Monday 17 June 2024

Karanta Tarihin Rayuwar Annabi Yahaya (A.S)

Tura Wannan Zuwa Ga

Yahya ibn Zakariyya (A.S) (Da Larabci: یحیی بن زکریا ) ko kuma Yahaya (A.S) Annabin bani Ba'isra'ila ne. Ya zama Annabi tun yana yaro, duk da mahaifinsa Ya tsufa kuma mahaifiyarsa bakarariya ce (Juya Mara Haihuwa) ya zo a cikin Alkur'ani, Yahya (A.S) ya kasance sananne ne da Yawan Ibada da yawan kuka Saboda tsoron Allah.


Tarihin Rayuwar Annabi Yahaya (AS) (Yohanna Mai Baftisma)
Hoto: Sarpoosh


MarubuciSaliadeen Sicey



Haihuwa


Annabi Zakariyya (A.S), mahaifin Yahaya (A.S) bai samu haihuwa ba har ya tsufa. Watarana ya ga Maryam (A.S) da ni'imar da Allah Ya yi mata, (Na Samun Haihuwar Annabi Isa A.S) sai ya roƙi Allah da ya ba shi Ɗa:


“Ya Ubangijina! "A cikin Addu'arsa ya ambaci rashin magajinsa da tsoronsa daga danginsa bayan rasuwarsa. Sai Allah ya yi masa alƙawari cewa zai haifi ɗa mai suna Yahya duk da cewa ya tsufa kuma matarsa ​​bakarariya ce.


Mahaifiyar Yahaya (A.S), Alisabatu, ƙanwar Maryamu ce (Mahaifiyar Annabi Isa A.S) Wasu sun ce Sunan Yahya ya samo asali ne daga tushen hyy (ya rayu) (Larabci: ح-ی-ی ) Allah ya halicce shi da imani ko da annabci Ba wanda aka taɓa kira da suna Yahya kafin shi. 


Annabta


Yahya (A.S) ya zama Annabi tun yana ƙarami. Ɗaya daga cikin halayensa shi ne kasancewarsa mai gaskata Annabi Isa (A.S). Yahya (A.S) ya bi kuma ya inganta shari’ar Annabi Musa (A.S), amma lokacin da Annabi Isa (A.S) ya zama annabi sai ya bi shi. 


A cewar Ruwayoyin tarihi, Annabi Isa (A.S) ya girmi Annabi Yahya (A.S) da watanni Goma Sha shida kuma shi ne mutum na farko da ya tabbatar da kuma gaskata Annabi Isa (A.S). Domin ibadarsa da kyawun Halayensa ya rinjayi mutane da yawa su gaskata da shi. 


Tabataba'i yana cewa "littafin" da aka ambata a cikin Kur'ani cewa Yahya (A.S) an umurci ya yi riko da shi shi ne Attaura.


Shahada 


Kamar yadda wani hadisi daga Imam Sajjad ya nuna cewa, wani sarkin Isra’ila ya kamu da soyayya da ɗaya daga cikin ‘yan uwansa muharramai kuma yana son ya aure ta. Yahya (A.S) ya yi adawa da wannan shawarar, kuma adawarsa ta kai ga ƙiyayyar yarinyar da mahaifiyarta a kansa. A sakamakon haka ne mahaifiyar yarinyar ta sa 'yarta ta nemi kan Yahya (A.S) a matsayin sharaɗin auren. Sarkin Isra’ila ya yarda ya fille kan Yahya (A.S) ya aika da kansa a cikin farantin zinariya ga yarinyar.


Halayen ɗabi'a


Daga cikin sifofin Yahya (A.S) an ambace su musamman: Imani da Annabi Isa (A.S), jagoranci ta fuskar ilimi da aiki, Annabi ne salihi, zakka da Taimakawa bayin Allah. 


A game da taƙawa, an ambaci cewa ya kasance yana kuka mai yawa don tsoron Allah.


Yahya (A.S) a cikin Alkur'ani


Sunan Yahya (A.S) ya zo sau biyar a cikin surori huɗu na Alkur'ani Labarin Haihuwarsa da kasancewarsa mai baiwar hazaƙa da wasu daga cikin kyawawan ɗabi'unsa sun zo a cikin Alkur'ani. A cikin Kur’ani 19:15, "Aminci ya tabbata a gare shi, ranar da aka haife shi, da ranar da zai mutu, da ranar da ake tayar da shi yana mai Rai."


Wurin binne shi


An samu saɓani kamar inda aka binne Yahya (A.S) wurin da ya fi shahara shi ne wani kabari a cikin masallacin Umayyawa, wanda ake kyautata zaton wurin ne aka binne gawar Yahaya (A.S) Wacce babu kai, kuma ana kyautata zaton cewa kansa ne aka binne shi a wani masallaci da ke unguwar Zabdani a birnin Damascus. Wasu Ruwayoyi sun ce an binne kan Yahya (A.S) a cikin kabari da ke masallacin Nabi Yahya a ƙauyen Sebastia na Falasɗinu. Har ila yau Kiristoci sun gina coci a kusa da wannan masallaci mai suna Church of St. John the Baptist.


Mandaiyawa 


Mutanen Mandaiyawa suna ɗaukar kansu a matsayin mabiyan Yahya (A.S). A cikin Masallacin Umayyawa da ke Damascus, akwai wani abin tunawa da aka fi sani da kabarin Yahya (A.S).


Mandaiyawa mutane ne masu yaren Aramaic waɗanda suka gaskata cewa suna bin Yahaya (A.S) kuma littafinsu na Yahya (AS) ne. An yi imanin cewa hijirarsu zuwa Iran ta faru ne a lokacin daular Farisa. Baya ga yahudawa suna ɗaya daga cikin baƙin haure na farko waɗanda ba 'yan ƙabilar Aryan ba waɗanda suka je Iran daga Falasdinu. Mandaiyawa masu tauhidi ne, Suna da nasu nassi, harshe, da rubutu. An ambace su a cikin Alkur'ani a cikin ayoyi da dama.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user