Wai Mutuwa ta ƙwanƙwasa wa wani mutum ƙofa domin ta ɗauki ransa. Sai mutumin ya ce ta dakata mana ko ɗan ruwa ta sha. Ya sa aka dama mata fura, aka sanya ƙanƙara da suga, ya kawo mata ta kwankwaɗa, daga nan ta ɓingire sai barci.
Marubuci: Bukar Mada
Da mutumin nan ya ga ta yi barci, sai ya ɗauki littafin da ta zo da shi, wanda sunayen mutane duka yake ciki, ya goge sunansa da ke saman littafin, ya mayar da shi ƙasa. Ya ajiye littafi inda yake, kamar bai taɓa ba.
Yayin da Mutuwa ta farka daga barci, sai ta yi wa mutumin nan godiya, ta jawo littafinta ta ce, "saboda karrama ni da ka yi yau, maimakon sunanka da ke sama, zan fara aikina da sunan da ke ƙasan littafi."
Komai na duniyar nan, rubutacce ne daga Allah. Abin da duk Allah ya nufi zai sami bawa, to ko ya fi Aula dabara ba zai iya canja shi ba, ba kuwa zai iya tsere masa ba.
Don ci gaba da samun ire-iren waɗannan, ku ci gaba da kasancewa tare da mu a kodayaushe.