HUSSAINI: Kamar yadda kika buƙaci na kawo miki dukkan abinda na sani naki, ga shi na dawo miki da shi.
Marubuci:- Hussaini Na Guys
FARIDA: Haka ne ka dawo da su, ga wasiƙunka nan sai ka karɓa.
HUSSAINI: ba zan karɓa ba domin ba na buƙatarsu.
FARIDA: aikuwa ya zama dole ka karɓa domin ba ni da alaƙa yanzu da su.
HUSSAINI: akwai mana domin kin karanta min wasiƙa don haka ba na buƙatar duk abin da kika taɓa karantawa.
FARIDA: oho maka dai gashi idan za ka ɗauka, ka ɗauka ni na yi tafiyata.
HUSSAINI: uhm tsaya kin manta abu guda ɗaya ba ki dawo min da shi ba.
FARIDA: mene ne?
HUSSAINI: zuciyar da kika bi rana kika bi dare kika sace min ita ba tare da na sani ba, ita nake so ki dawo min da abata yanzun nan.
FARIDA: Uhm wato ma kanka ka sani kenan? ni kuma tunanin da ka sani a kanka da yawan zubar da hawayen da na yi a kanka ina so a dawo min da su.
HUSSAINI: uhm ni ne wato na saki kukan ko bayan kin manta rashin lafiyar da na fuskanta duk ta sanadinki ita ma sai a biya ni.
FARIDA: to na ji na yarda zan biya ka amma ka fara cire kanka daga zuciyata duk zan iya biyan ka sauran.
HUSSAINI: ba zan iya ba domin na kafu a cikinta sai dai idan za ki gwada cire kanki.
FARIDA: an ƙi a cire so ma nake na fi da kafuwa.
HUSSAINI: me kika ce?
FARIDA: tunda ba ka ji ba shikenan.
HUSSAINI: to ai na ji ki yi haƙuri to na san kuskurena ne amma ba zan sake ba.
FARIDA: ka gan ka ko, ni dai ka daina ba ni hakuri ko na yi kuka.
HUSSAINI: to na daina dan ba na so daradaran idanun nan naki su koma jajawur.
FARIDA: ka gani za ka fara ko, aina ga dai ka fi ni kyau.
HUSSAINI: Kai!! Lallai ma ai tazarar ki da ni ta wuce a misalta domin idanu sun tabbatar da ke ɗin me kyau ce.
FARIDA: uhm bari na je sai anjima sai mun haɗu ko?
HUSSAINI: uhm to shikkenan ki je ki kwanta, ki sha ruwan sanyi kin ji?
FARIDA: uhm me ya sa?
HUSSAINI: saboda yau na ga faɗan ki.
FARIDA: hhhhh sai an jima ina son ka.
HUSSAINI: ina ƙaunar ki.
To masoya mu kula da zuciyar mu mu kai ta nesa.
Ku ci gaba da kasancewa tare da mu a kodayaushe, don ci gaba da samun zafafan saƙonnin soyayya da kalaman soyayya na saurare da na karantawa.