Babu abin da zan iya ɓoye miki tunda kin riga kin sani kuma kin fahimta da cewa zuciyata ta riga ta jefa ni cikin tarkon da ba zan iya kuɓuta ba, kamar yadda na jima ina sanar da ke cewa son ki kullum yalwa yake a cikin zuciyata, yake ƙara ƙaruwa tare da yaɗuwa babu kakkautawa wanda a yanzu sun riga sun yi ƙarfin da ba ni da iko ko kuma zaɓi wanda ya wuce na bin umarnin zuciyata, wacce ta kasance tana mai yi min jagoranci zuwa ko'ina a duniyar soyayyarki.
Marubuci: Imran Musa Jahun
Ba wai rashin kiran ki a waya ba ne, sai dai tsananin fargabar da zuciyata take na ganin yadda zuciyar ki za ta amince da ƙudurin zuciyata.
A yanzu ina mai tabbatar miki da cewa a duniya irin ta soyayyarki na kasance cikin duhu irin duhun da ban san ranar yayewar sa ba, wanda har yanzu na kasance ina mai fafutuka wajen nemo wa zuciyata abin da take kwaɗaituwa gare ta.
Ina mai tabbatar miki da cewa a yanzu zuciyata ta zamto mai ruruwa tare da azalzala wanda ya haddasa idanuwana suka makance, ganina ya rufe, kunnuwa suka kurumce, jina ya doɗe, ƙafafuwana suka gurgunce, tafiyata ta salwanta, hannayena suka janye, motsina ya yi tawaye, ba ni da ikon yi wa zuciyata umarni ko koma sarrafata ballantana uzuri, sai dai bin ta sau da ƙafa wajen taya ta neman abin da ta zurfafa a lokaci guda kuma ta makance domin ganin kai wa ga mallakarki.
Da ke nake kwana kuma da ke nake tashi da ke nake alfahari a ɓangaren so
da ƙauna, ba ni da aiki a cikin rai sai na yaban ki.
Kuma a haka zan kasance har sai lokacin da zuciyata ta daina fargaba. Tabbas ina son ki.
Ku ci gaba da kasancewa tare da mu a kodayaushe, don ci gaba da samun zafafan saƙonnin soyayya da kalaman soyayya na saurare da na karantawa.
0 comments:
Post a Comment