Manzon Allah (SAW) ya ce:"A (Ranar) Juma'a akwai wani lokaci da babu wani bawa musulmi da zai dace da shi, yana a tsaye yana sallah, sai ya roƙi Allah wani alkhairi face Allah ya ba shi". Bukhary da Muslim.
Abin da a ke nufi da "Yana tsaye yana sallah" ai yana zaune yana jiran sallah, yana ambaton Allah kuma yana addu'a, domin wanda ya zauna a masallaci yana jiran sallah to yana cikin sallah ne".
Shaykh Bn Bazz RA yace:
"Wannan lokacin shi ne bayan sallar la'asar har zuwa faɗuwar rana ga wanda ya zauna yana jiran sallar magriba, a masallaci ne ko a gida, mace ce ko namiji ya zauna yana jiran lokacin amsar addu'a, sai dai namiji ba zai yi sallar magriba a gida ba ko ma sauran salloli (na farillah) face da wani uzuri da Shari'a ta yarda dashi..."
مجموع فتاوى ومقالات الشيخ ابن باز (6/159).
Tushe/Asali: Zauran Daliban Ilimi