Dauda ko Dawūd (Da Larabci: داوود ) Annabi ne na Ba'isra'ila wanda kuma sarki ne. Annabi Dauda (AS) yana da murya mai kyau na rera waƙar Yabon Ubangiji kuma Allah ya ba shi fasahar ƙera makamai.
Marubuci: Saliadeen Sicey
Yana da shari'a ita ce Littafin Zabura da Allah ya saukar masa da shi. Dauda (AS) ya ci Urushalima (Kudus) domin Isra’ilawa.
Haihuwa
Annabi Dawud alaihissalam ana kiransa da Dawud a wajen Yahudawa. An haife shi a Urushalima (Birnin Kudus) a ƙarni na 10 kafin Haihuwar Annabi Isa (AS) Kamar sauran Annabawa, Annabi Dawud alaihissalam ya kasance masoyi Annabin ALLAH (SWT), kuma ALLAH (SWT) ya ba shi ikon mu'ujiza da ƙarfi da girma. Shi ne wanda ya kafa hukunce-hukuncen ALLAH Maɗaukakin Sarki a bayan ƙasa.
Imam al-Baqir (RA) ya yi nuni da Dauda (AS) a matsayin ɗaya daga cikin annabawan da su ma suka kasance masu mulki. Dauda (AS) ya yi zamani da Lukman. Dauda (AS) ya yabi Lukman a lokacin da ya yi masa nasiha.
A Cikin Alkur'ani
An ambaci Annabi Dawud alaihissalam sau 16 da sunansa a cikin surori daban-daban na Alƙur'ani a ruwayoyi daban-daban.
An Saukar da Littafin Zubur (Zabura) Ga Dawud alaihissalam.
"Kuma Ubangijinka ne Mafi sani ga Abinda ke cikin sammai da ƙassai. Kuma lalle ne, haƙiƙa, Mun fĩfĩta sãshen Annabãwa a kan sãshe, kuma Mun bai wa Dãwũda zabura. " (k:17:55).
Zabura
Kamar yadda Alƙur'ani da hadisai suka zo, Allah ya saukar da Zabur ga Dauda (AS). Littafin tarin wa'azi ne, da addu'o'i. Kalmar “Zabur” ta zo sau uku a cikin Alkur’ani a cikin suratun Nisa’i , (Alkur’ani 4) al-Anbiya’ (Qur’an 21), da al-Isra’i. (Alkur'ani 17).
Fitattun Halaye
Halaye da yawa an jingina su ga Dauda (AS) a cikin ayoyi da hadisai na Kur'ani. Kamar yadda kur’ani ya faɗa, Dauda (AS) yana iya fahimtar harshen dabbobi, Allah ya ba shi mulki da hikima, kuma Allah ya hore masa duk abin da yake so ya koya. An ruwaito Dauda (AS) ya kasance mutum ne mai yawan bautar Allah kuma yana kuka saboda tsoron Allah.
Akwai hadisai da yawa dangane da ibadun Annabi Dauda (AS), Annabi Muhammad (SAWW) ya yaba da azumi da addu'ar Daud.
Daud (AS) yana azumi kowace rana.
A cikin ingantaccen Hadisi Annabi Muhammad SAW yana cewa: “ Mafi soyuwar Sallah a wurin Allah (SWT) ita ce Sallar Dawud kuma mafi soyuwa a wajen Allah (SWT) Ita ce Sallar Dawud. Ya kasance yana barci rabin farkon dare ya sallaci kashi ɗaya bisa uku nasa, ya sake yin barci (sake) ɗaya bisa shida. Kuma ya kasance yana yin azumin ranaku daban-daban. Kuma a lokacin da ya gamu da abokin gaba bai taɓa guduwa ba. (Bukhari)
Daya daga cikin abubuwan da suka faru na ƙarfinsa da miƙa wuya ga ALLAH (SWT) tun yana ƙarami ya zo a cikin Alkur'ani a cikin suratu Baqarah.
Sai suka rinjãye su da iznin Allah, kuma Dãwũda ya kashe Jalũta, kuma Allah Ya ba shi mulki da hikima (wato Annabci) kuma Ya sanar da shi daga abin da Yake so. Kuma ba domin Allah Ya duba mutane da sãshe ba, dã ƙasa an ɓãci, kuma amma Allah ne Ma'abũcin falala ga tãlikai. (Qur'an 2:251)
Kamar yadda Alkur’ani ya faɗa, duwatsu da tsuntsaye sun ɗaukaka Allah tare da Dauda (AS). Akwai kissoshi daban-daban na abin da ɗaukakar tsaunuka da tsuntsaye suke nufi.
Hukunci
Allah ya ba Dauda (AS) hikima da fahimi a magana kuma ya umurce shi ya yi hukunci a kan mutane masu jayayya An kawo shari'o'in hukunce-hukuncen Dauda a cikin Kur'ani.
Yin Makamai
Kamar yadda Kur'ani ya faɗa, Allah ya koya wa Dauda (AS) yin makamai. Kamar yadda majiyoyin hadisai suka ruwaito, Allah ya yaba wa Dauda (AS) kuma ya gaya masa cewa shi bawane nagari, amma Annabi Dawud baya ji daɗin cewa ba shi da wani aiki kuma ya dogara da dukiyar jama'a don rayuwarsa. Dauda (AS) ya yi baƙin ciki da hakan kuma ya yi kuka. Sa'an nan sai, Allah ya hore masa yin sulke. Dauda (AS) ya ƙera kuma ya sayar da makamai. Don haka, ya yi rayuwa ta wannan hanyar Wannan sana'ar ya daina dogaro da dukiyar jama'a.
Annabi Dawud alaihissalam shi ne farkon wanda ALLAH (SWT ya yi masa gwanintar ƙera makamai da sulke na ƙarfe. ALLAH (SWT) ya ba shi mu'ujiza ta yadda yana iya narkar da ƙarfe a hannunsa ya mai da shi makamai da sulke.
ALLAH (SWT) yana faɗa a cikin suratu Saba: “ Kuma lalle ne, haƙiƙa, Mun bai wa Dawud falala daga gare Mu (Muka ce): “Ya ku duwatsu! Ku maimaita gõdiya tãre da shi, da tsuntsãye. Kuma Muka tausasa masa baƙin ƙarfe, (Muka ce): "Ka sanya waɗansu riguna masu faɗi, kuma ka auna Na'ura da kyau, kuma ka aikata ayyukan ƙwarai." Lalle Nĩ, Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa. (Alkurani 34:10-11).
Murya mai kyau
An yi imanin Dauda (AS) yana da murya Mai Kyau kuma ana ganin cewa babu wanda Allah ya ba shi irin wannan muryar waƙa mai kyau. An ce lokacin da Dauda (AS) ya karanta zabura dukan dabbobi sun je wurinsa suna sauraron muryarsa.
Jalut
Bayan wafatin Annabi Musa Alaihissalam , sai Banu Isra’ila suka zama marasa tarbiyya. Domin su gane rashin biyayyarsu da taurin kai, da kuma tunatar da su zuwa ga ALLAH, sai Allah SWT ya jarrabe su da sanya wani daga cikin mafi munin azzalumai a matsayin shugabansu mai suna Jalut (Goliath). Banu Isra’ila sun gaji da wulaƙanci da ci gaba da yaƙuƙuwa da cin kashi a masarautar Jalut.
Bayan shekaru masu yawa na jarrabawa, Allah (SWT) ya zaɓi Talut ya zama sarkin Banu Isra'ila. Talut manomi ne, kuma ya kasance mai biyayya, mai ƙarfi, mai hikima.
Talut yana da mutane da makamai a cikin sojojinsa, amma duk da haka, Jalut ya fi shi mallakar katafaren runduna, da ƙarfi, da kuma cikakkun kayan yaƙi nesa ba kusa ba. Dukan rundunonin biyu sun shirya yin fafatawa. Banu Isra'ila sun tsorata ganin girman rundunar Jalut.
Sarki Talut ya bayyana cewa duk wanda ya kashe Jalut zai ba shi Auren ɗiyarsa.
Ba wanda ya kuskura ya shiga gaba ya fara faɗa a wannan lokacin, sai ga wani yaro ƙarami ya fito yana cewa zan yaƙi Jalut. Talut ya ƙi yarda. Sai dai yaron ya dage a bar shi ya ce, na kashe zaki a daren jiya don in yi faɗa da Jalut. Wannan jarumin yaron shi ne Annabi Dawud alaihissalam.
Talut ya yarda kuma ya sa shi ya sa sulke don ya fara yaƙi. Annabi Dawud ya tafi da sulke kasancewar shi matashi ne kuma mai fata. Dawud alaihissalam ya fuskanci Jalut ba da wani makami ko takobi ba, sai Abin harbi majajjawa da ’yan tsakuwoyi. Ya yi addu'ar Allah (SWT) ya taimake shi ya shirya kashe Jalut.
Ya harbe shi harbin majajjawa, dutsen ya kai ga goshin Jalut. An buge shi da ƙarfi, nan take ya faɗi da jini na fita daga goshinsa, sai aka ga ya mutu cikin daƙiƙu.
Sojojin Jalut sun firgita ganin shugabansu ya mutu cikin daƙika. Daga nan sai Banu Isra'ila suka ci nasara a yaƙi akan sojojin Filistiyawa da yardar Allah (SWT) da taimakonsa duk da cewa ba su da yawa kuma ba su da kayan aiki.
Daga nan sai Dawud alaihissalam ya shiga ƙasa mai tsarki ta Kudus tare da iyalansa da sauran salihai.
Kamar yadda yayi alƙawari Talut ya aurar da ‘yarsa ga Annabi Dawud alaihissalam. Haka nan Talut ya naɗa Dawud alaihissalam a matsayin kwamandan rundunarsa.
Soyayya da ɗaukakar da Annabi Dawud yake samu daga mutane ya sanya Talut ya fara hassada da Dawud.
Wannan wuta ta kishi ta yi tsanani har Talut ya yi shirin kashe shi. Talut ya rinka tura shi yaki masu hatsari domin makiya su kashe shi, amma Annabi Dawud ya ci nasara a kowane yaqi da taimakon ALLAH (SWT).
A lokacin da Annabi Dawud ya samu labarin shirin Talut, sai ya bar wurin tare da iyalansa a wannan dare ya fake a wani kogo. Wasu mutane da yawa kuma sun sami mafaka tare da shi a cikin kogon. Sannan Annabi Dawud alaihissalam ya tafi daular Palastinu da ke maƙwabtaka da ita tare da mutanensa.
Talut ya kai hari kan Falasdinawa. Talut Ya mutu a wannan yaƙin kuma sojojinsa suka gudu. Annabi Dawud Alaihissalam ya zama sarkin Palastinu.
Annabi Dawud alaihissalam ya shafe shekaru 40 yana mulkin ƙasar Falasdinu cikin aminci da kwanciyar hankali. Ya yi shekara 7 a Hebron, ya kuma yi shekara 33 a Kudus (Urushalima).
Annabi Dawud ya fara gina masallacin Al-Aqsa wanda ya ruguje, ya yi babban aikin Gina Masallacin amma ya kasa kammala shi ya rasu. Daga baya ɗansa Annabi Sulaimanu Alaihissalam ya kammala gina masallacin Aqsa (Masallacin Kudus).
Mutuwa
Dauda (AS) ya mutu yana da shekara ɗari, bayan shekaru arba'in Yana sarauta.
Ku ci-gaba da kasancewa tare da mu a kodayaushe domin ci gaba da samun tarihin Annabawa da Manzanni da Sahabbai tare da salihan bayin Allah nagari, da kuma fitattun mutane a Duniyar Musulunci.