Sunday, 12 May 2024

Karanta Saƙon Soyayya Mai Daɗi Ga Masoyiya Cikin Salo Na Waƙa

Tura Wannan Zuwa Ga

Na mallaka miki zuciyata.

Ke ce kike jan ragamata. 

Ki taimaka kar ki ba ni rata.

Burina ki zamo matata.


Saƙon Soyayya Mai Daɗi
Hoto: Ot Gateway 


MarubuciAbba Muhammad Dan Hausa


Na durƙusa yau a gabanta.

Kuka zan yi wa mai sarauta. 

Wadda a mata ba kamarta.

Waje a zuci ki ban na huta.


Na yi shirin zan ba ki tuta.

Mai kyau na launi da tsafta.

Har da zanen furanni jikinta.

Yanayin su launin zuciyata.


Mutanen gari na yabon ta.

Saboda kyawun halinta.

Na san kina son ki san ta.

To ai ke ce masoyiyata.


Ba na iya zaunawa na huta.

Har sai na tambayi Lafiyarta.

Tare da farin cikin zuciyarta.

Sannan na samu na kwanta.


Idan Allah ya sa na azurta.

Ke ce wadda zan sai wa mota.

A garin Kano nan za mu huta.

Har da Ingila a gidan sarauta.


Kwalliyarki suke nazarta.

Kalamanki suke ta bita.

Halayenki suke karanta.

A kan ki suke wahalta.


Kina da kyawu na fata.

Muryarki wane algaita.

Fuskarki ya zan na furta?

Kin gama burge zuciyata.


Kin fi kala da gidan sarauta.

Saboda haka na baki tuta.

Ki je ki yo mulkin nagarta.

A cikin birnin zuciyata.


A nan gaɓar zan dakata.

Karda ki ce na matsanta.

Ɗan Hausa nake masoyiyata.

Abba Ko kuwa ki ce Ɗangata.


Ku ci gaba da kasancewa tare da mu a kowanne irin lokaci, don ci gaba da samun zafafan saƙonnin soyayya na saurare da na karantawa.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user