Saturday 15 June 2024

Bambancin Dan GRA Da Dan Cikin Gari

Tura Wannan Zuwa Ga

A wannan zamani, aƙidun ƙasashen ƙetare da ilimin zamani na ci-gaba da shafar rayuwar al'umma, musamman yadda jama’a suke mu’amala da ‘yan uwansu ta fannoni daban-daban na rayuwa. Misali shi ne rayuwar mutumin GRA da na CIKIN GARI. Ya kamata mu duba bambancin waɗannan mutane guda biyu, sannan mu bada shawara.


SHIN KAI MUTUMIN GRA NE KO NA CIKIN GARI?
Hoto: National moonlight


MarubuciBello Galadanchi


Tafiya ƙasashen waje neman ilimi na taka rawa wajen banbance jama’ar al'umma. A farko, mutumin GRA yakan samu damar zuwa ƙasashe masu yawa, inda yake cuɗanya da al'adu da aƙidu iri-iri. Misali shi ne ladabi da biyayya. Yadda jama’ar wasu ƙasashe kamar yammacin duniya suke nuna ladabi da biyayya ga iyayensu, da malamai da shuwagabanni ba shi da daraja idan aka kwatanta da yadda muka gada tun iyaye da kakanni a al'ummomin mu. Sakamakon haka, mutumin GRA ya kawo wasu aƙidu marasa kan-gado kuma masu rikirkita jama’a waɗanda ba’a fahimta ba, kuma ba su dace da al'ummar mu ba. A ɗaya ɓangaren kuwa, shi mutumin CIKIN GARI yana gida babu inda yaje. Ya fahimci tarihin mutanen sa da al'adunsu. Ya laƙanci darajar mutanen sa da matsalolinsu.


Sannan idan muka dubi halayyar jama’a ta ɓangaren cin abinci, akwai darusa da za mu koya masu amfani. Idan mutumin GRA na jin yunwa, sai ya yi gyaran murya ya ce yana buƙatar “breakfast” ko “lunch” ko kuma “dinner”. Ba zai wanke hannayensa ba, saboda za’a kawo masa “fork” da “spoon” wani lokacin har da wuƙa. A ɗaya ɓarin, idan hantsi ya dubi ludayi, mutumin CIKIN GARI murmushi zai yi, ya yi sallama, ya yi tambaya ya ce a ba shi duk abun da Allah Ya sawwaƙa. Idan ya samu, sai ya wanke hannayensa, ya zauna a kan tabarma ya yi bismillah. 


Bugu da ƙari, harshen da jama’a suke amfani da shi wajen tattaunawa abun dubawa ne. Duk lokacin da mutumin GRA ya samu dama, sai ya fara buga turanci. Wani lokacin yana magana yana ɗaga murya, yana busar iska. Idan ya samu yadda yake so, har manya-manyan kalmomi za ku ji yana harbowa, ko jama’a suna ganewa, ko ba su ganewa, babu abin da ya dame shi. Idan ka ba shi rubutun Hausa, sai ya yi maka ingausa ya ce “Okay, gaskiya ba zan iya reading wannan document ɗin ba, English is better”. Abun dariya shi ne asalinsa ɗan Gwammaja ne. A ɗaya ɓangaren kuwa, mutumin CIKIN GARI harshen mutanensa ya laƙanta. Karin magana, gatse da habaici duk ya laƙanta. Duk abin da ya faɗa, jama’arsa na ganewa. 


A ƙarshe, yana da matuƙar muhimmanci mu fahimci asalin mu da jama’ar mu. Ba mu da inda ya fi gida, kuma babu wata al'ada da ta fi ta mu daraja. Ilimi na da muhimmanci, amma kuskure ne mu fifita ilimi da al'adu da aƙidu ƙetare fiye da namu.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user