Thursday 13 June 2024

Karanta Hikayar Wani Sarki Da Talakawan Sa

Tura Wannan Zuwa Ga

An ce Sarkin Musulmi Murad na huɗu (IV), wanda ya jagoranci Daular Usmaniya daga shekarar alif da ɗari shida da ashirin da uku (1623) zuwa shekarar alif da ɗari shida da arba'in (1640), yakan yi ɓad-da-bami ya shiga cikin gari yana zagayawa domin ganin halin da talakawansa suke ciki.


Wani Sarki Da Talakawan Sa
Hoto: Kingdom Citizens


MarubuciBukar Mada


Wata rana ya yi irin wannan shigar, shi da Sarkin Dogarai, suna zagayawa cikin gari sai suka tarar da gawar wani mutum yashe a gefen hanya, babu wanda ya kula da ita, sai ka ce mushen kaza.


Sarkin Musulmi ya tambayi mutane, "wane ne wannan? Me ya sa aka bar shi haka, ba a yi masa sutura ba?"


Mutane suka ce, "ai mutumin nan ne mashayi kuma mazinaci?"


Sarkin Musulmi ya ce, "duk da haka nan bai kamata a ƙyale gawarsa kan hanya ba, sai ka ce ba Musulmi ba. Ku taimaka mini mu kai shi ga iyalinsa su yi masa sutura."


Aka ɗauki gawar mutumin aka kai gidansa. Da ajiye shi duk mutane suka watse. Aka bar Sarki da dogarinsa.


Yayin da matarsa ta gan shi sai ta yi ɓas da kuka, ta rungume shi tana cewa, "Allah ya ji ƙan ka bawan Allah, mutumin kirki. Na tabbata kai waliyin Allah ne."


Sarkin Musulmi ya cika da mamaki, ya dube ta ya ce, "ya aka yi ya zama masoyin Allah bayan kuwa yana aikata manyan laifukan da Allah ba ya so? Ko ba ki san cewa mijinki mashayi ne kuma mazinaci ba?"


Matar ta dubi Sarki, idanunta cike da hawaye ta ce, "da ma na zaci haka za ta faru, sai da na gargaɗe shi, amma bai ji ba." 


Ta share hawaye kafin ta ci gaba da cewa, "ka sani ya kai wannan baƙo, kullum da safe mijina zai tafi gidan giya ya sayo tulu guda ya tafo gida da shi. Idan ya zo sai ya ɓulɓular da ita ga ƙasa ya ce, 'yau na tserar da Musulmi daga shan wannan.' Idan yamma ta yi sai ya tafi gidan karuwai, ya samu ɗaya ya biya ta, ya shige ɗakinta ya ce ta rufe ƙofa. Idan ya dawo gida da safe sai ya ce mini, 'yau na tserar da Musulmi biyu daga yin zina.' 


Nakan ce masa, 'maigida, abin nan da kake yi fa mutane za su munana zato a gare ka, har idan ka mutu a rasa mai yi wa gawarka sallah.' 


Yakan yi dariya ya ce mini, 'kada ki damu, ina yi ne don Allah, ba ni kuwa son kowa ya san abin da nake ciki. Idan na mutu Allah ne zai jiɓinci lamarina, idan ya so sai ya sa jana'izata ta kasance a hannun Sarkin Musulmi, ya kuma sa mafi darajar mutane su yi mini sallah.'"


Yayin da Sarkin Musulmi ya ji wannan zance, hawaye ya ɓare daga idanunsa, ya gudana a kan kundukukinsa kamar ruwa har ya jiƙa gemunsa. Ya ce wa matar nan, "haƙiƙa mijinki ya yi gaskiya. Ki sani cewa ni ne Sarkin Musulmi Murad, kuma yanzun nan zan aika wa dukkan malaman da ke daulata, da dukkan talakawan da ke cikin garin nan, su gaggauta zuwa wajen jana'izar wannan bawan Allah."


Allahu Akbar! Sau da yawa muke fassara mutane bisa ga ayyukansu na zahiri, ko waɗanda muka ji ana faɗa. To, amma kuma ba mu san wane sirri suka ɓoye a cikin zukatansu ba, wanda ke tsakaninsu da Ubangijinsu.


Ya ku waɗanda suka yi imani, ku guji yawan zato, akasarin zato zunubi ne.


Don ci gaba da samun ire-iren waɗannan, ku ci gaba da kasancewa tare da mu a kodayaushe.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user