Ga wasu daga cikin alamomin da ke tabbatar da soyayya a tsakanin masoya.
Marubuci:- Khaleepa Hassan Inuwa
Kamar haka;
1. Sakin fuska ga wanda ake so.
2. Yawan fara'a da girmamawa.
3. Yawan yin zancen wanda ake so ɗin.
4. Bayar da kyautar wani abu koda ƙanƙani ne ga wanda ake so.
5. Jin maganar wanda ake so da mutunta shi.
6. Bada hankali gurin jin abin masoyi zai
faɗa, koda shirme ne.
7. Kunya da nuna biyayya gurin masoyi.
8. Murmushi na musamman a yayinda aka
haɗa ido.
9. Ambaton suna cikin tattausar murya.
10. Kallon nutsuwa da nuna bege a fakaice.
11. Bibiyar hanyar da masoyi/masoyiya ke bi a kllum.
12. Satar kallo da kuma nuna akwai kwarjini ga wanda ake so ɗin.
Domin ci gaba da samun ire-iren waɗannan abubuwan, sai ku ci gaba da kasancewa tare da mu a kodayaushe.