Nuhu wanda aka fi sani da Annabi Nuhu a Musulunci an san shi a matsayin annabi kuma manzon Allah. Yana daga cikin annabawan Ulu'ul azm. Aikin Nuhu shi ne ya gargaɗi mutanensa, waɗanda suke cikin lalata da zunubi, Allah ya umurci Nuhu aikin yi wa mutanensa wa’azi, ya gargaɗi su su bar bautar gumaka kuma su bauta wa Allah kaɗai.
Marubuci: Saliadeen Sicey
Menene labarin Annabi Nuhu?
Annabi Nuhu ya gaya wa mutane cewa shi manzo ne da Allah ya naɗa domin ya isar da saƙon Sa zuwa gare su kuma ya buƙace su da kada su ɓace daga shiriyar Allah, amma duk da kiraye-kirayensa, ba kowa ne ya karɓi shiriyar Ubangiji ba. Wasu sun sanya Annabi Nuhu wahala suka kore shi daga kwarinsu.
Menene Annabi Nuhu ya yi?
Allah ya umurci Nuhu aikin yi wa mutanensa wa’azi , ya gargaɗi su su bar bautar gumaka kuma su bauta wa Allah kaɗai, su yi rayuwa mai kyau da tsabta. Ko da yake ya yi wa’azin saƙon Allah da ƙwazo, mutanensa sun ƙi su gyara halayensu.
Wa'azin farko
Shi Annabi ne, wanda aka aiko don ya gargaɗi ’yan Adam na wannan yanki da mutanensa su canja hanyoyinsu. Ya isar da saƙon sama da shekaru 950. Littattafan Musulunci sun ba da labarin cewa a cikin zuriyar Annabi Adamu, maza da mata da yawa sun ci gaba da bin koyarwar Annabi Adamu ta asali, suna bauta wa Allah shi kaɗai da kuma zama masu adalci. A cikin zuriyar Adamu akwai jarumai da yawa masu tsoron Allah, al'ummominsu suna matuƙar ƙauna da girmamawa. Tafsirin ya ci gaba da ba da labarin cewa, bayan rasuwar waɗannan dattawan, mutane sun ji baƙin ciki mai yawa, Sai suka ƙirƙiri mutum-mutumin waɗannan mutane don tunawa da su. Sa'an nan a hankali, ana haka tsawon shekaru mutane da yawa sun manta da abin da irin wannan mutum-mutumi suka kasance kuma suka fara bauta musu, (kamar yadda Shaiɗan (Shaidan) ya yaudari kowane Al'umma a hankali) tare da wasu gumaka da yawa . Domin ya shiryar da mutane, Allah ya aiko Annabi Nuhu A irin wannan lokacin.
Annabi Nuhu ya fara yi wa mutanensa wa’azi a baki da kuma ta misali. Zai gode wa Allah a kai a kai kuma ya buƙaci mutanensa su yi haka, yana gargaɗin mutanensa a kan azabar da za su fuskanta idan ba su gyara jahilcinsu ba. Alkur'ani ya ce Nuhu ya sha gaya wa mutanensa cewa :
"Ya ku mutanena ku bauta wa Allah, ba ku da wani abin bautawa face Shi. Lalle ne ni, ina jin tsoron azabar yini mai girma."
Gwagwarmayar da Annabi Nuhu ( AS ) ya gudanar ne a fagen kiran mutanensa zuwa ga tafarkin Allah Maɗaukaki tsawon lokaci tare da irin tsaurin kai da ƙeƙashewar zuciya da suka nuna ta hanyar bijirewa duk wata gaskiyar da ta zo musu har ta kai ga matakin da suka fito fili suna ƙalubalantarsa da ya zo musu da azabar da yake yawan musu gargaɗin idan har ya kasance daga cikin masu gaskiya.
Sai Allah Maɗaukaki ya yi umarni ga Annabi Nuhu {a.s} na sassaƙa jirgin ruwa a matsayin shimfiɗar saukar azaba a gare su, bayan Annabi Nuhu ( A.S ) ya bi dukkanin hanyoyin da suka dace wajen ganin ya faɗakar da mutanensa tare da ɗora su a kan tafarkin gaskiya tsawon shekaru masu tarin yawa da alkur’ani mai girma ya fayyace mana shekarun da cewa 950 ne, amma babu waɗanda suka bada gaskiya sai wasu jama’a ‘yan kaɗan, sannan mutanen da suka kafirta suka ɗauki tsauraran matakan ganin sun katange sauran jama’arsu daga hasken shiriya kuma wani babban tashin hankali shi ne yadda suke yawaita haihuwa tare da tarbiyantar da ‘ya’yayensu a kan tafarkin tsananin kafirci da fajirci, sakamakon haka Allah Maɗaukaki ya umurci Annabi Nuhu {AS} kan ya sassaƙa jirgin ruwa a matsayin shimfiɗar saukar da azaba ga kafirai.
Alkur’ani mai girma a cikin Suratu-Hudu daga aya ta 36 zuwa 39 yana fayyace mana haƙiƙanin hikayar da cewa:-
“Kuma aka yi wahayi ga Nũhu cẽwa: Lalle bãbu wanda zai yi ĩmãni daga cikin mutãnenka sai waɗanda suka riga suka yi ĩmãni a baya, sabõda haka kada ka yi baƙin ciki game da abin da suka kasance sunã aikatãwa”. “Kuma ka sassaƙa jirgin ruwa a kan kularmu da wahayinmu, kuma kada ka yi mini maganar komai game da waɗanda suka kãfirta, haƙiƙa sũ mutane ne da za a nutsar da su”.
“Kuma yanã sassaƙa jirgin ( cikin natsuwa), kuma a duk lokacin da shugabanni daga mutãnensa suka wuce ta wajensa sai su rika yi masa izgili. Ya ce: Idan kun yi mana izgili {a yanzu} to, haƙĩƙa mũ mã {wata rana} zã mu yi muku izgili kamar yadda kuke yi mana izgilin”. "Da sannu zã ku san wanda azãba zã ta zo masa ta wulakantã shi {a dũniya}, kuma wata azãba madawwamiya ta sauka a kansa {a lãhira}."
Dangane da umurnin Allah Maɗaukaki gare shi na sassaƙa jirgin ruwa a matsayin shimfiɗar saukar da azaba ta wulaƙanci a kan mutanen da suka kafirta kamar yadda hikayar ta zo cikin littattafan tahiri kamar haka:- Haƙiƙa Allah Maɗaukaki ya hukunta saukar da azabar Ɗufana a kan kafirai, don haka ya umurci bawansa Annabi Nuhu ( AS) da ya sassaƙa jirgin ruwa bisa koyarwa da ilimin da Allah ya sanar da shi, domin Annabi Nuhu {AS} baya da masaniya kan irin haddin ruwan Ɗufana da za a saukar ballantana ya sassaƙa jirgin ruwan daidai da buƙatarsa kamar yadda wahayin Allah ne ke shiryar da shi kan zaɓan irin abubawan da zai yi amfani da su wajen sassaƙa wannan jirgin tare da taimakon Mala’iku.
Kamar yadda alkur’ani mai girma ke bayyana cewa "Kuma ka sassaƙa jirgin ruwa a kan kularmu da wahayinmu, kuma kada ka yi mini maganar komai game da waɗanda suka kãfirta, hakika sũ mutane ne da za a nutsar da su”.
Haƙiƙa Allah ya sanar da Nuhu {AS} cewa zai halakar da mutanen da suka kafirta ta hanyar ruwan Ɗufana kuma komai matsayinsu da kusancinsu ga Annabi Nuhu {AS} tare da hani gare shi kan neman ceto gare su.
Sakamakon haka Annabi Nuhu {AS} ya fara dasa itatuwa da zai yi amfani da su wajen sassaƙa jirgin ruwan, sannan ya jira bayan tsawon wasu shekaru ya yanke bishiyoyin tare da fara sassaƙe su domin samar da jirgin ruwa.
Sannan a duk lokacin da kafirai suka zo shigewa suna ganinsa ya duƙufa cikin aiki, kuma ga shi a kusa da shi babu wani teku tafki sai su dinga masa izgili da ba’a cewa; Ya Nuhu ta yaya wannan jirgin ruwan naka zai gudana? Shin a kan ƙasa zai dinga gungura? Ina ruwan da jirgin zai tafi a kansa? Lalle ya tabbata Nuhu ya haukace, sai su sheƙe da dariya.
Wasu kuma na gudanar da izgili da ba’a ga Annabi Nuhu {AS} ne da cewa: Nuhu ya zame kafinta bayan da annabci ya gagara. Duk da waɗannan maganganu na izgili da ba’a da kafirai ke yi, Annabi Nuhu {AS} ya ci gaba da gudanar da aikin da ya sanya a gaba na sassaƙa jirgin ruwa mai girman gaske, lamarin da ya kai ga kafiran na cewa:
Bayan annabci ya ci tura ga Nuhu a ƙarshen lamari ya koma ƙwararren kafinta mai sassaƙa jirgin ruwa. Wasu kuma na cewa: Wai! wannan jirgin ruwa mai girma haka? Ina ma ƙarami ka sassaƙa domin ka samu sauƙin jan sa zuwa bakin kogi?
Waɗannan kafirai sun ci gaba da yin izgili da ba a ga Annabi Nuhu {AS} suna kekecewa da dariya a gabansa domin wulaƙanci, kuma wannan maganganu na izgili da ba a ga annabin Nuhu {AS} kan jirgin ruwan da yake sassaƙawa sun zame su ne maganganun da ake gudanarwa a tsakanin jama’a a gidaje da wajajen taruwansu musamman kasuwanni, wajajen sana’o’i da sauransu, kamar yadda waɗannan kafirai suke yaɗa maganganun ƙarya da yaudarar kai a tsakaninsu da cewa:
Ku dubi yadda ƙarshen wannan tsoho ya kasance, lalle a yanzu ne muka ƙara samun tabbacin cewa muna kan gaskiya saboda bijirewa maganganunsa domin ya bayyana mana a fili cewa yana fama da matsalar taɓuwar hankali.
Duk waɗannan maganganu na banza da suke fitowa daga bakunan waɗannan kafirai ba dare ba rana amma Annabi Nuhu {AS} ya ɗauki matakin yin banza da lamarinsu tare da kara duƙufa a fagen gudanar da aikin da ya sanya a gaba, yana mai ƙara samun ƙarfin zuciya da nutsuwa kan abin da yake gudanarwa na bin umurnin Allah Maɗaukaki.
A kullum jirgin ruwan da Annabi Nuhu {AS} ke sassaƙawa sai ƙara haɓaka yake yi tare da fitar da siffar jirgin ruwa mai inganci da ƙarko, kuma a wasu lokuta Annabi Nuhu {AS} ya kasance yana mai da martani ga masu masa maganganun izgili da ba'a da cewa: “Idan kun yi mana izgili {a yanzu} to, haƙĩƙa mũ mã {wata rana} zã mu yi muku izgili kamar yadda kuke yi mana izgilin”.
Bayan Annabi Nuhu {AS} ya kammala sassaƙa jirgin ruwan, sai Allah Maɗaukaki ya yi masa wahayi da cewa: Haƙiƙa lalle bãbu wanda zai yi ĩmãni daga cikin mutãnenka sai waɗanda suka riga suka yi ĩmãni a baya sabõda haka kada ka yi baƙin ciki game da abin da suka kasance sunã aikatãwa”.
Sannan sai Annabi Nuhu {AS} ya gudanar da addu’ar saukar azaba ta halakarwa a kan kafirai yana mai cewa: "Ya Ubangijina, Kada Ka bar wani mutum ɗaya daga cikin kãfirai a bayan ƙasa”. Annabi Nuhu {AS} yana mai kafa hujja kan wannan addu’a tashi da cewa: "Haƙiƙa idan har Ka bar su, to zã su ɓatar da bãyinKa, kuma bã zã su haifi kowa ba fãce fãjiri mai yawan kãfirci".
Iyali
Ba a san kome ba game da tarihin Nuhu kafin kiransa na annabci. Duk da haka, Ibn Kathir ya rubuta Yace shi ɗan Lamech ne kuma jikan Metusela, ɗaya daga cikin kakanni daga zuriyar Annabi Adamu. Annabi Nuhu ba shugaban ƙabila ba ne kuma ba mawadaci ne ba amma, tun kafin a ya zama annabi, ya bauta wa Allah da aminci kuma kamar yadda Kur'ani ya faɗa, “mai yawan godiya ne”.
Nuhu ya auri wata mace da ba a ambaci sunanta a cikin Alkur'ani ba. Amma Wasu malaman tarihi na Musulunci irin su Al-Tabari sun yi nuni da cewa sunan matar Nuhu Umzarah bint Barakil amma hakan bai tabbata ba. Yawancin Musulmai suna kiranta da sunanta Naamah. Malaman addinin Musulunci sun yarda cewa Nuhu yana da ’ ya’ya maza huɗu, sunayensu Ham , Shem, Yam da Yafeth. Kamar yadda Alkur’ani ya ce, ɗaya daga cikin ‘ya’yan Nuhu ya kasance kafiri wanda ya ƙi yin imani da Annabi Nuhu kuma ya ƙi shiga cikin jirgin nuhu, maimakon haka ya gwammace ya hau wani dutse, inda ya nutse. An yi ittifaki a cikin mafi yawan malaman Musulunci cewa Yam, shi ne ya nutse; Sauran ukun kuma suka kasance mummunai.
Alkur'ani ya bayyana cewa matar Nuhu ba mumina ce ba, ba ta tare da shi.
An ambaci matar Nuhu ( Naamah ) a cikin Kur'ani a matsayin muguwar mace. Lokacin da Allah Ya jaddada a kan cewa kowa zai yi ta kansa ne a ranar sakamako kuma dangantakar aure ba za ta kasance a gare ku ba! A lokacin hukunci, Alƙur'ani yana cewa:
Allah Ya buga misãli ga waɗanda suka kãfirta , matar Nũhu da mãtar Lũɗu , sun kasance a ƙarƙashin wasu bãyin Mu biyu sãlihai, sai suka ƙaryata mazansu, kuma ba su wadãtar da kõme ba, a wurin Allah. Kuma aka ce musu: "Ku shiga wuta tare da waɗanda suke shiga."
- Qur'an 66:10 [ 46]
Yabo
Allah ya yabi Nuhu a cikin Alkur’ani, wanda ya nuna girman matsayinsa a cikin annabawa. A cikin Alkur’ani sura 17 :3, Allah yana cewa: “Lalle ne shi, ya kasance mai yawan godiya.
Har ila yau, daga Alƙur’ani mai cewa:
Nuhu ya yi kira zuwa gare Mu, kuma Mu ne Mafificin masu ji.
Kuma Muka tsĩrar da shi, shi da mutãnensa, daga azãba mai girma.
Kuma Ya sanya zuriyarsa su dawwama (a cikin ƙasa).
Kissa
Kur'ani ya bayyana cewa Nuhu wahayi ne daga Allah , kamar sauran annabawa irin su Ibrahim ( Ibrahim ), Isma'il ( Isma'il ), Ishaq ( Ishak ), Ya'qub ( Yakub ), Isa ( Yesu ), Ilyas ( Ilyas ), Ayyub . ( Ayuba ), Haruna ( Haruna ), Yunus ( Yunusa ), Dawud ( Dawud ) da Muhammad, (SAW) da kuma cewa shi manzo ne amintacce. Annabi Nuhu ya kasance da cikakken imani ga kaɗaitakar Allah, kuma ya yi wa'azin Musulunci (a zahiri "miƙa wuya," ma'ana miƙa wuya ga Allah ).