Wata rana na je baƙunta ƙauyen Zazzau (Zaria), ina shiga garin, sai kawai na ga mutane sai gudu suke yi. To abin ka da Bakano (Ɗan Kano/Ɗan asalin Kano), ban saba ganin irin haka a birnin Dabo (Kano) ba, ban san me ke faruwa ba, kawai ni ma sai na shiga sahun masu gudu.
Ana cikin gudu sai na fahimci kowa da ya zo ƙofar gidansu, sai ya faɗa ba tare da duba baya ba, kuma ba tare da rufe ƙofa ba.
Abin da ya kuma ba ni mamaki, da na duba kowa sai na ga ya fita daga hayyacin sa, kamar ya kuɓuto daga dajin Sambisa, ana cikin gudu da abin ya ishe ni sai na yanke shawarar, na riƙe ɗaya na tambaye shi.
Haka kuwa aka yi, ina juyawa na ga wani ɗan ƙwaƙƙwaran saurayi a gefe na, na ce "Malam wai gudun me ake yi ne haka?"
Sai ya ce "Ai wutar NEPA aka kawo, shi ne kowa yake gudu ya je ya saka cajin waya saboda hawa Facebook da Twitter da TikTok da kuma Instagram".
Hmm Wai da Ma Haka 'yan Zaria su ke?
Lura: ƙirƙirarren labari ne.
Tushe/Asali: Babu hanyar tabbatar da ainihin mamallakin rubutun, saboda rubutun yana yawo ne a kan yanar gizo-gizo ba tare da asalin sunan mamallakin shi ba. Mun kuma gyara wasu abubuwan a labarin domin ya ƙayatar da ku.