Wata tsohuwa ce a garin Kano ta je tashar mota ta hau zuwa jihar Lagos, an fara tafiya kenan sai tsohuwar nan da tuni ta samu kujera ta zauna cikin fasinjoji ta ce "Malam Direba idan an je Kaduna ka sanar da ni". Direba da ke tuƙi ya ce "To Baba.".
Marubuci: Imran Musa Jahun
An jima kaɗan tsohuwa ta sake cewa
Direba idan an zo Kaduna ka faɗa min fa, Direba ya hasala ya ce "Gyatuma ai na ji
kuma ban manta ba". Aka ci gaba da tafiya, can a wajen Kura tsohuwa ta sake nanata
zancenta, yanzu kam sauran fasinjoji ma
sai da suka ji haushinta, aka ce haba Gyatuma ai ko Direba ya manta za mu tuna
masa amma kin dage sai ka ce wacce za a
sace ki.
Wasu daga ciki suka ce a yi haƙuri
gigin tsufa ne.
Allah cikin ikon sa tsohuwa ta kwanta barci, Direba kuma Allah ya
mantar da shi, haka ma sauran mutanen
dake motar duk suka manta, tsohuwa
ba ta farka daga barcinta ba sai da tafiya
ta yi nisa, tsakaninsu da Ikko bai fi 50km,
sai tsohuwa ta farka, ta yi miƙa ta yi hamma ta ce "har yanzu ba a zo Kadunan
ba ne?" Nan take kowa hankalinsa ya tashi,
aka faɗa ma tsohuwa halin da ake ciki,
nan take ta rusa kuka.
Da jama'a suka ga haka sai aka yi shawara a kan cewar dole Direba ya yi haƙuri a koma Kaduna tunda matar nan ta tsufa da yawa, kuma ba ta da laifi tunda ta yi ta nanatawa.
Aka yi karo-karo aka ƙarawa Direba kuɗin mai aka juyo Kaduna, can wajen Magriba aka iso, aka ce Baba gashi an zo Kaduna.
Tsohuwa ta yi miƙa ta juya ta ce mun zo?
Aka ce ƙwarai kuwa, ta ce "to Alhamdulillahi".
Ta sa hannu ta buɗe jakarta ta hannu.
Ta laluba ta ɗauko PANADOL ɗan gwangwani guda biyu, ta jefa a baki ta bi shi da ruwa, ta ce "Da ma Jikata ce ta ba ni guda huɗu ta ce lallai lallai na sha 2 a Kaduna maganin gajiya ne, idan mun isa Ikko na ƙarasa 2, to tun da yanzu na sha na Kaduna sai kuma mun je Ikko sai na sha sauran biyun."