Ko da ƙarfe huɗu na yamma ta buga sai duk ma'aikatan Gidan Kifin suka fara harhaɗa komatsansu suna ficewa, cikinsu kuwa har da ni. Bayan na ɗauki jakata na nufi ƙofar fita sai na tuna da wata ajiya da na yi a wani ɗaki. Na juya da sauri domin in ɗauko.
Marubuci: Bukar Mada
Bayan na buɗe ɗakin na shiga, sai ƙofar ta koma ruf ta rufe kamar an tura ta. Ga shi kuma dole sai ta waje za a iya buɗe ta. Na bubbuga ƙofar ko Allah ya sa wani ya jiyo ni, amma shiru ban ji duddugen kowa ba. Mutane duk sun rigaya sun watse.
Ɗakin nan kuwa ɗakin ƙanƙara ne inda ake ajiye kifi. Nan take sanyi ya sallamo wa jikina, ya riƙa ratsa ƙashi da ɓargona. Na fara makyarkyata, haƙori na gamewa kaf, kaf, kaf. Na ci gaba dai da buga ƙofa, amma shiru babu wanda ya buɗe.
Bayan kamar minti talatin sanyi ya fara cin ƙarfina, na fara fita daga cikin hayyacinna, gaɓoɓina suka fara sandarewa, na faɗi ƙasa rib, na miƙa wuya ga mutuwa. Ba zato ba tsammani sai na ji an bankaɗo ƙofa, an shigo da sauri an sungume ni an yi waje. Bayan na farfaɗo sai na ga ashe Maigadin ƙofar shigowa gidan ne. Na yi mamakin yadda aka yi ya san ina ciki. Da na murmure sai na tambaye shi, ya aka yi ya san ina cikin ɗakin?
Maigadi ya amsa mini cewa, "tsawon shekarun da na share ina aiki a wannan kamfani, ma'aikata kan shigo su fita kullum, to amma kowa ya zo sai ya shige abinsa, ba wanda ya damu da ya yi mini ko kallon arziki, balle ya yi mini magana, sai fa 'yan kaɗan kan kula ni. Kai kuwa kullum sai ka gaishe da ni idan za ka shiga ciki. Idan an tashi aiki, sai ka yi mini bankwana. To, yau da aka tashi aiki, na ga kowa ya fita daga gidan nan amma kai ban ga fitowar ka ba. Shi ne na shigo ina bi ɗaki ɗaki ina dubawa, sai ga shi Allah ya sa na tarar da kai."
Da na ji haka ban san sa'adda ƙwalla ta cika mini ido ba, na ma rasa kalaman da zan yi amfani da su wajen gode masa. Ashe 'yar gaisawar da muke yi kullum, wadda ni ban ɗauke ta wani abu ba, shi kuwa ashe da muhimmancin gaske ya ɗauke ta. Da ma Hausawa sun ce, shimfiɗar fuska ta fi shimfiɗar tabarma. Na gode wa Allah da ya kubutar da ni daga halaka, na kuma gode wa Maigadi.