Mata masu yawa a ƙasar Hausa na zaman aure a cikin gida, ba tare da fita neman aiki a waje ba. Zaman gida na da nasa amfanin, da kuma ƙalubale. Wannan rubutu zai yi tsokaci ne akan yadda matan dake zaune a gida za su tafiyar da rayuwa mai ma’ana, musamman a dai-dai wannan lokacin da al'umma take fama da ƙalubale iri-iri.
Marubuci: Bello Galadanchi
1. KI KASAFTA LOKACI: Kafin ki ankara rana ta faɗi ba tare da ƙulla wani abun azo a gani ba, banda nauyin tafiyar da al'amuran gida da suka rataya a kanki. Duk da cewa babu takura idan aka kwatanta da wajen aiki, akwai matuƙar muhimmanci ki tsara duk wasu abubuwa da za ki yi a wannan rana bayan gari ya waye. Aikin sana’arki ne, unguwa za ki je, karatun Al-Qur’ani ne, za ki buga waya ne, za ki kalli wasan kwaikwayo ne, ya zamana komai yana da lokacinsa. Yin haka zai bai wa wannan rana tsari, sannan idan kina da yara, su ma za su fahimci batutuwan da kowace rana ta tanada da lokutan aiwatar da su. Yara suna son rayuwa mai tsari, kuma ke ma zai amfane ki.
2. KI ƘULLA ZUMUNCI: Musamman idan kina da sana’a, ko kina zuwa makarantar boko ko addini, ko kuma kina cikin wata ‘yar wata ƙungiya ne. Ki tabbatar kin ƙulla zumunci da ‘yan uwanki mata a waɗannan harkoki domin tattauna matsalolinku, bai wa juna shawarwari, hira domin nishaɗi da sauraron koken juna. Wannan zai rage zaman kaɗaici, kuma zai haɗa dangantaka da sauran mata waɗanda rayuwarku ke da alaƙa. Za su iya kasancewa iyayen yara a makaranta, abokan karatu a Islamiyya, maƙota a unguwa da sauransu.
3. KI ƘWARE WAJEN KASANCEWA UWA MAI DAƊI: Babu shakka duk iyaye mata suna da dadi, amma zama uwa shi kanshi wani aiki ne mai wahala. Me yaranki suke so? Shin kina kula da lafiyarsu? Kina kai su wuraren da za su ringa wasa suna jin daɗi? Shin jifa-jifa, kina saya musu abinci ko abun sha mai daɗi, ko kayan wasa? Kar ki yi shakkar duk wani abu da zai sawwaƙa wa rayuwarki idan har kin tabbatar kina bai wa ‘ya’yanki tarbiyya mai kyau. Ɗan adam tara yake bai cika goma ba, saboda haka kar ki ɓata lokaci wajen tabbatarwa sai komai ya tafi yadda kike so. Idan har ke da ‘ya’yanki kuna jin daɗin rayuwarku, kuma kina iya biya musu buƙata, to hakan ya wadatar.
4. KI SAMU MAI TAIMAKA MIKI: Idan kina da hali, to ki samu mai taimako saboda kula da gida da yara kullum, babu dare, babu rana jan aiki ne. Masu hikimar magana suka ce “hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka”, saboda haka babu laifi idan kika samu wani mai taimaka miki da tafiyar da harkokin gida. Idan kina da unguwar zuwa, ko wani abun yi a kasuwa, to hankalinki ba zai tashi ba.
5. KI RINGA FITA WAJE: Wannan gaskiya ne. Idan kina da miji, ki tambayi izinin shi ya ƙyale ki, ki fita ke kaɗai wani lokacin ba tare da yara ba (idan yaran ba jarirai ba ne). Ya zamanto za ki iya zuwa wajen ƙawaye ko ‘yan uwa domin hira, ko ziyara, ko wani abun ƙarin ilimi. Wannan zai ƙara miki ƙarfin gwiwa, kuma ya buɗe tunaninki dangane da zaman duniya da rayuwa. Bugu da ƙari, za ki fahimci aikinki daga waje, yadda idan kin komo gida, za ki tafiyar da nauyin da Allah Ya dora miki yadda ya kamata. Za kuma ki zama kina da alaƙa da jama’a a waje, waɗanda ba lallai ba ne su san ko mene ne yake tafiya a rayuwarki ta gida. Yin haka na ƙara nutsuwa da hazaƙa a zaman gida saboda ba duniya ɗaya kawai kike da shi ba. Kina da wata rayuwar a waje.
6. KI YI WA KANKI IHISANI: Yaran ki ‘yan ƙanana ba za su ba ki albashi ba, kuma ba lallai ba ne su yaba miki a kowace rana. Tunda kuwa babu kuɗaɗen shiga, wani lokacin za ki ga kamar ba’a ganin darajar ki, saboda haka kar ki bari hakan ya kashe miki gwiwa. Ki yi wa kanki albashi. Ki ringa yabawa kanki, sannan ya zamanto kin koya wa mijinki da ‘ya’yanki nuna jin daɗinsu game da yunƙurin da kike yi musu. Kar ki ji kunyar tambayar lada, ko tsire ko ma atamfa. Idan har mijinki yana da wasu hanyoyi na nuna farin cikinsa, ki gode sannan ki bayyana yadda hakan ya ƙara miki ƙarfin gwiwa wajen tafiyar da harkokin gida.
7. KI KAMA SANA’A: Duk wani hali dama ne. Idan zaman aure kike a cikin gida, to na tabbata kina da matsala, kuma ‘yan uwanki mata su ma suna da irin wannan matsala. Ki ƙulla zumunci da su, sannan ki fahimci matsalolin dake ci musu tuwo a ƙwarya. Ke kuma, sai ki yi tunanin hanyar da za ki warware wannan matsala cikin hanzari ba tare da ɓata musu lokaci ba, kuma ba tare da sun kashe kuɗi mai yawa ba. Wannan zai zama sana’a, sannan ki nemi ƙwararru domin ƙarin ilimi yadda za ki inganta ta. Ki tabbatar samun riba ba shi ne abu mafi muhimmanci ba a farko, har sai sana’ar ta kafu kuma ta samu karɓuwa sosai. Ki samar da wani abu da zai sa jama’a su dogara a kanki. Allah Ya albarkaci iyayen mu baki ɗaya.