa a koma ana cusguna ma rayuwarka a bayanta.


Mahaifiya ita ɗin Duniya ce guda, duk wanda ya rasa mahaifiya ku taya shi kuka, domin ya rasa kaso 99 na farin ciki. Allah ya jiƙan iyayen da suka rasu, mu kuma Allah ya ba mu ikon faranta ma namu iyayen da dukkan ƙarfin.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user