Wani mutum ya zo wucewa ta inda ake ɗaure giwaye, sai ya lura da 'yar igiyar da aka ɗaure ƙafar kowace giwa ga turkenta, to ko jaki aka ɗaure da ita zai iya fizgewa ya kubce. Ya tsaya yana mamakin wautar masu kula da giwayen, domin ya san kowane lokaci za su iya tsinke igiyoyin.
Marubuci: Bukar Mada
Yana nan tsaye yana wannan tunani, sai ga mai kula da su ya zo. Mutumin ya tambaye shi, "me ya sa kuke ɗaure giwaye da wannan 'yar igiyar, maimakon ku ɗaure su da sarƙa mai ƙarfi? Ba ku tsoron su kuɓce wata rana?"
Sai mai kula da giwayen ya yi dariya ya ce, "tun lokacin da giwayen suke ƙanana ake ɗaure su da waɗannan igiyoyin, tun a wancan lokacin kuwa sun gwada tsinka su, amma da yake ƙarfinsu bai kai ba, ba su iya tsinkawar ba, haka suka haƙura cikin tsammanin ba za su iya tsinka su ba. To har yanzu ma da suka girma, sun tafi a kan zaton ba za su iya tsinka igiyoyin ba, don haka ko ƙaƙarin jaraba tsinkawar ma ba su yi."
Mutumin ya bushe da dariya, ya tafi yana mamakin sakarci na waɗannan giwaye. Ga shi dai za su iya tsinke igiyoyin a kowane lokaci, amma zaton ba za su iya ba, ya hana su gwadawa.
Kodayake wasu mutanen ma ai haka suke. Da zarar sun jaraba wani abu sau ɗaya sun kasa, to ba za su sake jaraba shi ba. Sun tafi bisa zaton wannan abu ya fi ƙarfinsu har abada. Alhali da za su sake jaraba abun, to da wataƙila su same shi cikin sauƙi. Kada mu yarda igiyar zato ta ɗaure mu, tamkar yadda ta ɗaure giwayen can.